← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 133 OF 158

Sashe 133

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tarin missed calls ɗin da ya gani daga Alhaji Lawan mutumin daya siya gidan Jalilah a hannunsa ya tabbatar masa da ba lafiya ba, a maimakon ya kira Alhaji Lawan ɗin kai tsaye sai ya fara kiran Nasir domin shi yayi hanyar cinikin.

"Yanzu nake shirin kiranka dama; kana ina?" Nasir ya faɗa bayan daya amsa wayar Bilal ya ce

"Mai ya faru naga mutumin nan daya siya gida a hannuna yana ta kirana a waya ban lura ba sai yanzu?"

"Shiyasa na ce kana ina? Akwai matsala gaskiya" Nasir ya bashi amsa. Bilal ya girgiza kai kamar yana gaban Nasir ɗin kafin ya ce

"Ina Abuja, ka faɗa mun abinda ya faru dalilin daya saka na fara kiranka kenan kafin na bi bayan nasa kiran"

"Wasu mutane ne suka je gidan, a faɗar su sun siyi gidan ne dan har takardu suka nuna masa kuma daya ɗakko musu nasa aka haɗa sai ya gane na gurin sa fake ne su suke da original ɗin" Nasir ya faɗa.

Wata hajijiya da bugawar ƙirji suka ziyarci Bilal lokaci ɗaya, a hankali ya sulale ya zauna akan gado zufa ta shiga keto masa kamar wanda yayi gudu. Yana jiyo Nasir ta cikin wayar yana cewa

"Idan kuskure ne tun wuri ka nemo hanyar da zaka gyara dan wlh Alhaji Lawan bashida daɗi musamman akan maganar kuɗi; yanda ya kirani kuma yanzu na san a shirye yake da yin koma menene dan haka asirinka a rufe ko dai ka mayar masa da kuɗinsa ko kuma su waɗanda ka siyarwa yanzun su haƙura ka basu kuɗinsu tun kafin magana tayi nisa".

Kusan minti biyar yana zaune ya rasa tunanin da zai kama, Su waye suka siyi gidan? Kuma wanene ma ya siyar musu? Yanzu da Nasir yake cewa ya mayarwa da Alhaji Lawan kuɗinsa ina ya gansu? shi da dubu ɗari ma yanzu sai dai a ɗaure shi dan bashida ita. Watansa biyu rabon daya samu albashi, da yaje yayi ƙorafi sai lokacin ma ya san wai ashe an sake bashi query toh bai ma sani ba balle yaje yayi depending kansa daga amsar da account ɗin kuma ya bashi wai yaje yayi ta addu'a ya san abu ne mai wahala idan bai rasa aikinsa ba.

Abun mamaki kuma, a cikin shirinsa harda barin aikin da zarar abubuwan da yake shiryawa sun tabbata amma kuma sai yaji hankalinsa ya tashi sosai yanzun ko da yake dole, duk abubuwan da yake lissafawar sun ruguje, da kuɗin shagunan Jalilah ya so yayi jari zai fara harkar Import and Export ya gama saita komai amma kuɗi sun ƙi samuwa kamar asiri an rasa mai siyan shagunan duk wanda aka samu sai an fara magana kamar gaske sai wasa ya shigo ciki gashi duk kuɗaɗen da suke account ɗin sa ya kashe su akan auren Zulaiha ɗan canjin daya rage masa ya san ko cikakken cefanen wata ɗaya ba zai musu ba ga wata ya taho gangara itama Hajja zai yi mata nata cefanen ya kuma bata kuɗin da yake bata duk wata.

