Sashe 48
Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Washe gari har azahar banga Bilal kuma babu wani daga dangin sa se yan uwana da suke ta kaikawo a gurin. A ƙa'ida da safe za'a sallame mu tunda na cike awanni shida na ƙa'ida amma da likita ya shigo duba mu ya ɗauki yaron se yace akwai alamun jundice a tare dashi dan haka ba zasu sallame mu a lokacin ba se mun ƙara 12 hours under observation idan abun is not severe da zamu iya tafiya gida tohm. Nan da nan hankali na ya tashi saboda yanda nake jin labarin jundice ance yana kashe jarirai, shaiɗan da saƙe saƙe tuni har na fara hasaso wai babyn ma mutuwa zeyi. Ina kwance nake wannan tunanin se kawai na tsinci kaina da fashewa da kuka kamar har abun ya faru ne.
Gwaggo, ƙanwar Abbanmu ta taso da sauri ta iskeni tana cewa
"Lafiya Yaya? Ko ciwon ciki ne?" Nan hankalin sauran mutanen ɗakin ya dawo kaina duk suka shiga jera tambayar meya same ni? Ko wani gurin ke yi mun ciwo ni kuwa kamar suna tunzura ni na samu guri na cigaba da Sheƙa kuka ba ji ba gani.
"Ku rabu da ita babu inda yake mata ciwo baze wuce akan wancan mijin nata da be san daraja da ƙimar ta ba take wannan kukan. Ace ka haihu gari ɗaya ba wai daga wata nisan duniya ba miji ya kasa zuwa ya duba halin da kake ciki ko abinda ka haifa ba? Ko da yake ita ta jawa kanta ba wani da dan haka namu ido".
Maganganun ta suka buɗe musu fili kowa ta shiga tofa albarkacin bakinta dukdai be wuce zagin Bilal da Ahalin sa ba.
"Ai wlh ko a wata jaha suke daga dai haihuwar ta tun jira da yamma zuwa yanzu azahar yaci ace ko mutum biyu sun taso sun zo amma ce gari ɗaya ko shi uban cikin be zo ba balle wani nasa yayi kara shima yazo? To Alla ya rufa asiri, duk irin abunda aka ringa hango mata kenan soyayya ta rufe mata ido shima Yaya Aminu ya biyewa Yaya Salamatu, dan kai ka auri mace ka mata halacci se aka ce yarka ma idan tayi irin auren zata dace? Tsabar lalacewa ma fa ase daidai da ginin gidan shi ya bashi maƙudan kuɗaɗe ya ƙarasa duk a shawarar Yaya Salamatu. Wannan yaron yace mun a gurin sa aka siyi ƙofofi da wundunan gidan yace saboda samun guri wanda ma sukayi magana da Yaya Aminun za'a bashi da yaje se cewa yayi basu yake so ba ya nuna wasu daban kuma Yayan yace a bayar. Abun nan ya daɗe yana cimun rai kawai nayi shiru ne dan kar ace a baki na magana ta fito".
Murmushi kawai Anty Labiba ta ringa yi tana gyaɗa kai irin abun ya mata daɗi, Anty Rakiya wadda yayan maza suke da su Abba tace
"Kuma shine saboda su ɗin ba gadon arziƙi bane yayi mata lefe a leda; wato bata kai ko a cikin kuɗin da uban nata ya bashi ya ragi wani abun ya siya mata akwati ba"
"Ke kuwa idan suka zubo a akwati ai abun tsiyar ƙara yawa zeyi, yo ina abun zubawa a akwatin ma banda abinki Rakiya? An dai cuci yarinya kawai an kaita an baro" Gwaggo Hajiyayye ta faɗa. Se Anty Labiba tayi caraf tace
"Ta dai cuci kanta waya mata dole a auren sa?"
Dana gaji da sauraron cin mutunchin da suke mun se kawai na tashi daga kan gadon na shige banɗaki. Tunani nake dagaske Abba ne ya bawa Bilal kuɗin daya ƙarasa ginin sa ko dai surutun su ne kawai?
Da ace Anty Labiba ce ta faɗa zan iya cewa duk cikin son ta cusa mun tsanar Bilal ne amma kuma banga hujjar da ze saka Anty Rakiya tayi ƙarya cikin wannan maganar ba, a karon farko naji haushin Bilal har zuciyata. Idan har ta tabbata dagaske Abba ne ya bashi kuɗin nan amma har ya iya buɗe baki ya kira ni da yar matsiyata ba sau ɗaya ba sau biyu ba lallai Bilal ban ma san a wane aji ya kamata na ajiye shi ba. Kuka na se ya canza salo, dama ɗazu na jin daɗi ne yanzu ko dana samu dalili me ƙarfi se na shiga kukan tausayin kaina. Bubbuga ƙofar banɗakin da akayi yasa na wanke fuskata na fito.
Abba, Baba Salahu se abokin Abba Baba Lawan ne suka zo, ban yarda mun haɗa ido ba na gaishe su Baba Salahu ya shiga tambayar meya same ni ido na ya kumbura ba kunya Anty Labiba tace wai kumburin haihuwa ne.
"Shine haka har ido kamar wadda tasha kuka?" Baba Lawan ya tambaya. Ni dai shiru nayi bance komai ba, basu jima ba suka tafi. Haka yinin ranar ya doshi ƙarewa har la'asar banga Bilal ba ban kuma ga wani daga ɓangaren sa yazo ba.
