← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 158

Sashe 138

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A reception na tarar da duka staffs harda cleaners anyi layi na tafi inda naga sa'annina da alama tsayuwar matsayi aka bi, yanda kasan waɗanda zasu tari wani Gwamna ko Shugaban ƙasa haka muka nutsu muna kallon ƙofa kusan minti uku kafin suka shigo, Dr Sa'id ne a gaba sai wasu mutum biyu da ban sansu ba da alama tare suka zo da CEO ɗin sai kuma shi Dr SALMAN ABDULLAHI AGI da wasu mutum biyun a bayan sa, ɗaya daga gani PA ɗin sa ne sai kuma ɗayan da yayi kama da security.

Fuska ba yabo ba fallasa ya ringa kallonmu suna tayi masa sannu da zuwa banda ni dana zuba masa ido ina ƙare masa kallo kamar mai neman wani abu a jikinsa. Duk yawan shekarunsa ba zasu kai 40 ba yanzun ne na sake tabbatar da haka dana ganshi a zahiri. Dogo ne sosai dan har ranƙwafawa yayi, a kallo ɗaya kuma dukda suit ce a jikinsa zaka fahimci yana da kirar ƙarfi irinta masu ɗaga ƙarfe.

Bashi da wani shahararren kyau kuma baƙi ne mai ƙananan ido amma akwai wani abu a tattare da idanuwansa da bai zai barka kayi masa kallo ɗaya ba tareda ka ƙara ba, gayu da iya ɗaukar wanka ya saka ya ƙaƙalo kyawun a dole amma ba dan asalinsa mai kyau ɗin bane irin su Bilal da aka haife su da kyan su, amma maganar gaskiya a ture duk wani ƙaƙale-ƙaƙale, Dr Salman ya haɗu; ga kuma tarin ilimi abin ba'a cewa komai.

Yanda nake kallonsa shima haka ya tsayar da idonsa a kaina sanda ya kallo ɓangarenmu, naga sanda laɓɓansa suka motsa alamar magana yayi amma kunnuwana basu jiye mun sautin mai ya faɗa ba ganin kuma mun haɗa ido ya saka nayi saurin sadda kaina ƙasa ina jin haushin irin kallon ƙurillar daya kamani ina yi masa. Juwairiyya ta zungureni na kalleta da son jin ƙarin bayani, da ido ta nuna mun CEO ɗin da har sannan ashe ni yake kallo na zare masa ido cikin rashin fahimtar dalilin kallon da yake yi mun.

"Tambaya yayi wai baƙuwa akayi?" Juwairiyya ta raɗa mun a kunne, still ban fahimci kan zancen ba sai da Dr Sulaiman ya ce
"Sallah tayi garin sauri kuma ta manta ta fito a haka". Sai lokacin na lura ashe ni kaɗai ce a gurin babu lab coat a jikina cikin yan Lab, nayi ƙasa da kai ina kallon takalman ƙafarsa kafin na ɗaga kai a hankali jin yana cewa kowa ya gabatar da kansa. Sai kace za'a gudu ba zai bari aje a zauna ba tukunna. Da ɗai-ɗaki kowa ya ringa gabatar da kansa da kuma position ɗin sa har aka zo kan coppers mune kuma ƙarshe, Juwairiyya dake kusa da ni tayi tana gamawa na buɗe baki zan fara magana wayarsa tayi ƙara sai ya ɗaga mun hannu alamar na dakata ya karɓi wayar daga hannun PA ya amsa kafin ya fara tafiya suka shige Elevator shida muƙarrabansa suka barmu a tsaye musammani, ni ce fa kaɗai na rage banyi introducing kaina ba maimakon ya bari nayi sai su wuce gaba ɗaya yanzu ko mai yake nufi sai Allah, zamu tsaya ne yaje ya dawo ko kuwa shikenan taron ya watse? Wai dama iya dalilin daya saka aka tsayar damu kenan ko da saura?

Dr Sa'id ne ya dawo ya ce zamu iya tafiya wai amma gobe kowa ƙarfe takwas tayi masa a gurin za'ayi meeting. Haka muka fita ina mita ga rana ta take babu lallai kuma na tarar da masu clearance ɗin suma tunda ƙarfe biyu ta rigada tayi amma haka nan na biya tunda idan na ce na bari gobe Friday kuma ban san sai ƙarfe nawa zai sake mu ba. Da haushin rashin samun clearance ɗin na wuce gida dan munyi waya da Anty Labiba tace mun suna gidan Mama.

Ban san ɗaya matar da muka hau Adaidaita tare cikin unguwa za'a shigar da ita ba tunda tace Sabon titi kawai na ɗauka a bakin hanya zata sauka ni kuma ya wuce dani sai da muka je naga yana ƙoƙarin shiga layin Gidan Ƙanƙara layin su Bilal kafin nayi masa magana.
"Ba ciki sosai bane Hajiya kuma kan hanya ne inda zata sauka sai mu fita ta baya Hajiya" mai Adaidaitan ya bani amsa. Ƙoƙarin mayar da kaina kan wayata da nake dannawa nayi amma na kasa sai na zurata cikin jaka na shiga kallon hanya ina tuna zuwana gurin na ƙarshe ranar da muka zo duba Hajja bayan mun dawo daga gidansu Duniyarsa.

A kan layinsu Bilal ya tsaya, na leƙa ina hango ƙofar gidansu daya sha sabon fenti ga mata suna ta shige da fice kamar ana wata hidima a gidan,
"Ko mai akeyi sai Allah" na faɗa a fili kafin na ɗauke kai na koma kallon mai Adaidaitan dake irgawa matar data sauka canji.

