← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 158

Sashe 73

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A haka na rainin cikin Sharifa cikin ƙunci da baƙin ciki domin kwata kwata Bilal canzamun yayi. Sai mu yini mu kwana bai ce mun komai. Da farko ya sakko lokacin da Mama ta ɗauki Al'amin ganin ina shan wahalar laulayi, watan sa biyu a can gidan kafin aka dawo da shi. Dawowar ta sa ma da farko farko bai wani nuna ɓacin rai ba sai bayan da siyayyar kayan ciye ciyen da aka haɗo shi da su ta ƙare ranar da na fara masa magana zai fita nace ya taho masa da ƙwai da Ceralac dan har sannan ita kaɗai yake yiwa shan ƙoshi sai kuma ƙwai haka ya rufe ido ya ringa zazzagamun masifa har yana faɗin idan da an san ba za'a iya riƙe yaron ba akan me za'a ɗauke shi aje a lalata shi da ciye ciyen banza?

Ba zai siyo ba, ai dama tun farko ni na koya masa shan cereal ɗin har kunu Hajja ta haɗo ta kawo amma naƙi bashi dan haka sai na cigaba shi baze iya ba. Ranar sai da na ji kamar na haɗa kaya na na bar masa gidan amma bazan iya ba. Ina son sa ina kuma son zama da shi. Nayi uzurin cewa cikin da na samu ba tare da shawarar sa bane ya ɓata masa rai na kuma ɗauki alƙawarin da zarar na haihu bazan fito daga labor room ba sai na yi family planning har idan hakan zai faranta masa rai.

A haka na haihu, na samu ya mace wadda ya bani zaɓin akan duk sunan da nake so in saka mata na kuma zaɓa mata SHARIFA. Sai ana gobe suna kafin ya bani dubu saba'in wai ko akwai abinda zan buƙata. Nayi murmushi kawai na karɓa. Ba abinda nake nema wanda bani da shi. A lokacin na godewa gatan da Anty Labiba ta mun na kwashe duk wani abu da muke da shi double lokacin haihuwar Al'amin ta ɓoye mun. Riguna kawai na kwalliyar mata na siya dan duk wani unisex muna da su. Ban yi taro ba, duk da yan uwan sa sun zo amma da suka ga babu kowa a gidan basu zauna ba suka tafi.

Haka na shiga rainon yara biyu sai kuma a lokacin kuma na fuskanci zaton da nake yi na zan iya ɗaukar nauyin kaina da abinda zan haifa ba tareda na damu da abinda Bilal zai yi mun ba ba mai yuwuwa bane.

Abban da yake bani kuɗin tun da na haifi Sharifa ya janye mun tallafi. Sai na yi zuwa biyar gida ba tare da ya bani ko sisi ba. Idan ma zai banin ya dena bani da yawa kamar da ƙarƙarin kyautar bata haura dubu goma ko ashirin saɓanin da da duk watan duniya sai ya tura mun dubu hamsin wanda ko Mama bata san da hakan ba kuma shi ya hana na faɗa mata. Sannan duk sanda naje gidan idan zan tafi zai bani na mota.

A sannu na fara gane ainihin abinda ake kira da yau da gobe bata bar komai ba, ga hidimar yara, ga damuwar Bilal da gaba ɗaya zaman mu ya canza salo. Duk ta inda nake zaton matsala nayi ƙoƙarin gyarawa amma tamkar ina sake rura wutar ne. Idan nayi abinci haka zai balbaleni da masifa ya ce na koyi mugunta wai yanzu sai na ringa abinci kamar wanda za'a bawa bayi ba taste babu komai. Akwai ranar da nayi tuwo da miyar kuka kamar yanda ya faɗa mun na yi kafin ya fita da ya dawo na kawo masa haka ya saka ƙafa ya ture kwanon miyar ya ringa sababi har da yi mun Allah ya isa akan ɓarnar abincin da nake masa kamar yanda ya ce. Abincin da ni da yaran sa muke ci amma shi ya ce ba daɗi baze iya ci ba, na rasa gane kan Bilal na kasa fahimtar inda ya saka gaba.

Duk yanda nake tunanin na samo bakin zaren shirin baya wuce na kwana biyu zuwa uku zai sake birkicewa. A sannu na fahimci hanya ɗaya ce take samar mun farin ciki tattare da Bilal shine samuwar kuɗi a hannu na. Idan ina da kuɗin da zan girka masa abinci mai daɗi a ci zamu ɗauki tsayin lokaci ba tare da kowa ya ji kanmu ba, daga sanda cefane ya canza na fara girka zallar abinda ya ajiye mana sai tashin hankali ya ce ina lalata masa abinci. Ma fahimci abinda yake so, ko da ba zan ɗauki kuɗi na bashi ba yana so na wahalata masa shine farashin soyayya ta a gare shi.