Zuwa lokacin har na rasa wane tunani zanyi akan ma'anar abinda Bilal ɗin yayi mun. Da kunne na naji Abba yana faɗar ya kirashi be amasa ba kuma ya tura masa da saƙo tun sanda aka kawo ni asibiti; sannan ni ma da kai na na kira shi da wayar Anty Labiba be amsa ba. Nama rasa wane tunani zanyi, shin yana sane yaƙi amsa wayoyin kuma yaƙi zuwa ko kuwa akwai wani al'amari daban da bamu sani ba?
Haka muka sake kwana; ƙarfe goma na safiyar washe gari aka sallame mu. Gidan mu aka wuce dani, a ɗakin Mama na kwanta dan na shiga tsohon ɗaki na in da yake na Amirah a yanzu ganin kayan ta a barbaje yasa na fahimci ba a nan zamu zauna ba ƙila ko ɗakin baƙi za'a gyara mun.
Mama Fauziyya ce tayi mun wanka, nasha kuka amma kuma naji daɗin jiki na duk gajiyar dake tare dani ta warware. Se da naci abinci kafin na kwanta, bacci nake so nayi se dai tunanin daya cunkushe mun zuciya ya hanani.
Gaba ɗaya zuciyata babu daɗi, kwanaki biyu daya kamata su zama mafiya farin cikin a rayuwata sun juye zuwa na akasin haka. Ace na haihu har kwana biyu uban ɗan yana raye amma be iya zuwa in da muke ba, idan wani ne ya gaya mun haka zata iya kasancewa tabbas bazan yarda ba se gashi ni da kaina na shaida hakan. Amma dana tafi lissafin baya tun daga goyon cikin da yanda sam ban shida irin ɗoki da farin cikin da ƙawaye na suke bani labarin mazajen su na yi ba a lokacin da suka samu ƙaruwa se banyi mamaki da abinda ya aikata mana a yanzun ba.
Na tuna sanda Hansa'u ta haihu, yar da a haifa ita ce ta goma sha biyu a jerin yayan mijinta amma hakanan ya baro abin da yake yi a Dubai in da yake kasuwancin sa ya taho a ranar ya duba su sannan ya juya ya tafi. Irin soyayyar da nayi tunanin a gurin yaro matashi sabon jini kaɗai ake samun ta se gashi rayuwar Hansa'u da Mijin ta ta ƙaryata tunani na.
Sau tari har bana son buɗe status ɗin ta saboda abubuwan da nake cin karo dasu da suke sosa mun zuciya har nake jin kamar da gayya ma take ɗorawa saboda na gani. Duk da shekarun mijinta baya kunyar su fita tare su je guraren Shaƙatawa a ciki da wajen ƙasar nan suyi hotunan da kana kallo baka buƙatar a faɗa maka su ɗin masoya ne dake cike da farin ciki. Tun da na auri Bilal sau ɗaya zan ce mun taɓa zuwa wani guri shima ba wai haka nan ba dalili ne ya kaimu birthday budurwar wani abokin aikin sa Patrick da akayi a wani garden. Duk sanda na roƙe shi da mu fita wani guri ko da gidan zoo ne mu sha iska se yace ba yanzu ba.
"Yanzu ke ba zaki ji wani iri ba na ɗauke ki a mashin kawai muje kowa suna zuwa a manyan motoci masu aji?" Abin da yake faɗa mun kenan duk sanda na masa maganar. Na kan yawan tunasar dashi akan
"Shi farin ciki babu ruwan sa da wadata. Shi yasa ma nake ce maka muje irin guraren da nasan munfi da yawan waɗan da zamu tarar wadata ƙila mu zama abin kallo ma a gurin su da bayar da sha'awa. Sannan duk ma inda muka ga damar zuwa ina ruwan mu da masu zuwa a motoci? Se ta yuwu muje mu kashe dubu ɗaya wanda yazo a ƙatuwar motar se dai kawai yayi zagaye ya tafi ba tare da ya kashe ko sisi ba ni ban san me yasa kake yawan damuwa da maganaganun mutane ba ko kallon da mutane zasu maka. A baya da kake ɗauka ta a mashin ɗin muke zuwa me yasa baka taɓa tuna za'a raina ka ba se yanzu?"
Duk sanda mukayi haka daga ƙarshe abin rigima maganar take komawa yace na raina ƙoƙarin sa ina hangen rayuwar da wasu sukeyi; idan nayi haƙuri nima wata rana zamu taka matsayin fa nake hange hangen shi kenan se ya ɗauki fushi idan ba'a yi sa'a ba se anyi kwana biyu ina bin sa da rarrashi da ban baki kafin ya sakko muci gaba da walwala a gidan.
Ƙarfe biyar bayan nayi wankan yamma babyn ma anyi masa ina zaune ina cin gasassun yan shilan da Anty Labiba ta ajiye mun Mama ta shigo ɗakin.
"Kiyi sauri ki ƙarasa kada magriba tayi ku samu ku tafi" ta faɗa daga tsayen da take.
Kallon ta nayi da rashin fahimtar abinda maganar ta take nufi. Kamar ta fahimce ni fuska babu walwala tace
"Abban ku yace ki koma can gidan ki". Se na ture kwanon gabana na fuskance ta da kyau nace