Sashe 86
Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Tare sukaje da Bilal ɗin suka amso saƙon wannan kuma shine haɗuwar su ta farko dukda gaisawa kawai sukayi sama sama suka wuce. Ba'a fi wata ɗaya ba bayan nan ta sake zuwa Kano bikin wata ƙawar ta nan ma ta kira Hafiz akan yayi mata booking hotel bayan ta sauka kuma ta sake kiransa akan ta fasa can gidan bikin zata sauka dan Allah ya zo ya kaita yace ba zaije ba, data ringa masa magiya kawai yace mata toh ya kashe wayar. Bilal da duk yaji yanda sukayi ya shiga bashi baki akan bai kamata ya ringa wulaƙanta ta haka ba duk wanda ya ga yanda take kallonsa yasan tana son sa dan haka ko baya jinta a ransa ya ringa nuna kulawa tunda dai abu ne na lokaci ba wai kullum ne take zuwa inda yake ba, daga ƙarshe da Hafiz ɗin yace shi fa ba zaije ba shine yace shi ya bashi mota yaje ya kaita toh, haka kuwa akayi ya bashi mota da number yaje ya ɗauke ta. Kwana ukun da tayi a Kanon shi ya ringa jigila da ita yawon biki har suka gama ta tafi har sannan kuma babu wata shaƙuwa a tsakanin su kwatsam bayan nan suka sake haɗuwa a Abuja lokacin da yaje wani workshop.
A reception ɗin hotel ɗin da aka sauke su ya ganta, sai da yayi mata dogon bayani ma kafin ta gane shi sai kuma suka shiga hira har tayi masa godiyar hidimar da yayi da ita a Kano da zata wuce ta karɓi number sa shikenan da dare kawai ta kirashi tace ko zasu fita yaga gari kar yayi ta zama a hotel tunda yace mata bai san ko ina ba sai gidan su Hafiz da gidan Babban Yayansu shi kuma a lokacin ma suna Kano sunje hutu. Ranar ta fita dashi suka sha yawo tayo masa shopping kayan sakawa har da waya Iphone dan lokacin keypad ce a hannunsa bayan an ƙwace masa waya da babur. Sai da ta jera kwana uku tana fita dashi kullum kuma haka zata yo masa siyayya kamar bata san ciwon kuɗi ba a kwana na ukun kuma ya gama abinda ya kaishi amma tace masa ya zauna ya sake hutawa mana tunda dai ba wani abu zaiyi idan ya dawo Kanon ba kuma yace matarsa ma tana gida taje wanka.
A lokacin ta fito fili ta faɗa masa ita fa tunda bata samu Hafiz ba zatayi madadi dashi domin duk abinda take so a gurin Hafiz yana dashi har ma yafi Hafiz iya kalaman soyayya, da aure tazo masa dan da ace ya amince tun a lokacin da ƙila kafin Halima ta dawo daga wanka zai auri Jalila amma sai yaƙi ya kawo mata uzurin bai jima dayin aure ba yasan ba lallai mahaifiyar sa ta yarda ba da sauran uzuri dai amma ta bashi wata shida zuwa shekara ɗaya zuwa lokacin ya sun shekara uku da aure ya san babu wanda zaiyi wani surutu dan yace zai ƙara wata matar. Ta yarda da hakan, musamman da itama ya yarda da nata Sharaɗin na yi mata duk abinda take so duk ya ce ba zai taɓa kusantarta ba har sai an ɗaura musu aure amma kuma duk ɗaya domin shigarta ne kawai bayayi bayaga wannan babu kalar abinda baya mata, haka suka dilmiya cikin ƙazamar rayuwar da suka zaɓawa kansu, ta sakar masa bakin aljihu tana jiƙa shi da kuɗaɗe wanda koda wani lokacin yaji rashin dacewar abinda sukeyi ya fara janye mata tunda ta fahimci shi ɗin masoyin kuɗi ne alert ɗaya zata masa ta girgizashi ba ma sai tace ya taho ba zai kama hanyar Abuja yaje gurinta ko kuma ita tazo Kano dan har gida ta siya da sunan sa akan idan sunyi aure zata zauna a ciki dan haka idan tazo can take sauka baki alaikum ba sai sunje hotel ba.
Haka suka cigaba da tafiya a sirrance dan daga shi har itan babu wanda yake so Hafiz yasan abinda yake tsakaninsu musamman Bilal dan hatta yan uwansa da duk sanda tazo Kano sai tayi nacin ya kaita su gaisa amma saidai yayi ta bata uzurin yau gobe a haka har ta gama kwanakinta ta wuce. Shammatar sa tayi ta kai kanta gurin Hajja ta kuwa yi mata shatara ta arziƙi ta gabatar mata da kanta a matsayin budurwarsa shikenan Hajjan ta gigice ta ringa faɗin ga arziƙin gaske ya tarar dasu har gida amma da yaje ya kwaso musu yar masu kuɗin cizo dan abinda Jalilan ta kai mata a zuwa ɗaya ya fi duk hidimar da Halima ta mata tun daga neman aurenta har zuwa yanzu.
Shikenan ta samu nayi kullum zancen ta yaushe zai tura ayi maganar aurensu ai yanzu ne zai yi mata yarinyar jinin larabawa wanke hannu ka taɓa ga tarin arziƙi kuma hannunta a buɗe dan ba'a rufa wata ba tareda tayowa Hajjan aike ba ta hannun sa wani sa'in kuma ta tasha zata turo musamman idan kayan amfani ne haka kwana bibbiyu zata kirata a waya su gaisa kati kuwa da data duk zalamar Fadila sai dai ta gaji ta ajewa Hajja wayar ta dan basa taɓa yankewa ita Jalilan ce ma ta saka aka buɗewa Hajja Whatsapp a sabuwar wayar data siya mata wai ai batayi tsufan da za'a ce ba zata riƙe babbar waya ba.
