← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 158

Sashe 93

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Saboda dama ni nace ka koreta ko ya akayi da zaka sakani a bakin duniya?" Ta katse shi, sai ya marairaice ya ce
"Yanzu dai kiyi haƙuri Hajja ta dawo, ni da nake tunanin ma in ƙara wata kafin wata biyun ta cika sai in kulle ƙofa da Jalilah yar gaban goshin ki". Kallon baka da hankali tayi masa kafin tace

"Saboda ka zama namamajo ko baka da wani lissafi a rayuwarka sai na aure? To ban yarda ba kuma bada yawuna ba Halima dai ko da kaca aka ɗaura aurenku sai ka datse ka sallameta can Allah ya haɗa kowa da rabon sa abinda akayi a baya ma ya isa Allah ya sa albarka".

"To yanzu idan na saketa zaki barni in auri wata kenan?" Ya faɗa cikin ɗar ɗar, ta balla masa harara kafin ta miƙe ta shige ɗaki ta barshi a zaune. Jiki babu laka ya fita daga gidan suka ci karo da Abubakar dakw shirin shigowa, kallo ɗaya Abubakar ɗin ya masa tamkar bai ganshi ba ya wuce ciki sai Bilal ɗin ne ya dakatar dashi yana cewa

"Kai baka ganni bane? Yaushe kuka fito daga camp ɗin?" (Aikin custom ya samu sunje training). Cikin ko in kula yace masa
"Na ganka mana, jiya na dawo" ya shige gida. Sai ya bishi da kallon mamaki domin ko da wasa magana mai shige da raini bata taɓa haɗa shi da ƙanin nasa ba balle ya masa irin haka, to menene dalili?

A jikin motar sa ya tsaya duk ya rasa ina ya kamata ya dosa, ya kamata ya leƙa office ɗin su dan an tura masa da query akan rashin zuwansa aiki dukda ya ɗauki leave amma hutun ya ƙare tuni kuma bai koma ba haka nan bai tura saƙo abinda ya sa bai wani damu yanzu da aikin ba saboda harkokin da ya kama yana ganin in ya cigaba sun isa su riƙe shi dama jira kawai yake shagon da Jalilah take shirin buɗewa a nan Kano ya tabbata zai yi resigning saboda harkar fita waje da zai ringayi na shigo musu da kaya.

Wayar sa ce tayi ƙara ya zarota daga Aljihu, sai da gabansa ya faɗi ganin Hafiz ne yake kira a ƙalla kusan sati uku kenan rabon da suyi waya balle su haɗu. Kamar kar ya amsa sai kuma dai ya ɗaga. Daga can Hafiz ya ce

"Ranka ya daɗe yau na ci sa'a waya ta shiga an amsa kenan?"
"Tuba nakeyi yallaɓai wlh tafiya ce ta sameni ba shiri mun tafi da Hajja can yakin Nijar gurin wani mai magani jiya muka dawo dama yanzu ka ganni nake shirin fitowa zan kiraka naji gida zanzo ko office sai kuma ga kiranka" ya shato ƙaryar da shi kansa sai da ya jinjinawa kansa. Cike da Jimami Hafiz ɗin ya ce

"Jikin ne har yanzu kuma? Amma me ya sa maimakon a mayar da ita Asibiti zaku tafi kuma gurin wani mai maganin gargajiya?"
"Ai ka santa ko kwanciyar da tayi a Asibitin da yaya? Ai dan an fi ƙarfinta ne ita dai tafi ganewa masu maganin gargajiya shiyasa ma na bita ɗin gudun kar a samu wata matsala kuma Alhamdulillah gashi jiki yayi kyau ta warware harma ta aje sanda yanzu tana taka ƙafar lafiya lau" ya sake rattabo wata ƙaryar har zufa ce ta tsattsafo masa yana yi kuma yana zare ido haɗi da duban gefensa ko da wani a kusa yana sauraronsa.

Hafiz ya ce
"Toh masha Allah Allah ya ƙara lafiya ya tsare gaba in sha Allahu zan shigo sai na dubata, ashe shi yasa Madam ta koma gida ni duk Suhaila ta tayar mun da hankali wai taje ta ganta a wani irin yanayi jiya kai kuma gashi ina ta kiran layinka bana samu". Da sauri ya ce

"Taje gurin Halima? Me tace mata toh?"
"Babu abinda ta gaya mata ko akwai wata damuwa ne naji yanayinka ya canza?" Cewar Hafiz, sai yayi saurin daidaita nutsuwarsa ya ce
"Babu komai naji kace ta ganta cikin wani hali ne ni kuma bata ce mun bata da lafiya ba amma bari yanzu in je gidan in ganta kawai hankalina zai fi kwanciya" kafin Hafiz ya sake magana ya katse wayar. Mota ya shiga ya kunna haɗi da kunna Ac dan zafi yakeji kamar wanda yayi gudu dukda garin akwai iska sosai tana kaɗawa.

Yanzu da gaske Halima bata gayawa Suhaila komai ba ko kuwa dai kawai rufe masa yayi yake so ya bigi cikinsa? Wayarsa tayi ƙara alamar shigowar saƙo ya duba Hafiz ɗin ne ya turo masa saƙo yana cewa
"Ka samu ka shigo office dan za'a iya samun matsala gaskiya" ganin saƙon ya saka ya tayar da mota ya kama hanyar office ɗin a ransa kuma yana ayyana daga can gidan su Halima zai biya. Sau biyu Zulaiha ta kirashi yana hanya amma bai amsa ba dan yana ganin sunanta maimakon yaji farin ciki irin yanda ya saba sai kawai tunanin jiya ya faɗo masa daga ƙarshe ya kife wayar bayan ya sakata a silent ya cigaba da kokawa da tunanin da ke neman ɓata masa yanayi.

