← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 82 OF 158

Sashe 82

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ban taɓa zaton haka kake ba Bilal, ka ci amanar So da yarda. Bilal mai nayi maka a rayuwa da ka zaɓi saka halaccin da na maka ta wannan hanyar? Laifi ne da na So ka na ce sai kai? Laifi ne da na fifita farincikin ka a kan na kowa? Dame na rage ka? Ta ina na gaza daka zaɓi zubar da ƙimarka da mutunchin ka haɗi da barin ubangijin ka ta hanyar aikata abinda yayi hani da? Bilal Zina da aurenka?.... "

"Wlh kika sake cewa tak Halima sai nayi miki abinda baki taɓa zato ba" ya katseni cikin hargagin da saida yayan hanjina suka juya. Ya nufoni idanunsa jajir har wani jirkicewa sukayi ya nunani ya ce
"Ki iya bakinki ki kuma san abinda kike furtawa idan ba haka ba" ya kaɗa yatsunsa biyu akan fuskata. Na haɗe yawu daƙyar saboda har ga Allah na tsorata da yanayin sa, ban kuma sake cewa komai ba kawai na maida kaina gefe hawaye suka shiga ziraro mun. Wannan shine a dake ka kuma a hanaka kuka, wannan naɗe tabarmar kunyar da yakeyi cikin hauka kuma ya sake tabbatar mun da cewar duk abinda na gani gaskiya ne. To ta yaya ma zai ƙaryata bayan da idona da kuma kunnuwana na ga shaida kuma a wayar sa ba wai wani ne ya faɗa mun ba?

Sai bayan sallar Isha'i likitan ya bamu sallama, dana sakko daga gadon zuciyata ta raya mun in fita na tari Adaidaita na tafi gidan mu sai lokacin na tuna banga yara na ba. Ina tsaye bakin ƙofar reception ya taho bayan yayi settling bill ya tsaya ba tareda ya kalleni ba yace "muje mana"
"Ina yarana?" Na tambaye shi yayi gaba yana cewa

"Suna gidan Alhaji Sani" (Gidan Maman Yusuf) shine dalilin daya saka na bishi na kwanta a bayan motar ganin ya nufi wata hanyar daban ba wadda zata kaimu gida ba kamar nayi masa magana sai kuma nayi shiru kawai. Can wani gurin siyar da kayan ciye ciye mukaje, ya fita ya barni ya ɗan jima saboda layi kafin ya dawo yana shigowa motar naji ƙamshin gashi ko Kaza ko Nama ga wata ledar da nake zaton Fura ce ko Yoghurt ya aje su a sit ɗin gaba ya tayar da motar. Ko kusan burgeni banji yayi ba, a lokacin Allah Allah kawai nake mu isa gida naga yarana daga nan na zauna nayiwa kaina karatun abinda zai fishsheni.

Ɗaki na wuce kai tsaye na faɗa wanka dan shi nafi buƙata a lokacin, ina wankan ina kukan daya rigada ya zame mun aboki a kwana biyun. Dana fito na jiyo surutai a falo dan haka na zura Hijab na fita na tarar da Maman Yusuf ce da Anty Amina kishiyarta sai Al'amin da su Kursum da Alina suke guje guje. Sannu suka shiga jera mun, na samu guri na zauna ina ɗan murmushi. Maman Yusuf ta ce

"Sannu Halima kinga ki har kin ɗan marmaro fuskarki ta ciki ba kamar ɗazu ba" ni dai nayi murmushi ba tareda nace komai ba sai ta sake cewa

"Ina fita muka ci karo da Baban nasu ai nasan ba lallai kin san ma ya aka fita dake ba dan naga kamar suma kikayi" sai tayi ƙasa da murya kafin ta ce
"Ya kuwa kira yan gidanku naga kun dawo ku kaɗai?"

Murmushi nayi nace
"Eh sunje asibitin" ta gyara zama ta ce
"Toh, ɗazun ne naga da nace ya kira iyayenki ya gaya musu kinga yanda ya hayayyaƙo mun kamar zai rufeni da duka nace toh ko shima irin mazan nan ne da basa son faɗa idan wani abu ya faru a gidan su?"

"Yo rashin lafiya kuma menene abun ɓoyewa ai kamata yayi ma ace iyayen su za'a fara kira a gaya musu idan abu yazo da ƙarar kwana ai dole a kirasu ace an mutu ai" Anty Amina ta faɗa suka jigaba da jajanta mun kafin shigowar Bilal ta saka suka miƙe Maman Yusuf na cewa
"Ko dai mu tafi da Sharifa a ƙarasa yayen kawai?" Nayi yar dariya tace
"Ai bama ta da damuwa naga taci abincin ta sosai suka sha wasa tayi bacci ko sau ɗaya batayi kuka ba". Har get na raka su ina musu godiya, a kitchen na hango shi yana ƙoƙarin ɗumama kaza a microwave na wuce ɗaki na kimtsa kaina, bana jin yunwa ko dan ruwan da aka saka mun ne dan haka nayi sallolin da suke kaina bayan na idar na haye gado na kwanta. Bilal ya sake shigowa ɗakin a karo na uku dan sau biyu yana shiga sanda ina sallah, ya kwantar da Sharifa da tayi bacci akan gado kafin ya tsaya a kaina yana kiran sunana.