**********************

Daƙyar na iya buɗe ido na da suka mun nauyi dalilin kukan Al'amin da na jiyo. Na yunƙura daƙyar na tashi ina dafe kaina da yake mun ciwo matuƙa. Waya ta na janyo na duba, biyu saura kwata lallai na daɗe a kwance ashe. So nake na fita na ji dalilin kukan nasa tun kafin ya tashi Sharifah wadda a garin lallaɓa ta ne bacci ya kwashe ni nima. Ajiyar zuciya na sauke saboda jiyo muryar Bilal a falon yana tambayar me akayi masa, dukda cikin faɗa da hargagi yake maganar amma shirun da Al'amin ɗin ya yi ya saka na samu nutsuwa har na miƙe daƙyar na shiga banɗaki.

Ina fitowa ya shigo ɗakin yana jan rai kamar numfashin sa zai ɗauke. Na janyo shi jiki na a hankali na ce
"Kasan idan ka bari kukan nan ya fita Dady ya ji muryarka zai dake ka ko? Wai me ma aka yi maka? Wa ya ɗakko ka daga makaranta?" Bai bani amsa ba sai rungumeni da yayi, na ringa shafa bayan sa har saida ya daina ajiyar numfashin bacci ya ɗauke shi daga tsayen da yake kafin na kwantar da shi na zare masa takalman ƙafar sa sannan na miƙe daƙyar ina dafe kaina na fita falo.

Bilal na zaune kan 2 sitter kunnuwan sa saƙale da air pods yana danna wayar dake hannun sa fuskar sa ɗauke da murmushi, lunch box da school bag ɗin Al'amin dake ajiye a ƙasa na ɗauke, motsi na ya saka ya ɗago ido ya kalle ni nayi kamar ban ganshi ba na yi wucewa ta kitchen. Ina jin motsin alamar ya biyo ni nayi maza na kullo kofar kitchen ɗin. Ina jin sa ya zabga tsaki ya ce
"Halima so kike ki ƙure haƙuri na ko? Tun jiya nake binki akan ki zauna muyi magana amma kinƙi wai me yasa kike haka?"

Kwanukan da ban samu na wanke ba na shiga wankewa ba tare da na bi ta kansa ba. Jin har na gama bai fita daga falon yasa na nemi kujera na zauna haɗi da jingina da cabinet dan gaba ɗaya bana jin daɗin jiki na.

Sai da na jiyo kukan Sharifa kafin na fito daga kitchen ɗin na tarar da ita a hannun Bilal yana gani na ya nufo ni yana cewa
"Jikin ta ya yi zafi sosai, kuma kiji numfashinta yanda yake yi". Karɓar ta nayi ta wuce ɗaki ba tare da na amsa shi ba, na sake fitowa na wuce kitchen na ɗakko sauran kunun dana dama mata. Sauran madarar da na ajiye akan dining na nema ban ganta, na ɗaga kai na kalli Bilal dake tsaye shima yana kallo na ya ce
"Am, bari na karɓo a shago nayi amfani da ita". Banza na masa na shiga shayar da ita shi kuma ya fita. Daƙyar take shan nonon saboda hancinta da yake a toshe ta baki take numfashin.

Wata irin mura take yi me zafin gaske. Tunda ya kwashe su ya kai su gidan Hajja ranar Juma'a ko cikakkiyar awa biyu basu yi da tafiya ba sai ganin su na yi jage jage cikin ruwan sama Salima yar Anty Amina ta kawo su wai kuka take tayi shine Hajja ta ce a maido da ita. Tun ranar ta fara mura duk da na basu loratidine da paracetamol, ta Al'amin kwana biyu ta warke ita kuwa kamar ana ƙara murar ga tari da amai dukda na sake kai ta chemist an bata wani maganin amma a banza ganin abun na nema ya wuce hankali ya saka dole na tattara kuɗin dake hannu na na kaita asibiti bayan an yi mata test suka tabbatar mun infection ne, magungunan da aka rubuta mata antibiotics a pharmacy dubu ashirin da huɗu.

Bani da su ba kuma ni da ƙarfin halin da zan kira wani cikin yan uwana na roƙe shi kuɗi a yanzu.
Haka na koma gida na bashi takardar kai tsaye kuma ya ce mun bashi da kuɗi.
"Kina sane kika kaita wannan asibitin ai bayan kin san shegiyar tsada ce da su. Ni bani da wasu kuɗi da zan baki ki siya mata magani yanzu sai dai ki jira zuwa jibi mu gani akwai abinda nake saka rai idan na samu sai a siyo. Banda ma jaye jayen abu normal mura ce fa kin sani amma kinje sai an jawowa yarinya wani ciwon daban" ya faɗa yana danna wayar sa da ta zama abokiyar hirar sa a yanzu ko da yaushe tana hannun sa yana kallo yana murmushi.

Tunda ni na damu da lafiyar ta haka na siyar da zobe na guda ɗaya na siya mata magungunan da abincin ta na yiwa Al'amin shopping ɗin abin tafiya makaranta dan cewa ya yi na ringa zuba masa duk abinda muka karya dashi shi ba ze ɗaukar wa kansa ƙaryar da bazai iya ba.
Chapter 73 · 0% Book details