HALIMA

Ina kwance rigingine akan gado ina amsa wayar Hansa'u, na gyara kwanciyata ina sauraronta tana cewa

"Kusan sati huɗu fa kenan ace babu waya babu zuwa balle aike kuma wani nasa bai biyo sahu ba iya wannan ai ya isa ya shaida miki amsarsa akanki Halima". Ajiyar numfashi nayi kafin nace

"Da wahala idan yan uwansa sun san abinda ya faru tunda dama ba wai zuwar mun sukeyi yanzu ba balle su san bana gidan, shi kuma nake ganin harda kunya ta hana ya zo"

"Ashe har yanzu akwai sauran uzurin da zaki masa Halima? Gaskiya da sauranki, duk abinda ya faru ace kin cigaba da kare shi to gaskiya ban kuma ga wani abu da zai buɗe miki ido ki kalli gaskiya a yanda take ba kuma ɓata yawun baki na kawai nakeyi da lokaci na ina miki magana shiga suke ta kunnen dama su fice ta hagu" Hansa'u ta faɗa cikin ƙunar rai, nayi murmushi na ce

"Haba y zakice haka? Ai wlh duk wata shawara da kike bani na ɗauka kuma ina ganin amfaninsu, kawai na faɗa miki nawa tunanin ne na wai lallai hakan bane ba".

"Dole kuwa ki canza tunani ko in ce ki bawa ƙwaƙwalwarki da zuciyarki dama su ringa tunanin daya dace ba wai iya abinda kike so suyi tunani a kai ba. Wlh Halima muddin baki yiwa kanki faɗa ba zaki kashe rayuwarki a banza ki ƙare a inda ba'a san mutunchinki ba. Yanzu ke ko dagaske kunyar yake ji idan yana sonki kuma yana darajaki da son cigaba da zama dake zai ɗauki tsayin lokacin nan ba tareda yabi ta kanki ba? Ki cigaba da mafarki kina yaudarar kanki, ko ki yarda ko karki yarda Halima Bilal baya sonki, idan ma a baya ya soki to yanzu bakya gabansa. Ya daɗe yana miki kora da hali wanda idan kina da tunani ya kamata ace tuntuni kin fahimci haka kin nemawa kanki mafita amma kin tsaya kina yaudarar kanki ke gaki uwar yan uzuri toh sai ki cigaba Allah ya bada sa'a". Bata bani damar sake cewa komai ba ta datse kiran.

Na tashi zaune ina sauke numfashi, ban san me yasa ba kowa ya kasa fahimtata. Waya ta ce tayi ƙara, na ɗauka Hansa'u ce dukda na san ko zata huce ba nan kusa ba sai dai sunan da na gani yana yawo akan screen ɗin ya saka gabana yankewa ya faɗi. Harta katse ina kallon screen ɗin wani kiran ya sake shigowa, bana so, hannuna kansa ya so yaƙi bani haɗin kai amma bisa tirsasawar zuciyata na amsa kiran. Ban ce komai ba na kara wayar a kunne na, daga can ɓangaren ina jin yanda ya sauke ajiyar zuciyar da na jita har cikin magudanar jinin jikina kafin cikin murya mai taushi haɗi da rauni ya furta

"Halims ashe zaki iya dogon fushi haka dani?". Kamata yayi ace naji haushin furucin sa domin ƙarara abinda yake nufi duk tsayin lokacin ni yake jira na kira shi Kenan shiyasa bai nemeni ba amma shirun na cigaba da yi ina saurarensa ya sake cewa

"Nayi kewarki adadin da baki ba zai iya furtawa ba dan Allah Halims ko mai zai sakw faruwa tsakaninmu a gaba ki hukuntani ta kowacce siga amma kada ki sake bari na, zan jure komai amma ba zan sakw iya jure rashin ji da ganinki a duniya ta ba wlh na azabtu wahalar da na sha a tsakanin lokacin nan kawai sai dai nayi fatan ta zame mun kankarar zunubi amma Halims kin sakani a wani yanayi da bana fatan na sake shiga irin sa".

Jin da nayi kamar wacce aka ɗauraqa fuka fukai ina shirin fara shawagi a sararin samaniya na sakw hawa gajimaren yaudarsa wanda sai nayi nisa ƙila ya sake girgijeni na faɗo na karye a in da ba zan ɗoru ba, tattaro duk wata jarumta haɗi da ƙarfin hali na nayi na ja masa tsaki mai ƙarfi kafin na zare wayar daga kunne na na kashe. Yanda kasan wacce ta sha tseren gudu haka na dafe ƙirji da hannu biyu ina sauke numfashi, na bi wayar da kallon jin kira ya sake shigowa har ya katse ya sake kira kafin ya dakata sai kuma ga saƙo sai a lokacin na ɗauke ta na buɗe na karanta.

"Na san kin huce, ina waje ki fito mu koma duniyarmu" abinda ya rubuta a ciki kenan. Kashe wayar nayi gaba ɗaya na kwanta lokaci ɗaya hawaye suka ɓalle mun. Ashe kallon wacce ta haukace a soyayya kawai Bilal yake mun yana ganin na manta ƙima da martabata a matsayina na mace shi yasa har yake tunanin bayan irin abinda ya faru tsakaninmu baya buƙatar wanke kansa ko rarrashina kai tsaye zan manta komai na sake komawa gareshi, lallai kuwa da na cika sakarya.
Chapter 93 · 0% Book details