Ban amsa ba haka nan ban motsa ba, ya miƙa hannu ya taɓa ƙafata na buɗe ido da sauri na kalle shi yayi gajeran tsaki ya ce
"Da idonki biyu dan wulaƙanci kina ji na kenan kika yi shiru" ban tanka masa ba ya sake cewa

"Ki taso kici abinci ki sha maganinki". Sai lokacin na tashi zaune na kalle shi nace
"Har yaushe ka fara damuwa dani ko lafiya Bilal?"
"Halima kada ki tunzura ni, ina duk iya ƙoƙarin da zanyi naga na biki a hankali amma naga alama magana kike so ki jani da ita. Rashin kunya da zagina da kika yi basu isheki ba so kike ki ƙara wani" ya faɗa yana harɗe hannayen sa a ƙirji. Sai na tashi zaune da kyau na sauke ƙafafu ƙasa na fuskance shi na ce

"Ƙwarai magana nake so muyi". Ya zuba mun idanunsa da suka canza launi kafin ya ja stool ɗin gaban mudubi ya zauna ya ce
"Ina sauraronki".

"Ka dubi Allah ka faɗa mun gaskiya Bilal dame na rageka a zamantakewarmu?" Na faɗa bayan shirun kusan minti biyu da nayi ina ƙoƙarin kamo ta inda zan fara magana, yayi tsaki ya ce
"Idan kina da magana mai muhimmanci kiyi"
"Wannan ita tafi komai muhimmanci a gurina domin ina so na san cikin zunubin ka ina da kaso ko babu" nima na katse shi, sai ya kalleni kafin ya ɗauke kai gefe ba tareda yace komai ba. Kukan da ban so zuwan sa a lokacin ba ya ƙwace mun dukda haka na ce

"Mai ya baka sha'awa a matan bariki Bilal? Mai ka taɓa nema nayi maka banyi ba daka gwammace ka fita ka nema a waje?"

"Kina ji ko Halima kowanne mutum da kika gani a rayuwa yana da kuskuren sa kuma da za'a ce kowa a tona nasa da ba lallai a samu sauran wanda za'a ringa yiwa kallon mutumin kirki ba a duniyar nan, idan da kina da tunani bai kamata ki bari abinda kika gani ya dameki har ki nemi ki hallaka kanki a banza da damuwa ba, kuma duk maganganun da kike faɗa kawai ina miki uzuri ne kuma ko da kike wannan surutun baki da qata shaida akan abinda kike zargin na aikata. Abinda kika gani kawai normal abu ne tsakanin Saurayi da budurwa amma gaba ɗaya kin wani mayar dashi kamar wacce kika kamani turmi da taɓarya da ita, idan ba ban yafe miki ba sai Allah ya bi mun kadin ƙazafin da kike mun domin baki da hujja" ya faɗa ba tareda ya kalleni ba.

Ni ko tunda ya fara magana hawayen da nakeyi suka tsaya, zuciyata ta shiga bugawa da ƙarfi mamakin ƙarfin halinsa da kalaman da yake furtawa suka sumar dani a gurin da nake zaune. Ban san sanda na ce

"Ashe har kana da bakin da zaka iya kare kanka Bilal? Bilal da idona fa na gani na kuma saurari irin fasiƙancin da kakeyi sannan har ka iya buɗe baki kace wai da ina da tunani bazan bari abun ya dameni ba Normal ne, Zina ce ta zama Normal a gurinka? Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un Bilal ina iliminka ina saninka na addini da har ka bari duniya ta rufe maka ido kake kiran Zina da Normal abu?" Na ƙarasa ina sakkowa ƙasa kan guiwoyina. Sai ya miƙe cikin fusata ya ce

"Halima idan kika sake dangantani da Zina wlh sai kin sha mamaki na"
"Ka faɗa mun abinda ya kamata na danganta dashi toh Bilal idan ban kiraka da Mazin...." Marin da ya kai mun ya hanani karasa maganar dana fara, sai da na wuntsila gefe saboda yanda marin ya shige ni na fasa kuka mai tafe da ƙara lokaci ɗaya Sharifa ma ta farka ta fasa mata kukan. Ko a jikin sa ya shiga cewa

"So kike sai kin ƙure haƙuri na, da zaki ringa ce mun Mazinaci da uwarki nayi Zinar?"
Tamkar dukan guduma haka naji maganar a kunnuwa, yau Bilal ne yake wannan zagin na rashin mutunchi? Ban dawo daga shock ɗin farko ba yaci gaba da cewa
"Ki ɗauki duk matakin da kike ganin yayi miki Halima idan kinga dama ki tafi gidan Radio ki siyi fili ki faɗawa duniya kinga ina Sex Chat da mace, amma kafin nan ki sani kanki zaki zubarwa da mutunchi bani ba. Duk inda kika ɗauki laifina kika kai kafin a saurareki sai an miki dariya ko kin manta kin zaɓeni akan kowa da komai naki? Duk kuma aje a dawo ba zaki taɓa iya rayuwa babu ni ba dan haka zaɓi ya rage naki ko kiyi haƙuri da abinda kika gani mu cigaba da zamanmu cikin rufin asiri ko kuma ki tafi ki zubar mana da mutunchi kuma ki dawo ɗin mu zauna, zaɓi ya rage naki" ya ƙarasa yana watsa hannaye alamar matsalata ce ba tashi ba kafin yasa kai ya fice daga ɗakin.
Chapter 82 · 0% Book details