← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 104 OF 158

Sashe 104

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kasa motsawa yayi daga in da yake ya dafe kai da hannu biyu ya tafi laluben ya zaiyi? Yau da ace iya Halima ce kaɗai ma zai iya cewa da dama dama domin ya san yanda ta iya riƙe wancan sirrin wannan ma ba zata taɓa tonawa ba amma yanzu harda wannan ƙanin nata da ya fi kowa tsanar sa da tsanar zamansa tareda Halimar.

Wai har tun yaushe ma suka shigo gidan har suka shigo falon bai sani ba? Shi da kunnen sa yake kamar na maciji ko yaya motsi yake zai ji amma ya akayi har aka buɗe gidan aka shigo bai sani ba duk bai ji ba?

"Ta ina zakaji bayan tunaninka da nutuswarka sun yi nisa a cikin aikata saɓon ubangiji?" Zuciyarsa ta tuna sar dashi.

Hannu biyu ya zura yana barbaza gashin kansa a fili cikin sauti kamar zai fasa kuka ya ce
"Na kwafsa, tun farko ma mai ya sa na biyewa Jalilah gashi ta kaini ta baro waya sani ma ko ita ta shirya komai ta kira Haliman?" Shiru yayi saboda tunanin daya ɗarsu a ransa, haka kawai Halima ba zata zo gidan ba ya sani dole wani ne ya gaya mata ko dai Jalilan da kanta ko kuma wani a yan unguwar ya ganshi yayi mata waya ya gaya mata.

Ta shi yayi da sauri ya mayar da rigarsa ya fito dukda bashi da tabbacin sun tafi ko suna nan, cikin sa'a yana buɗe ƙofar kuwa yaga mota a tsaye. Sai da ya tattaro duka ƙarfin halin da yayi masa saura ƙafin ya shiga ƙwanƙwasa window gefen da take zaune.

HALIMA

*KURA A RUMBU*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 44*

Kafin na kai ga buɗewa Mu'azzam ya ɓalle murfin motar ya fita da sauri, gefe suka matsa, ina kallon su amma ban san mai ya cewa Bilal ɗin ba na dai ga ya kama baki da hannu biyu cikin alamar ninkuwar tashin hankalin da ya fito dashi akan fuskarsa kafin Mu'azzam ɗin ya nufo mota shi kuma ya biyo shi sai dai bai ko sake kallon sa ba ya shiga motar ya tayar.

Na waiwaya ina kallon Bilal da ya bi motar da kallo cikin tashin hankali kafin na rufe ido na hoton ganin da na musu tar tamkar a lokacin abun yake faruwa take na sake fashewa da kuka har muryata na sarƙewa. Ci kanki Mu'azzam bai ce mun ba sai gudu da yake fellawa a titi kamar zamu bar gari hakan kaɗai kuma ya isa ya sanar mun da ransa a ɓace yake.

Na ɗauka a yanayin da nake zaiyi tunanin mayar da ni gida ne amma akasin haka sai naga ya ɗauki hanyar Jambulo, daƙyar na iya ce masa

"Ka mayar dani gida" ai kuwa kamar yana jira ya taso mun yana cewa
"Iya abinda kika gani yanzu ya isa idan har ba dusace a cikin kanki ba ki gane ya kamata ki nemawa rayuwarki ma'ana ko dan saboda gobenki" ya ja tsaki mai ƙarfi kafin ya mayar da hankalinsa kan tuƙi.

Ban sake cewa komai ba na mayar da kaina tsakanin cinyoyina ina jin wani abu na mun yawo tsakanin maƙoshi ga amai dake taso mun haka kaina yanda kasan ana kiɗan ƙwarya a ciki kai gaba ɗaya duniyar ma juyamun takeyi. Da muka isa ban ko yi yunƙurin motsawa ba dan bana jin akwai sauran ƙarfin da zai iya riƙe ni a tattare da jikina.

Uncle Mudassir ya kira a waya, ban san mai ya ce masa ba ya fita ya shiga gurin shi kaɗai ya ɗan jima kafin suka fito tareda wani mutum babba. Ƙofar ɓangaren da nake ya buɗe na ɗaga kai daƙyar na kalle su, mutumin ya ce
"Subhanallah, mai yasa zaku fito tana jin jiki haka? ai da ya kirani kawai ya gaya mun idan ya so daga baya sai ta zo".

Baki Mu'azzam ya taɓe ya ce
"A hanya rashin lafiyar ta sameta ai"
"Ikon Allah, toh Allah ya bada lafiya amma ya kamata ku wuce asibiti daga nan gaskiya" mutumin ya sake faɗa kafin ya juya ciki tareda Mu'azzam ɗin. Bai jima ba ya fito, a jikina ya watsa mun posting letter da state ID card ɗina suka zube nan ƙasa ban ko bi ta kansu ba nima dan ta kaina nakeyi. Har muka je gidan bai sake ce mun komai ba, sai da ya gama daidaita parking kafin na kalle shi daƙyar hawaye na ziraro mun na ce

"In roƙe ka alfarma?"
"Idan ma ɗaukar ki zaki ce nayi wlh ba zan ba" ya faɗa na girgiza kai lokaci ɗaya ina fashewa da sabon kuka na ce
"Dan girman Allah kada ka faɗawa kowa abinda ya faru".

