← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 102 OF 158

Sashe 102

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har raina naji daɗi dan dole ai yanzu a fasa fitar, falon na fito, ina buɗe ƙofa muka haɗa ido da Abba dake tsaye da alama kuma ni yake jira. Kamar munafuka sum sum na zube a ƙasa murya ba amo na shiga gaishe shi, bai amsa ba sai cewa da yayi cikin dakewa

"Tashi ku tafi".

Nayi diriri a tsugunne ina ji Mama na cewa
"Da dai ta karya ko?"
"Idan sun dawo sai ta karya yanzu Mudassir ya kirani mutumin yana ta masa waya".

"Sai ku wuce ku tafi ai" Mama ta faɗa, na miƙe kamar kazar da aka tsamo daga ruwan zafi na nufi ƙofa Abban ya dakatar dani yana cewa
"Ina uniform ɗin?"

"Suna can gidan ai" na bashi amsa ina kallon ƙasa. Da hannu ya mun alamar mu je, Mu'azzam yayi caraf ya ce
"Bafa zasu barta ta shiga a haka ba yanzu doka na aiki ko colored hijan ba'a shiga dashi secretariat balle taje musu da kayan gida, kalli shigar da ta yi ga fuskar ta duk a kumbure ɗauka za suyi ma mabaraciya ce".

"Kuma dai? To sai ku bari sai gobe ai a cigita ko a cikin unguwa ai ba za'a rasa masu service ɗin ba su bata aron uniform ɗin kan ta ɗinka wani" Mama t faɗa, sanyi na ji har raina sai dai kuma murnata ta koma ciki jin Abba ya ce

"Tunda uniform ɗin makaranta ne da zaki ce ta aro? Su biya ta can gidan ta ɗakko ko babu muƙulli a hannunki?" Ya ƙarasa yana kallona. Yau ɗin ganinsa nake wani daban kamar ba Abba na mai yawan fara'a da wasa da dariya ba, da sauri na ɗaga masa kai alamar akwai kafin na juya cikin ɗaki na ɗakko muƙullin dan yana ajiye dama a kan mudubi.

Har muka isa layin gidan ci kanki Mu'azzam bai ce mun ba nima kuma tawa ta ishe ni tunda na haɗa kai da window ban ko motsa ba sai da naji ya tsaya na duba na ganmu a ƙofar gidan.

Karki ɓata mun lokaci Malama" ya faɗa yana wani ɓata rai kamar shine gaba dani, haka nan na ringa jin wani iri a jikina. Na kalli layin daga farko har ƙarshe ina tuna ranar da na bar gidan. Sammani mai gadin gidan Maman Yusuf ya taso da sauri gani na, dole na ƙago murmuyna ɗora akan fuskata sanda muke gaisawa ya ce

"Kin dawo Hajiya?"
"Abu nazo ɗauka dai amma dan Allah karka gayawa su Maman Yusuf na zo dan sauri nakeyi ba zan samu damar shigar musu ba" na bashi amsa. Yana shafa kai ya ce
"Ai bata nan ma Hajiyar tana Umarah, Amarya kuma ai ta bar gidan kin san Alhaji ya ƙara aure shine ta tayar da rigima har dai sai da ya saketa yau kwanata huɗu da tafiya ita Hajiya tana can Saudiyya ma duk bata san meya faru ba".

"Allah ya rufa asiri" na faɗa ina zura key a jikin ƙofa har cikin raina kuma banji daɗin sakin Maman Khadija da ya ce anyi ba, na tuna yanda suka ringa kirana a waya suna bani baki akan nayi haƙuri na dawo aure duk zaman haƙuri akeyi dan duk a zaton su da sauran yan unguwa sakina Bilal yayi ashe itama nata sakin na tafe.

Ganin motar sa ajiye ya saka nayi turus dan ban zaci zamu iya samunsa a gidan ba musamman tunda yau ɗin akwai aiki kuma lokaci ya fara ja dan sha ɗaya har ta gota. Ji nayi kamar an ƙara bugun da zuciyata take yi, na yi taku biyu da niyyar in basar amma naji ba zan iya ba. Komawa nayi waje, ba tareda na kullo ƙofar gidan ba na buɗe mota na shiga.

Mu'azzam ya kashe wayar da yake ansawa yana kallo na ya ce
"Har kin ɗakko?"
"Yana gidan ba zan iya shiga ba" na bashi amsa ina dafe ƙirji na da hannu biyu saboda yanda bugun da zuciyata yakeyi na ke jinsa kamar numfashi na zai ɗauke. Tsaki yayi ya kashe motar ya fita yana cewa

"Muje, dukanki zai ko me da zaki ce ba zaki iya shiga ba?"

Sai da ya shiga gidan kafin nayi ƙarfin halin bin bayan sa. Banyi mamakin ganin ƙofar falon a buɗe ba tunda ga motarsa a gida, babu kowa a ciki ko ina tsaf tsaf hakan kuma ba sabon abu bane a guri na tunda na san wanene Bilal gurin tsafta. Ɗaki na na wuce Mu'azzam kuma ya tsaya, nayi turus ganin kan gadon a hargitse alamar ba'a jima da tashi daga bacci ba ga kuma wani ƙamshi da nake jin kamar ma sanshi a wani guri.

Bugun zuciya ta ne ya ƙaru sai dai ban bari tsoro da firgicin dake taso mun sunyi tasiri ba na wuce in da na ajiye ledar kayan tun ranar da na je camp na ɗauka na buɗe su har sun fara warin ajiya dama ga warin sabuntaka suna yi.