"Gadon ƙaya" muryarsa ta sauka a kunnena tamkar dirar aradu kafin ƙamshin turarensa da tunda na sanshi bai taɓa canzashi ba ya mamaye iskar da take yawo yawo a gurin, na ɗago; har ya zauna a gefena. Dukda na razana da ganinsa amma ban bayyanar da hakan a kan fuskata ba sai na mayar da hankali na kan mai Adaidaitan na ce
"Malam drop fa na ɗauke ka, itama saboda naga hanya ɗaya zamuyi kuma abin hawan yana wahala shiyasa na bari ka ɗauketa"

"Kiyi haƙuri Hajiya, Malam yi haƙuri ka sauka ba can zamuyi ba" mai Adaidaitan ya faɗa, sai lokacin Bilal ya kalleni idan kuma nayi rantsuwa na san ba zanyi kaffara ba tsabar wulaƙanci ne ƙarya yakeyi ya ce bai san ni bace a ciki sai a lokacin.

"Halima" ya faɗa muryarsa da idanuwansa suna bayyanar da mamaki, na ɗauke kai a raina ina cewa
"Ƙaryar banza wlh ka san ni ce" kafin kuma na saita fuskata na kalle shi da irin yanayinsa na ce
"Au Bilal, kai ne?"

"Kun san juna ma ashe? Toh mu ɗauke shi ko zai sauka?" Mai Adaidaita dake kallonmu ta cikin mudubi ya faɗa, shiru nayi dan har ga Allah ƙarfin hali kawai nakeyi sai Bilal ɗin ne ya ce masa
"Bari sai na sauka a titi tunda ciki zaku shiga" ya tayar da mashin ya juya sai lokacin na ƙaƙalo murmushi ganin yana kallona na ce

"Ya su Hajja?"
"Amma baki faɗa mun zaki ringa fita wani guri ba, ko kin manta har yanzu ina da iko akanki tunda kina cikin iddatah?" Ya faɗa yana kallona cikin sauti mai kama da raɗa dan nima ba dan shi nake kallo ba bai zama lallai na ji abinda ya faɗa ɗin ba. Na saki murmushin irin na tura takaici wanda ni kaina ban san na iya ba kafin nima na sauke murya yanda yayi na ce

"Da alama amarci ya sa ka faa manta lissafi, ko dai in saka ayi maka babbar calendar da zaka ringa duba watanni da ranaku saboda gudun manta abubuwa masu muhimmanci irin haka?"

"I'm serious Halima, 28th of this month ya kamata ki fara cycle ɗin ki na uku" ya sake faɗa, ganin mum kawo kan titi mai Adaidaitan na neman cigaba da tafiya ya saka nace masa

"Ya sauka a nan" sai ya dakata, na kalli Bilal da shima ni yake kallo kafin na ce
"An zo titi Malam", kallona yakeyi kamar wanda yaga wata halitta ta daban dan haka na kaɗa yatsuna akan fuskarsa ina sake maimaita masa cewar an zo titi,

"Ki fara shiri, na mayar dake ɗakin ki" ya faɗa yana sauka daga Adaidaitan, bansan lokacin dana fashe da dariyar da har mai siyar da ƙanƙara a inda kuka tsaya da mutanen dake gurin saida suka kallemu ba, da hannu na nuna kaina ina cewa

"Da alama kayi hauka ko?"
Ya miƙawa mai Adaidaitan gudar dubu ɗaya yana cewa
"Za'a ga wanda yake hauka tsakanin ni da ke" ya wuce ya tsayar da wani Adaidaitan ba tareda ya tsaya karɓar canjinsa ba, abun nasa yayi bala'in bani dariya; lallai bansan Bilal mahaukaci bane sai yanzu. Wato shi yana can yana mun lissafin Iddah kenan? To da bai haɗu dani ba yanzu wa zai aikowa da saƙon ya mayar dani ɗin?

Ni kaɗai na ringa dariya mai Adaidaita dai sai satar kallona yakeyi da alama magana ce fal bakinsa amma ya kasa furtawa har ya saukeni ƙofar gida nayi wucewara tunda Bilal ya biya mun, lallai yau kam za'ayi ruwan sama harda ƙanƙara Bilal ya biya mun kuɗin mota.
[5/28, 11:06 PM] Hauwa Galadima: ❤️ *ƊANLARABAWA INVESTMENT! Kyau Da Ƙima A Hannunku!* ❤️

*Ku sauka lafiya zuwa masarautar ƙayatarwa!* 👑

*ƊANLARABAWA INVESTMENT* na kawo muku:

*Atamfofi masu kyau na zamani*
*Shaddodi da Laces masu ɗaukar ido*
*Takalma & Jakunkuna masu ladabi da ƙima*
*Hijabai, mayafai da dogwayen riguna masu salon zamani*
*Yari da sarƙa da kayan ado masu ban sha’awa*
*Akwatuna masu kyau don tafiya ko haɗa lefe*
*Turaruka masu ƙamshi da kayan kwalliya na garari*
*Nau'in kayan kicin na alfarma da kayan ɗaki*
*Zannuwan gado da labulaye na kashe kala*

*Da dai sauran su*

*Muna tura kayanmu ko'ina a fadin Nijeriya da ƙasashen ƙetare. Cikin mutuntaka da cika alƙawari in sha Allah*

*Location: Kano, Ƙofar Waika, Layin Malam Sani Shawus.*
*Lambar waya domin tuntuɓa*: 08080049548

*Ko ku shiga zaurenmu na manhajar WatsApp ta wannan link kamar haka:*

https://chat.whatsapp.com/Loht5sGuLJO3LXYE9OkqNs

*Za ku more da kallon kayayyaki na ƙawa bisa ingantaccen farashi da rahusa mai kama da kyauta. Sayen nagari, mayar da kuɗi gida.*

*KURA A RUMBU*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 57*
Chapter 138 · 0% Book details