← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 158

Sashe 80

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bana son hauka da shashanci Halima. Wato saboda kinga na sake miki kwana biyu shiyasa har kika samu damar ki ajiyeni kina tuhumata kamar wani ɗan cikinki ko? Uwata ce ke ko me da kike zaton zan miki ƙarya?" Yayi maganar cikin ɗaga murya. Sai na waiga na kalli cikin falon inda Al'amin da Sharifa suke duk su biyun sun zubo mana ido da alama hargaginsa ne ya janyo hankalin su dan haka na sauke murya na ce

"Da dai kayi haƙuri ka dena wannan ihun kaga yara suna kallonka". Ai ina wuta y jefani a ciki wai mahaukaci ma na ɗauke shi kenan nace yana ihu, ya ringa surfa mun tijara kafin daga ƙarshe ya fice daga gidan gaba ɗaya garin sauri kuma ya manta wayarsa dake kan dining bai kula da ita ba. A gurin na zauna na rizgi kuka Al'amin da Sharifa suna tayani, ganin suna kukan ya saka na rarrashi kaina daƙyar nayi shiru na goya Sharifa Al'amin kuma ya kwanta akan cinyata.

Muna zaune shiru a falo kamar marayu naji ƙarar wayarsa a gurin dining, kamar kar na kula amma zuciya da shaiɗan suka ingizani ko babu komai zan samu amsoshin zarge zargen da suke mun yawo a ƙwaƙwalwa sai na janye Al'amin na miƙe kafin na kai gurin kiran ya katse na ɗauki wayar na danna. Password ɗin sa da na sani na saka suka ce wrong. Naja kujera na zauna na sake gwadawa ko ban shigar daidai bane still bata buɗe ba, tagumi nayi ina ƙoƙarin tuna wata number mai muhimmanci da zai iya sakawa a matsayin password ɗin sa daidai nan kiran ya sake shigowa gabana ya yanke ya faɗi da ganin sunan dake yawo akan screen ɗin wayar "DUNIYA TA".

Cikin son in tabbatar da cewar Hajja ce ko ba ita ba domin kuwa a zatona ita kaɗai ce zata iya samun matsayin wannan sunan a wayar Bilal tunda ni dai na san da HALIMS yayi saving number ta. A speaker na saka wayar bayan dana amsa kiran, daga can naji muryar mace cikin sautin da ban tantance haka take magana ba ko kuma shagwaɓa take masa tayi sallama take kaina ya sara, zuciyata ta shiga bugawa da sauri haka gaba ɗaya ilahirin jikina ya ɗauki rawa zufa ta shiga keto mun tamkar wadda nake a gaban murhu dukda kuwa falon a wadace yake da iskar fanka da Ac dan akwai wuta amma lokaci ɗaya naji na fara ɗigar da zufa.

Dukda a zaune nake kan kujera amma sai na ringa jin kamar a tsaye nake har jiri yana neman kayar dani dan haka na dafe table ɗin gabana da hannaye biyu muryar budurwar na cigaba da yi mun amsa kuwwa tana tana nanata "Hello, Yah Bilal kana ji na kuwa?"

Allah ne ya taimake ni ta katse wayar daga can zuwa lokacin ba wani gane komai nakeyi sosai ba dan ji nayi tamkar an ɗora mun gingimemen dutse a kaina ya danne mun ƙwaƙwalwa ya hanani tunani. Ƙarfin halin sake ɗaukar wayar nayi, tunanin gwada shekarar daya gama secondary school nayi dan yana yawan faɗar shekarar nada tarihi a rayuwar sa dukda ban san ko tarihin menene ba cikin sa'a kuwa ina sakawa wayar ta buɗe kai tsaye na dirarwa Messages ɗin sa.

Number JALILAH da na fara cin karo da saƙon ta wanda bai jima da shigowa ba dan bai ma karanta ba na buɗe. Zan iya cewa tunda nake a rayuwata ban taɓa shiga tashin hankali makamancin wanda na tsinci kaina a lokacin ba, na ringa buɗe idanuwana da suka mun nauyi suna neman rufe kansu amma naƙi basu damar hakan burina na karanta abubuwan da nake gani wanda duk kalma ɗaya nake jin ta tamkar ɗigon dalma a zuciyata. Saƙon ƙarshe da tace ya duba Whatsapp ta ajiye masa saƙo na karanta dan haka na fita daga message ɗin na koma Whatsapp.

Na miƙe tamkar wadda tasha tayi mankas ina tangaɗi goyon da nayi yana rinjayata, da bin bango na isa ɗaki na maido ƙofar na kulle da muƙulli kafin na kwance Sharifa nayi zaman dirshen a ƙasa na buɗe Whatsapp ɗin nasa. Unread messages biyar na gani wanda Jalilar ta aiko da alama kuma hotone, saboda yanda zuciyata take bugawa ji na ringayi tamkar zata fito ta bakina wani irin tsoro da ban san dalilin sa ba ya lulluɓe ni amma haka nan na buɗe chat ɗin nasu da nake jin wata murya a ƙwaƙwalwata tana ƙoƙarin hanani buɗewa sai dai aikin gama ya rigada ya gama.