Buɗe baki yayi yana kallo na cike da mamaki, na kamo hannunsa ina cigaba da kukan na ce
"Dan Allah ka rufa mun asiri, kada ka duba ni ko shi ka duba Al'amin da Sharifa kada ka janyo...." Fizge hannun sa yayi da ƙarfi ya buɗe motar ya fita, ban san ta inda na samu ƙarfin da na fita na bishi da sauri ina kiran sunansa ba amma ko tsayawa bai yi ba. Dab da zan shiga falo na taka step na farko ina ɗaga ƙafa zan taka na biyu juya ta ɗebe ni lokaci ɗaya wani duhu ya mamaye idanuwana ji da ganina suka ɗauke a lokaci ɗaya daga nan ban sake sanin mai ya faru ba kawai na farka na ganni a gadon asibiti.

BILAL
Ya fi minti biyar a tsaye yana kallon hanya dukda tuni motar su ta ɓacewa ganinsa. Yanda kasan wanda yake gaban tandar waina haka zufa take keto masa saboda sabon tashin hankalin da ya riska bayan wanda yake ciki.

"Shawara ɗaya zan baka shine ka fita daga rayuwar yar uwata, idan kuma ba haka ba ka kuka da kanka domin ina da hoto da kuma video abinda muka tarar da kai kana yi zan kuna watsa shi a duniya kowa ya gani dan ba zai yuwu yar uwata ta cigaba da shaƙar baƙin ciki ita kaɗai ba" abinda Mu'azzam ɗin ya faɗa masa kenan daya fito daga motar bai kuma tsaya ya bashi damar cewa wani abu ba ya juya ya tafi.

Shi yanzu ina zai tsoma rayuwar sa yaji sanyi? Idan ta tabba Mu'azzam ya ɗauke hoton su ai ya gama yawo domin ya san yaron farin sani bashi da mutunchi kuma dama can ba ƙaunar sa yakeyi ba tsaf zai aikata masa abinda ya ambata. Komawa yayi ciki yana jan ƙafa kamar wanda ya sauka daga iskokai, a falon Halima ya zauna kan kujera ya dafe kai da hannu biyu cikin tsananin tashin hankali da rashin sanin madafa.

Duk Jalilah ce ta janyo masa, shiyasa tun jiyan data kira shi kwata kwata bai yi farin ciki ba jikin sa kuma ya ringa bashi kamar akwai wani sharri dake tareda ita ilai kuwa gashi nan ta jefa shi a masifa.

Ya shafe sama da awa biyu a zaune a gurin yana sharce zufa dan tunanin sa ma ya ƙi tsayuwa guri ɗaya balle ya nemi mafita, Jalilah ko tana cikin ɗaki tana bacci abunta tamkar babu abinda ya faru. Ana ƙwala kiran Azahar ya jiyo ana buga get. Zabura yayi ya miƙe, abinda ya fara zuwar masa yan gidansu Halima ne suka zo kwashe kaya shikenan ta faru ta ƙare wai an yi wa mai dami ɗaya sata.

Kasa fita yayi ya buɗe sai da ya ji bugun na ƙaruwa nan kuma ya shiga tunanin idan Jalilah ta farka wani sabon case ɗin ne dan haka ba shiri ya fita. Wayar sa ya ɗauka a bayan pillow daya ɓoyeta kafin ya fita ya tsaya daga baya yana tambayar waye?

Muryar Fadila ya ji ta saka shi sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi hankalin sa ya ɗan kwanta, amma kuma daya tuna lokaci da kuma irin bugun da takeyi ya san ba haka kawai ta kawota ba, to ko yan gidansu ya turawa? Amma kuwa da ya gama dashi. Har wasu maiƙon hawaye yaji a idon sa saboda tunanin da yayi, amma kuma ai cewa yayi idan ya sake takurawa Halima yanzu kuma shi ko bin su bai yi ba ma ai.

Cigaba da buga ƙofar da tayi da ƙarfi ya saka ya zura muƙulli ya buɗe, tare hanya yayi ganin tana ƙoƙarin shiga ya ce

"Ke meye haka? Ina zaki je?"
"Dan Allah ka matsa na shiga ni na gaji ka san uwar ranar dana kwaso kuwa? Sannan minti na nawa a tsaye ina bugu baka buɗe ba" ta bashi amsa tana ƙoƙarin raɓe shi ta shiga amma ya hanata. Babu wasa ya ce

"Ke baki da hankali ko kwai mace a gidan ne da zaki ce zaki shiga ne?"

Tsayawa tayi ta kalle shi daga sama har ƙasa ta ce
"Lallai ma Yaya Bilal sai kace ni ɗin ba muharramarka bace ko kuwa ma yau na fara zuwa gidan Haliman bata nan?"

"To na canza tsari daga yanzu ba zaki sake shiga ba sai matar gidan ta dawo" ya bata amsa yana sake babbake ƙofar. Shiru tayi kamar mai nazarinsa kafin ta ce

"Sai dai idan kuma wani abun kake ɓoyewa a ciki da baka so a gani"

"Ke ni kike gayawa haka dan ubanki sa'anki ne ni?" Ya taso mata. Tayi baya tana magana ƙasa ƙasa ta ce
"Zancen gaskiya dai ai ga alamun rashin gaskiya nan sun bayyana a tareda kai"

"Bar nan kafin na saɓa miki" ya faɗa yana nuna mata hanya, ta harareshi kafin ta ce
"Toh Hajja ce ta aiko ni in kira mata kai kuma tace kazo yanzu yanzu take son ganinka tun safe akw ta neman ka a waya ka kashe har Yaya Hafiz ta kira ya ce baka je Office ba shiyasa ma tace na zo gidan ƙila kana nan".
Chapter 104 · 0% Book details