Haka nan suke, yana jin daɗin mu'amalar sa da Jalila domin kuwa ta sake masa kuɗi yanda ya kamata ba sai ya tambayeta ba yana zaune kawai zaiga alert kuma bata taɓa tura masa kuɗi kaɗan haka kyaututtuka kusan tun da suka fara mu'amala zai ce bai sakw siyan sutura ko wani takalmi ko agogo ko turare ba ita take siya masa kuma masu asalin tsada da kyau, bayan gidan da ta siya da sunan sa a yanzu haka ya mallaki filaye biyu Manya da gona itama babba y siya babu daɗewa saboda yana so ya fara noma.
Hatta wannan motar ita ta bashi kuɗi miliyan shida cis tace ya siyi mota, da farko cewa tayi ya zaɓi wacce yake so zata siya masa sai kuma yayi tunanin rana tsaka a ganshi da mota zai zama abin surutu wannan ya saka yace kawai ta bashi kuɗin ta kuma bashi sai ya raba biyu da niyyar ya siyi kamar ta 3m haka amma da yayiwa Hafiz magana shine ya cika masa yace ya ɗauki wannan ɗin a gurin siyar da motocinsu. A hakan ma ya sha surutu koma yace yana kan sha dan yanda yake dai da aikinsa kowa ya san an ɗan lokacin nan bai kai ya tara kuɗin siyan mota haka ba amma duk wanda ya cewa ubangidan sa ne ya bashi shikenan tunda da yawan abokanan sa sun san Hafiz ɗin sun kuma san yana da sararin da zai bashi fiye da ita ma shiyasa yayi dabarar jona shi cikin zancen motar tun farko.
Matsalar daya fara fuskanta da Jalilan yanzu, a farkon tarayyarsu bata damu da Halima ba, ta gaya masa ita ko mata uku yake dasu bata da matsala zata shiga a ta huɗu amma kuma da tafiya ta fara nisa sai zance ya canza ta fara nuna masa ita fa ba zata iya haɗa shi da wata ba dan haka idan lokacin auren su yazo sai dai fa ya zaɓa ko ita ko Halima wanda wannan abunda ta ɓullo dashi yana daga dalilin daya saka neman nasu yin tsaho domin yace ba zai iya sakin Halima hakanan ba dan babu wani laifi da zai iya danganta cewa tayi masa da zai saketa akan hakan amma ta bashi lokaci zai ɓullo da hanyoyin da ita da kanta zata gaji ta nemi rabuwa dashi.
Sai dai fa a zuciyar sa kwata kwata ba son Jalila yakeyi ba kwaɗayin abun hannunta yakeyi. Dama a wannan tsukin yake tunanin samo hanyar rabuwa da ita cikin sauƙi domin har ransa bashi da burin aurenta, a lamarin aure yana buƙatar macen mai tarbiyya wacce zai faɗawa magana taji irin Halima ba wacce zata zama ita ce mijin shi kuma matar ba balle kuma ita da ya rigada ya san halinta kuma sun gama tambaɗewa ai babu zancen mutunchi ko zaman lafiya ma a tsakanin su idan su kayi aure.
Yana da burin ƙara aure nan kusa kuma ZULAIHA yake so ita ce zaɓin sa tun asali kuma ita zai aura kuma ko a yanzun rabin abinda yake samu daga gurin Jalila ita yakeyi wahaltawa yake kuma yi mata tanadin bayan auren su gashi yanzu garajen Halima na nema ya rusa masa lissafin daya shiryo.
Wayarsa dake ajiye gefe ta ɗauki ƙara abinda ya maido shi daga duniyar tunanin daya lula. Sunan DUNIYATA dake yawo akan screen ya saka shi sauke ajiyar zuciya kafin ya ɗauki wayar ya amsa haɗi da sakata a speaker. Daga can tayi sallama cikin muryarta me sanyi da sautin shagwaɓa, amsa sai taci gaba da cewa
"Habibi lafiya kake kuwa yau kwana uku ina kiran wayarka sai dai tayi ta ƙara amma baka amsawa kuma baka biyo baya ba?" Ta ƙarasa kamar zatayi kuka. Ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi kafin ya ce
"Banida lafiya ne".
"Subhanallah, mai ya sameka?" Ta tambaya a ɗan rikice, sai ya sake yin ƙasa da murya kamar mara lafiyar gaske yace
"Zazzaɓi nakeyi da mura"
"Wayyo Allah ya baka lafiya Habibi ni dama na san sai dai ba lafiya ba shine kaɗai abinda zai saka ka kasa amsa kirana, to yanzu ya jikin naka? Amma dai da sauƙi ko kasha magani?" Ya amsa mata da
"Eh da sauƙi kuma nasha kada ki tayarda hankalinki dama yanzu nake so idan nayi wanka na kiraki nasan zaki damu kwana biyu baki jini ba".
"Wallahi ko na damu sosai tun waccen ranar da Umma tace mun kaje tareda Maman Al'amin na kira kace kana driving zaka kirani shikenan fa da na sake kira da daddare ka amsa bakayi magana ba har naji tsoro ko zuwan da kukayi da ita ya haifar da wata matsala ne yasa kake avoiding ɗina" tayi maganar kamar zatayi kuka, sai ya saki murmushi yace
"Wace matsala zuwan Halima zai haifar? Kin san dai yanda nake sonki ko duniya zata taru babu wanda ya isa ya shiga tsakanina dake ko?"