Da ƙarfin gaske na runtse ido na bayan dana saki wayar daga hannu na cikin furucin da babu sauti na shiga nanata Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un sakamakon mugun ganin da nayi, nafi minti biyu ina ƙoƙarin tattare hankali da ƙoƙarin na gane a zahiri ne abubuwan da suke faruwa ko kuwa hallucination nake yi? Tamkar mai taɓa kunama haka na sake ɗakko wayar na buɗe idanuwa suka sake yin arba da mugun hoton da na gani wanda ya sake tabbatar mun zahiri ne ba wai tunani nake ba, a hankali na sake kife wayar a jikina na shiga sauke ajiyar zuciya tamkar wadda tayi gudun tsere, ratar minti ɗaya zuciya ta sake ingizani na ɗaga wayar, nayi scrolling har zuwa farkon chat ɗin su kafin na fara tilawa ina karantawa tareda sauraron muryoyin da sukayi musaya a tsakanin su duk da wata muryar tafi ƙarfin kunnuwa na su saurara ba murya ba wani rubutun kansa ya girmi ƙwaƙwalwa ta da ta karanta shi.

Na ga tashin hankalin da ko bisa kuskure wani ya alaƙanta Bilal da wannan muguwar ɗabi'ar tabbas mai rabani dashi sai Allahn daya halicce mu. Ashe dalilin daya saka ya koma kwana a ɓangaren sa kenan shine kuma dalilin zaryar da yakeyi tsakanin Kano da Abuja ya kife ni da sunan aiki yake zuwa ashe alaƙar da take tsakanin sa da JALILAr kenan?

Kasa cigaba da bin chats ɗin nayi saboda yanda abinda nake ji da gani ya ƙazanta, na kife wayar a cinyata na fashe da kukan da ni kaɗai da na ci karo da wannan baƙin cikin sai kuma wadda ta taɓa tsintar kanta wanda ta bawa dukkan yardarta a cikin irin wannan yanayin kaɗai zata iya hakaito abinda nake ji. Tabbas Bilal yaci amanata ya kuma ci amanar yarda da SO.

Tambayar da na ringa yiwa kaina dame na rage shi da har ya zaɓi wannan hanyar? Ashe ban ishe shi ba? Duk yanda nake ƙoƙarin ganin na kare masa haƙƙin sa ta yanda bazai ga haram a waje ta burge shi ba ashe shi ba haka bane a gurin sa? Da nake masa kallon wanda mace bata dame shi ba har wasu lokutan nake ganin kamar ina matsa masa da fitina ashe ni duk haukan banza na nakeyi ni ɗin ce ban isa ba ban kai macen da zai ringa nuna zalamarsa akaina ba yana tareda ni ne kawai amma hankalinsa yana kan wasu?

Na rintse ido na hotunan tsiraici JALILAH suka shiga gilma mun. Tabbas a inda mace kamarta take ni ɗin ban isa komai ba sai dai kuma a yanzu na tabbatar da Bilal ƙasurgumin munafuki ne kuma maƙaryaciya saboda yanda yasha faɗa mun shi cikar jikin Mace bata wani burgeshi yafi son komai daidai irin nawa ba wanda zai rasa yanda zaiyi dasu ba amma gashi yanzu na kamashi yana tarayyar haram da mai irin jikin da yake faɗar baya burge shi har yana faɗa mata kalaman da tunda nake dashi ni matarsa ta sunna ko kusan bai taɓa furta mun ba.

Nayi kuka tamkar raina zai fita, sai da naji numfashi na ya fara yi mun sama sama kafin na fara ƙoƙarin tsayar da kukan sai dai na kasa saboda yanda muryoyi da hotunan da suka samu mafaka a ƙwaƙwalwata suke sake jefani cikin wani yanayi. Allah kaɗai yasan ire irenta nawa yake tarayya da su tunda nata kaɗai na gani yanzu. Waya sani ko itama waccen da yayi saving da DUNIYAR SA itama irin mu'amalar da take tsakaninsu kenan?

Ina nan zaune tamkar mara rai, kukan zahiri ya tsaya mun sai na zuci da na cigaba da yi, na yunƙura daƙyar saboda buga ƙofa da kuma kukan da na jiyo Al'amin yanayi. Daƙyar na buɗe masa ƙofar dai dai lokacin kuma Bilal ya shigo falon idanunmu suka faɗa cikin na juna nayi masa kallon da ko a mafarki ban taɓa zaton zanyi masa irin sa ba, kallon tsana mai cike da dana sani da nadamar kasancewa a duniyar sa. Gurin da na taso na koma na zauna haɗi da mayar da kaina baya na ɗora akan Gado, Al'amin ya kwanta kusada Sharifa yaci gaba da baccin sa ina jiyo motsin Bilal a falo da alama wayar sa yake nema kafin na jiyo yana kiran sunana cikin sautin da ban tantance ba dan sai naji kamar muryarsa a sanyaye take.

A yanzu muryarsa tana cikin sautikan da bana fatan sauraronsu a kusa dani, muryoyin da nayi matuƙar ƙoƙarin koresu daga kaina suka shiga dawo mun, voice ɗin ƙarshe dana saurara wanda ba zan iya maimaita kalmomin da suke ciki na suka shiga dawomun sai na saka hannu biyu na toshe kunnuwana ina jujjuya kaina da nake jin tamkar zai tarwatse saboda azabar ciwon da yakeyi mun daidai lokacin kuma ya shigo ɗakin ya tsaya daga bakin ƙofa yana kallona kafin ya ce

"Lafiyarki kuwa Halima?"
Ban amsa ba illah cusa kaina da nayi tsakanin cinyoyina dan bana son ganin sa, ina jinsa ya nufoni yana sake nanata
"Mai ya faru? Wani gurin ne yake miki ciwo ko kanki ne?" Ya faɗa yana tsugunnawa a gabana. Daƙyar na ɗaga kai na kalle shi na ce
"Ka tashi ka fita kai ka dame ni kaine bana son gani ko sauraron muryarka a kusa da ni".
Chapter 80 · 0% Book details