Kayan jikina na cire na saka KHAKIn, yanda ka san kyanwa haka nayi wata yar tsurut a cikinsu. Dama sunyi mun yawa tun ranar dana dawo na duba naga over size ne, nayi niyyar na bayar a rage mun sai dai kuma ban samu damar hakan ba abinda ya faru ya wakana. Cikin kayana na buɗe komai yana nan yanda na barshi na ɗakko Abayar da na tanada saboda fita da Khaki na saka sannan na ɗakko farin PLAIN VEIL cikin waɗanda na siya gurin *MARYAM ALL IN ONE EMPORIUM*. Hansa'u ce ta haɗa ni da ita lokacin da muka taɓa yin hira nace mata ina so na fara gwada kasuwanci tace mai zai hana na gwada siyar da mayafi musamman *PLAIN CHIFFON VEILS* da kasuwar su take ci a yanzu gurin yammata da matan aure. Shine ta bani number ta na siyi half dozen na amfani na kafin na samu kuɗi na saro wanda zan fara siyarwa.

Na yaba da kyawun yadikan da kuma quality domin idan ba an faɗa maka ba zaka iya ɗauka irin na Egypt ne. Abinda ya fi burgeni sauƙin farashinta domin har tambaya nayi naji yana ƙasa da na kasuwa kuma ya fi shi kyau ga colors irin wanda sai kayi zuwa nawa kasuwar ma baka samo su ba ƙarin daɗi tana delivery zuwa ko ina a faɗin Nigeria abinda kuma ka siya shi za'a kawo maka.
(Yar uwa mai neman sana'ar da zaki gwada kin san dai yanda kasuwar mayafai take ci a yanzu musamman PLAIN CHIFFON, ga in da zaki sara a ɗinkensu anyi packaging sai dai kawai ki tallata ki siyar ba ruwanki da wuni a sabon gari ko kwari gurin sarin mayafi.
Masu siyan ɗai ɗai muna maraba da ku muna da kowanne size daga smalla, medium har big bayan haka muna sa sauran kalolin luxury mayafai sai iya wanda kika zaɓa. Muna Kano muna aika kaya ko ina a faɗin ƙasar nan da yardar Allah a tuntuɓe mu kai tsaye akan *09064960666*).

Na ninke kayan dana cire na saka su a leda, already dama na siyi farin cambass shi na ɗakko kan shoe rag na saka dan waɗanda aka bani duk sunyi mun yawa. Wayata ta shiga ƙara na duba naga Mu'azzam ne na san zaice na daɗe dan haka ban ɗauka ba na fita daga ɗakin.

Yana ganin na ya juya fita dan dama tsaye yake a bakin kofa, na waiga ina kallon falon kamar bana so na fita daga cikin sa har hawaye ne ya tarar mun. A garin kalle kallen na hango can ƙasan kujera.

Ji nayi kamar an doka mun guduma a tsakiyar kaina, na saki ledar hannu na a ƙasa kafin na nufi gurin da sauri dan tabbatar da zahiri nake gani ko kuma gizo ido na yake yi mun?

Ɗauka nayi na shiga ƙare mata kallo tsabar yanda zuciyata take bugu tamkar zata fito ta baki, ko a lokacin da nake shayarwa duk yanda ƙirji na yake cika ban taɓa saka girman wannan size ɗin ba balle na yi tunanin ko tawa ce na, kai ni ban ma taɓa ganin irin design ɗin ba dan ko da nake a rikice tar na gane designer ce mai tsada ga kuma irin ƙamshin da na ringa ji a cikin ɗaki na nan a jikinata.

Sakinta nayi a ƙasa dai dai sanda na sakeyin wani mugun ganin, ɗan kunne, agogo harda zobe na mace akan center table. Da baya na ringa tafiya ina jin kamar ana zare mun laka, kaina ya cushe ta yanda na gagara tuna komai da ya kamata nayi a lokacin.

"Bilal ya ƙara aure" maganar Hafiz ta shiga dawo mun. Yaraf na zube kan kujera na dafe kaina da naji ya mun wani yammm kamar an barbaɗa mun yaji.

Ban san tsayin lokacin da na ɗauka a zaune ba, nesa nake jiyo muryar Mu'azzam yana mun magana amma ban fahimci komai ba sai bin sa da na ringayi da kallo, can kuma kamar an tsikareni na miƙe na fice daga falon da sauri ya biyo ni yana kiran sunana amma ban tsaya na sai da na dangana da falon Bilal.

Taimakon da ubangiji yayi mun tsayuwar Mu'azzam ɗin bayana na tabbata ba dan haka ba yanda na tafi idan da ace na samu nasarar kaiwa ƙasa tabbas a wannan karon babu lallai in warke domin da wahala idan ban samu paralyze ba. Dukda yanda nake jin jikina tamkar an saka mun shocking haka na fizge daga riƙon da Mu'azzam ya mun na juya baya domin na hana idanuwana cigaba da arangama da mummunan ganin da nayi.

Bai sakeni ba sai rungumeni da yayi lokaci ɗaya na fashe da kukan da komai dakewar zuciyar mai sauraro sai ya tausaya mun. Idanuwana a rufe suke amma hoton mugun abinda na gani yana nan tar tamkar a lokacin nake kallo, Bilal kwance kan cinyar wata mace da ban san matsayinta gare shi ba tana shayar dashi tamkar jariri.

A yanda nake a jikin Mu'azzam ya ringa tafiya da ni har ya sakani a mota, yanayin sa kaɗai ya bayyanar da shima ya shiga shock da abunda muka gani. Sama da minti goma muna zaune a motar ni ina kuka ahi kuma ya riƙe haɓarsa ya zurawa gaban motar ido.
Chapter 102 · 0% Book details