← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 126 OF 158

Sashe 126

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*End of free pages, za mu ci gaba da update a payment group*

*For continuation of the book Halysaah, pay 500 into 3276052019 Fcmb Hauwa Bello Jiddah*

_And ur evidence of payment via 07087865788_✍🏻

*My special thanks to those that have already patronized since the beginning of this book, Thank you so much and i appreciate you*🥺
[5/20, 6:42 AM] Zainab Madawaki Dahiru:
*KURA A RUMBU*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 52*

Kwana yayi yana tunanin yanda akayi Zulaiha ta yaudareshi, tsayin shekarun da suke tare ace bai taɓa tunani ko hasashen tana da wani hali na daban bayan wanda ya santa da shi ba. Yaran da talauci da matsin rayuwar da suka tashi a ciki ya saka basuda kataɓus ko a cikin unguwa ɗaiɗaikun mutane ne suke mu'amala da su balle makaranta.

Shigar sa cikin rayuwarsu ne ya kawo musu ɗauki har suka samu yanci dukda hakan kuma suna gabatar da rayuwarsu ne cikin takatsantsan dan ya sha tambayarta mai yasa bai taɓa ganinta da wata da sunan ƙawarta ba sai ta ce Ummansu ta hana wai bata so suyi ƙawaye kada zuciyarsu ta ringa ƙawata musu abubuwan da basu da halin mallaka dan haka bata da wata ƙawa daga unguwa har makaranta kuwa sai dai yayan yan uwa da ya kan gansu jefi jefi.

A saninsa kuma babu in da suke zuwa daga makarantar boko sai Islamiyya kuma suk inda zasu je ɗin cikin shigar Hijabi harda safa da Niƙab babu wata suffa ta a tattare dasu da zata taɓa bayar da hanyar da za'a zargesu da wani abu mara kyau. Ashe dai su ɗin Abin tsoro ne wai KURA A RUMBU.

Kalaman Kawun su zuwan da yayi suka ringa masa yawo a kai kamar tilawa ya ringa haɗasu da labarukan da take bashi akan sharrin da Kawun nasu yake musu dalilin karatun jami'ar da shi ya ɗauki nauyinta amma Kawun sai ya ce yawon lalatarta kawai takeyi ba wani karatu ba da yanda ta ce mutanen unguwa suna surutu akan alaƙarsu ana cewa iskanci sukeyi shiyasa yake wahalta mata ashe duk raina masa wayau kawai ta ringayi tsayin lokaci Allah kaɗai ya san irin rayuwar da take yi a bayan idonsa.

Haka ya raba dare har asuba yana tunani, sai da aka kira sallah kafin ya tashi daƙyar saboda ciwon kai ga cikinsa daya ɗaure kamar an saka masa dutse. Haka ya lallaɓa yayi alwala, dukda haushinta da yake ji haka nan zuciyarsa ta tilasta masa zuwa tashinta. Munsharinta yayi masa maraba, sabon baƙin ciki ya turnuƙeshi. Fitilun ɗakin ya kunna gaba ɗaya haske ya gauraye ko ina a zatonsa irin Halima ce da duk baccin da takeyi aka kunna fitila sai ta farka amma ina Zulaihan kamar matacciya munshari kawai take ja.

Ya matsa yana ƙarewa gadon da ya ɓaci da jini sai kace wanda aka yanka kaza a kai, mamaki ya kamshi, daga ina aka samu jinin b dai daga jikinta ba? Domin shi dai ya san free get ya wuce sai dai idan kuma shine ya zubar da jinin ba zaiyi mamaki ba. Sai lokacin ya tuna da zaiyi wanka ma yaga jinin a jikinsa amma da yake lokacin ba'a nutse yake ba bai mayar da hankali ba. A saitin kanta ya tsaya yana matse fuska, ji yake kamar ya sharara mata mari a baƙar fuskarta da yaga tayi masa muni irin wanda bai taɓa ganinta da shi ba.

Ya ringa kokawa da zuciyarsa dake ingizashi akan wai ya sharara mata mari ta tashi tayi masa bayanin abinda yake ci masa zuciya amma ya kasa ƙarshe ya shiga kiran sunanta ya ringa maimaitawa amma ko gezau baiga alamar zata amsa ba sai ya shiga dukan katakon gadon nan ma ya fi minti biyar kafin tayi juyi cikin muryar bacci take cewa
"wai meye haka dan Allah ka rabu da ni bacci nakeji"

"Ki tashi, kalli fa cikin ƙazantar da kike kwance" ya bata amsa yana sake kallon gadon, tayi tsaki kawai tana sake gyara kwanciya, ya kai mata duka mai zafi ta zabura ta miƙe zaune kamar zata mayar da martanin dukan amma ta tsaya tana hararasa da manyan idanuwanta da yaji shakkar kallonsu ta kamashi. Ganin ta tashi zaune ya saka ya juya yana ce mata
"Ki tashi kiyi sallah" ya fice daga ɗakin haushin kansa yana kama shi.

Tsaki tayi ta koma baccinta ba tareda tayi abinda ya ce ɗin ba. Bilal kuwa a kan dardumar daya yi sallah bacci ya kwashe shi dama ga gajiya bai farka ba sai ƙarfe tara da mintuna sakamakon bugun ƙofar da ya ringa jiyowa kamar za'a karyata.