Wayar daya kashe bayan sun gama magana da Nasir ɗin ya ɗauka da niyyar kunnawa ya kira Jalilah domin dai daga shi sai ita ne a cikin maganar gidan dukda bashida tabbacin samunta a wayar; yau kusan sati biyu kenan rabon da suyi magana tunda ta kirashi ranar tace masa kayan da ta turo sun sauka suna Lagos zata tura masa number wanda zai kira sannan zata tura masa kuɗin da za'ayi clearance shikenan yaji shiru, ya gama shirya da zarar ta tura kuɗin ya dafe su zai sake danna mata block suyi rabuwar ƙarshe sai gashi kwana da kwanaki shiru kuma idan ya kira wayarta a kashe haka ko a Whatsapp baya ganinta.

Ya ɗan shiga damuwa da tunanin ko wani abu ne ya sameta dan har Hafiz ya tambaya ya ce masa tana lafiya sunyi magana, hakan ya bashi mamaki har yayi niyyar ya tambayeshi yaushe sai kuma ya fasa gudun kada Hafiz ɗin y zargi wani abu.

Kunna wayar yayi zuciyarsa ta raya masa daya kira layinta na Nigeria cikin sa'a kuwa yana kira ta shiga murna kamar ya taka rawa sai dai har wayar ta ƙaraci ringing ta katse ba'a amsa ba. Sake kira yayi nan ma shiru bata ɗauka ba, sai kawai ya miƙe ya shiga saka kaya dan dama daga wanka ya fito, a ƙalla tunda ya samu wayar a kunne ai magana ta ƙare komai zai zo da sauƙi.

Yana taje sumar kansa Zulaiha ta shigo ɗakin cikin kwalliyar da idan zata fita kaɗai yake ganinta da ita.

Daga bakin ƙofar ta tsaya tana jifansa da kallon daya fi kama dana raini ta ce
"Zan fita"
"Bada yawuna ba" ya bata amsa yana zura wayarsa a aljihu, tamkar ɗan data haifa haka ta taso masa tana cewa

"Ai kuwa wlh baka isa ba fita kamar naje na dawo, haka kawai; sai kace wata dabba zaka turkeni a gida ba kulawa ba walwala ka kuma hana ƙawaye na zuwa balle na gansu naji daɗi sannan kace ba zan fita waje in shaƙata ba ai wlh kasan ƙarya kakeyi kuwa".

Kallonta ya ringayi dukda tuntuni ya dena mamakinta ya kuma fahimci dagaske wannan itace asalin Zulaiha; Ƙazamar mace, mara kunya kuma mara tarbiyya. Sanin da yayi mata a kamila, nutsattsiya kuma mai kunya duk yaudara ce kamar yanda ta yi nasarar lulluɓe halayyar tata da sunan Aljanu wanda duk sai a hankali da zama ya fara nisawa ya fahimci haka take babu wasu Aljanu ko wata iska da take shafarta kuma ba iya ita ba.

Ya gyaɗa kai tareda raɓeta ya wuce yana jin ta saki tsaki haɗi da cewa
"Ƙaryar banza" kafin ta bi bayansa, kafin ma fita da mota ya kulle gidan ita har ta kusa titi, ya na ƙoƙarin tsayawa ya ɗauke ta tare Napep ta shige abinta tamkar ma bata ganshi ba. Ya sauke numfashi mai nauyi yana shafa kansa. Yayi zaton samuwar Zulaihan zai zame masa cikar burika da kuma samun nutsuwa sai dai daga ranar data fara amsa sunan matarsa shi dai kullum komai ƙara lalace masa yakeyi.

Zulaiha ta raina shi, raini irin wanda bai taɓa zaton wani mahaluki zai yi masa a duniya ba. Da fari zama ya fara yin daɗi a tsakaninsu, yana ƙoƙari gurin ture abinda yake hanashi sukuni akanta ya tarairayeta irin yanda ya daɗe yana mata tanadi itama kuma tana ƙoƙari matuƙa gurin kyautata masa sai dai abinda ya fara haɗasu kwashe-kwashen ƙawayenta.

Ya mata magana ya fi sau shurin masaki akan mutanen da take tarawa suyi masa kaca kaca da gida kuma su tsallake su tafi su barshi a haka itama da take zaune a gidan ba zata gyara ba haka zata zauna cikin ƙazantarta tayi ta danna waya ko tayi kallo idan yayi magana ta ce dare yayi an hanata shara da daddare tunda shi kuma ba zai iya bacci da datti a in da yake ba dole komai dare haka zai gyara gidan hakan kuma ba zai hana washe gari su sake dawowa su maimaita abinda sukayi jiyan ba.

Ga Almubazzaranci, buhun shinkafa daya ajiye bai ko rufa musu wata biyu ba tace ya ƙare duk kuwa da ba wai shi kaɗai bane akwai su taliya, macaroni harda couscous, kada kayan shayi suji labari dama, idan ya siyo madara ta leda ko gwangwani yau in sha Allahu kwana uku yayi yawa sai dai ya tarar da burbuɗi a ciki balle ƙwai da idan ta tashi shida take soyawa idan bai tashi ba haka zata cinye ita kaɗai su Nama, kaza kuwa tunda ya siyo na farko bayan an kawo mata Freezer da ta ce Mijin wata Antyn ta ne ya siya musu ita da Nuratu ya yiwo cefane da yawa aka zuba, shi dai bai irga sau nawa ma ya ci abincin nata ba balle ya ci Naman ba'a rufa sati biyu ba zai fita ta ce masa ya aiko da naman da za'ayi girki, ya rufeta da faɗa bata saurara ba itama ta haye masa tana cewa

"Karka kuskura ka zageni akan nama wlh, banda tsiya da ƙaranta mai akayi akai nama da har zaka ringa tada jijiyoyin wuya akansa? Dama ba saboda na ci ka siyo ba ko kuwa ado zanyi dashi a Freezer? Toh wlh karka sake, ba kuma ka isa ka mun shamaki da wani abu a gidan mijina ba zan ci abinda nake so kuma dole ka kawo dan haƙƙina ne dole ka bani abina" ta faɗa tana wani zare masa ido kamar uwarsa.

Ya ringa kallonta cike da al'ajabi ba tareda ya shirya ba kuma ƙwaƙwalwarsa ta tafi masa tariyar lokutan baya zamanin Halima. Ya tuna lokacin da yake mata tijara akan abinda ya siya da kuɗinsa ko wanda aka kawo mata daga gidansu, dai-dai da rana ɗaya bata taɓa ɗaga kai ta kalle shi ba balle ta mayar masa da raddi idan ya gama kuma ta bashi haƙuri.

Kawar da tunanin yayi ya kalleta ya ce
"Kin fi kowa sanin ba'a bishiya nake tsinko kuɗi ba dan haka tun wuri ki shiga hankalinki ki kuma koyi tattali" daga haka ya wuce shi da kansa mamakin kansa ya kamashi. A wata biyun ta masa abubuwan daya kamata ace ya rufeta a ɗaki ya mata dukan tashi kisha gishiri amma ko magana mai zafi zuciyarsa bata taɓa yarda ya furta mata ba ko yayi niyya kawai sai yaji ba zai iya ɓata mata rai ba sai dai ya shanye komai a cikinsa shi kaɗai.

Gajiya yayi da tafiya ya samu gefen titi yayi parking, sai da ya matsar da kujera baya ya kwanta haɗi da tallafe kansa ya lula tunani. A lissafe yake komai ya rasa kuma ta inda ya kuskure abubuwa suke neman su lalace masa haka.

Wayarsa ya ciro daga Aljihu yaga sake ganin Missed call ɗin Alhaji Lawan, ya ja tsaki a fili to wai mai yake so yayi masa ne?
Yana ƙoƙarin sake kiran Jalilah kiran Alhaji Lawan ɗin ya sakw shigowa, ya kuma zabga tsaki kafin ya tashi zaune dakyau ya ɗaga wayar. A gajarce suka gaisa Alhajin ya ce
Chapter 133 · 0% Book details