Ya tashi zaune daƙyar yana dafe kansa da a maimakon baccin da yayi ya saka ciwon ya ragu ƙaruwa ma yayi, dai dai lokacin Zulaiha kuma ta fito daga ɗakin ɗaure da towel wanda da kaɗan ya wuce mazaunanta jikinta da kumfa alamar wanka takeyi bugun ya fito da ita, suna haɗa ido ta watsa masa wani shegen kallo kamar wacce taga kashi tayi ƙofa tana sakin ƙaramin tsaki. Ya kira sunanta da dasasshiyar murya ta tsaya ba tareda ta waiga ta kalle shi ba, a hankali ya miƙe yana dafa kansa sai da ya isa kusa da ita kafin ya ce

"A haka zaki fita saboda bakida hankali?"
"Aa daga turu aka kwantoni ƙarewar hauka, da kana ji ashe tsabar wulaƙanci baka tashi ka buɗe musu ba". Tsayawa yayi yana kallonta da mamaki ita kuwa ko a jikinta ta juya ɗaki tana kaɗa masa mazaune. Ya haɗiye abinda ya tsaya masa a maƙogaro kafin ya fita jin masu bugun basu da niyyar dainawa.

Ƙawayenta na jiya ne su huɗu Suby kaɗai ya gane a cikinsu, ya matsa suka shigo fuska a haɗe babu ko wacce ta gaida shi suka wuce ciki da kayan da suka taho dasu kwalin Tv sai ƙananan kwalaye da bai san menene a ciki ba haka ya rakasu da ido har suka shige falon yana jiyo yanda suka fasa ihu da alama su da Zulaihan ne abin mamaki sai kawai ya mayar da ƙofar ya rufe ya wuce ɗakinsa yana sauke ajiyar zuciya kamar wani maraya.

Kwanciya yayi ya sake faɗawa tunani, babban abinda yake damunsa, har ransa haushin Zulaiha yakeji kamar ya kamata ua rufeta da duka har sai yaji yanda akayi tayi masa wannan cin amanar amma kuma a hakan bai ji ko ɗigo ɗaya na daga son da yake mata ya ragu a zuciyarsa ba. Tun daren jiya yake ayyana gari na wayewa zai ce ta tattara ta wuce gidansu ba zai iya zama da ita ba amma kuma zuciyarsa ta kasa bashi haɗin kai akan hakan.

Ya ɗauki wayarsa daya bari a ɗakin tun daren jiyan ya kunna amma kuma ya rasa wa zai kira ya raba baƙin ciki da shi ko zai samu sauƙin abinda yakeji a ransa. Dariya za'a masa ma, ba yan uwa ba ba abokai ba ya tabbatar muddin wani ya san halin da ya tsinci kansa sai ya shiga uku a gari.

Haka ya ringa juyi yana jiyo ihu da hargowar Zulaiha da ƙawayenta suna da sabgogi kamar ma tsakar gidan suka fito, ƙamshin ƙwai daya ringa jiyowa ya tayar masa da yunwar daya kwana da ita. Tun yana jira yaga ta kawo masa ko tazo ta kirashi ya karya har agogo ya buga sha ɗaya ba Zulaiha babu breakfast. A waya ya kirata murya kamar wacce akawa dole ta amsa da
"Menene?" Cikin tasa muryar da yunwa da fara ɗaukewa ya ce
"Ina breakfast ɗina?" Tayi shiru kafin kuma ta kashe wayar ya tashi daƙyar ya shiga banɗaki yayi brush ya fito yana jiranta.

Zulaiha kuwa da Asuba bayan daya tasheta baccinta ta koma bata kuma farka ba sai ƙarfe tara shima saboda kiranta da Suby tayi ta sanar mata gasu nan a hanya sai lokacin ta tashi tana jinta sakayau saboda kwanciya da tayi akan katifa mai kyau ba irin siɗaɗɗiyar tasu ta gida ba. Rai fes take jinta burinta ya cika ta mallaki sahibul karɓinta Bilal ita da shi kuma mutu ka raba.

Tana son Bilal kusan akansa ta fara sanin menene so dukda kafin shi tayi soyayyar ƙuruciya da wani yaro Nura a tsohuwar unguwar su. Yaron babansa nada kuɗi da wannan kuma ya ringa hillatarta da yake ita ɗin Allah yayita da ƙwadayi da son cin daɗi sai dai kuma sun tashi a gidan da ci uku ma wahala yake musu a lokuta da yawa. Da wannan yaron mai suna Nura yayi amfani ya ringa siya mata kayan ƙwalama da sunan yana sonta, lokacin data shiga JS1 ya ce zata ringa zuwa gidansu ta haɗu da ƙannensa a ringa yi musu extra lesson tunda ya fahimci tana da ƙoƙari da kuma son karatu.

Ummansu wacce ita ce sila ko ace musabbabin lalacewarta ta goyawa abun baya dukda mahaifinsu ya nuna ƙin amincewa amma tayi masa tatas kamar yanda ta saba duk sanda magana ta tashi akan yaran sai ta ce yanda ya barta dasu baya tsinana musu komai karya kuskura yace zai ringa tsoma musu baki a sabgoginsu. Shikenan ta fara zuwa extra lesson wanda ba karatun sukeyi ba ɗakinsa yake kaita tun bata son abinda yakeyi mata har ta saba ya zama ko bai kirata ba ko ba ranar lesson ɗin ba zatayi ƙaryar zuwa wani guri ta tafi gurin Nura, tun a lokacin kuma mutane da yawa sun sha kaiwa Ummansu maganar saboda ba a iya gidansu ba har shagunan abokansa suke zuwa amma duk wanda ya faɗa mata zagi da cin mutunchi ne zai raba su tace an yiwa yarta ƙazafi.
Chapter 126 · 0% Book details