← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 113 OF 158

Sashe 113

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kayi haƙuri ka ajiye duk wani tunaninka ko shawara a yanzu, Halima yatace, da yardata ta aure shi a yanzu kuma da na hangi cutarwa a zamansu zan datse alaƙar dan haka kowa ya riƙe shawarar sa bana buƙatar su na rigada na yanke hukunci kuma ko mutuwa zatayi wlh sai sun rabu" Abban ya faɗa yana kallona. Hawayena suka ƙara gudu har sannan dai kaina yana ƙasa ban sake ɗagowa ba ya cigaba da cewa

"Kin ɗauka shirun da kikayi zai tabbata gaskiya ba zatayi halinta ba kenan? Tun zuwan da yaron nan abokinsa yayi da maganganun daya faɗa mun na saka mutane suka mun bincike na kuma ringa bibiyar duk wani motsinsa a sannu kuma na gane gaskiyar komai har abinda bai faɗa mun ba na gano da kaina dan shi da ya zo ce mun yayi kawai ko da ace kin nuna buƙatar komawa gidan Bilal mu hanaki saboda Bilal ɗin ba wanda muka sani a baya bane cigaban zamanki da shi kuma zai iya jefa ki cikin halin da zamu zo muna da na sani.

Ba sai na faɗa miki abinda na binciko ba dan kin rigani sanin wasu amma tunda naga har yanzu hankalinki bai tsaya guri ɗaya ba a hakan kike tunanin sake koma masa to babu wannan maganar, yanzun ma na kiraki ne dan kar idan yayi taurin kai na maka shi a kotu ki ce an tozarta uban yayanki, dan haka tun da girma da arziƙi ki faɗa masa ya sallameki".

Na ringa kallon Baba Salahu in ji ko zai sake magana amma bai ce komai ba da alama yaji gargaɗin Abban da ya ce baya buƙatar shawarar kowa. Haka na tashi ina share hawaye jiki ba ƙwari na koma ɗaki na kwanta na cigaba da sabuwar sana'ata.

Ƙarar wayata ta saka na waiwaya na kalli in da take, sunan Yaya Nasir da na gani ya saka na ɗakko ta amma kafin na amsa ta katse. Ajiyewa nayi ina tunanin ko me ya saka ya kirani sai Allah. Ƙila haƙuri zai bani ya ce in koma gidan Bilal ko kuma shima irin Hafiz ɗin ne cin dunduniyar Bilal zaiyi ya ce kar in koma?

Tambayar kaina na shigayi wai ma shi Hafiz meye ribarsa duk a cikin maganar nan? Yanzu ladan me ya samu daya zubarwa da Bilal mutunchi a gaban iyayena? Wani haushinsa ya kamani, wato shiyasa aka ce makashinka yana tareda kai yanzu idan ba halin ɗan adam na rashin tsoron Allah da munafunci ba ta yaya za'ayi abokinka ko ma in ce amininka ne zai kawo sukarka gidan surukai shi da ya kamata ace ko wani aibunka ya ji sai inda ƙarfinsa ya ƙare?

Kiran daya sake shigowa ya tsayar mun da tunani na ɗaga da sallama muryata a dashe saboda kukan da na sha. Daga can ɓangaren Bilal ya sauke numfashi tamkar jaririn daya yini yana kuka, na zare wayar daga kunnena ina kallon screen ɗin dan in tabbatar da waye ya kira amma naga number Nasir ɗin ce dai.

"Dan Allah karki kashe Halims" ya faɗa kamar ya san abinda nake shirin yi kenan. Na dakata da waya a kunne ba tareda na ce komai ba daga can ɓangaren ya marairaice ya ce

"Duk abinda aka faɗa miki ba gaskiya bane wlh so kawai sukayi su raba mu"

"Abban nawa ne yake ƙarya kenan?" Na faɗa cikin dasasshiyar murya, da sauri ya ce
"Aa wlh ba shi nake nufi ba su waɗanda suka faɗawa Abban nake magana ai kin sani dama duk ba ƙaunar ganinmu tare sukeyi ba dan Allah karki bari suyi galaba akanmu kinji my Halims na sani kina so na zaki mun uzuri duk abinda ya faru sharrin shaiɗan ne amma ina neman alfarma ki bani dama mu zauna in warware miki komai na san zaki fahimce ni daga nan sai kiyi mana alƙalanci".
[5/11, 9:51 AM] Zainab Madawaki Dahiru: *KURA A RUMBU*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 48*

Abinda ya fi tsaya mun a rai yanda duk sanda zamuyi magana sai ya ce ya san ina son sa, kenan shi baya so na kuma yana ɗaukata wawuya saboda ina sonsa dole na jure duk wani abu da zan fuskanta daga gare shi ko me?

"Dan Allah karki ce Aa Halims ki taimaka mu haɗu kada ki bari mahassada suyi galaba akanmu" ya sake faɗa cikin marairaice kamar zai fashe mun da kuka. Cikin dakiyar da na aro na azawa kaina na ce

"Ka sameni a gidan Anty Labiba bayan Magriba"

"Gidan Anty Labiba kuma?" Ya faɗa kamar a ɗan tsorace, a taƙaice na ce

"Idan ma ba zaka zo ba ai na tabbatar kaji saƙon Abba a gurin Kawun ka koh?"

"Haba Halims me yasa ki...." Ban tsaya sauraron mai zai ce ba na katse wayar na jefar da ita gefe na dafe ƙirji na da yake duka uku uku.

Siririn kuka na saki, ina jin yanda zuciyata take yamutsawa dalilin famin ciwon son da ya cika ta. Na jima ina kukan sai da aka fara kiraye kirayen la'asar kafin na tashi nayi sallah bayan na idar nayi wanka, ko mai ban shafa ba na zura doguwar rigar abaya na ɗaure kaina da ɗankwalinta na fita falo. Tunani nakeyi yanda Mama zata barni na bi Anty Labiban.

Mama kaɗai na tarar a falo tana shan fura Sharifa na kwance tayi matashi da cinyarta tana bacci na zauna kan kujera ina kalle kalle kafin na ce

"Sai ke kaɗai Mama?"
"Eh, Amirah sun fita da Zainab wai zasu karɓo awara a gidan Sahura ta bayar ayi musu" Maman ta bani amsa a sake yanda banyi zato ba ganin yanzu mun koma kamar wasu abokanan faɗa a gidan kullum cikin ɗaure mun fuska take.

"Anty Labiba fa?" Na sake tambayarta ta ce
"Tun ɗazu ta wuce dama wai hanya ce ta biyo da ita ba zama sukayi ba"

"Lah shine basu mun sallama ba na so fa in bita" na faɗa a sanyaye, na saci kallonta jin tayi shiru itama ni take kallo kamar me karantar gaskiyar dake bayan maganar da nayi sai kuma ta ce

"Kina gurin Abbanku ai sanda suka tafi, sai ki bari gobe in Allah ya kaimu ki je ai"

"Yau ɗin dai na so in je sai na kwana gobe na dawo" na sake faɗa, ga mamaki na sai na ji ta ce

"To sai ki shirya ai ki tafi yanzu tunda Magaji yana nan sai ya sauke ki". Ajiyar zuciya mai ɗan nauyi na sauke kafin na miƙe na wuce ɗaki. Kaya kala ɗaya na zuba a jaka sai ɗan abinda zan buƙata na undies na zura Hijabi na fito har sannan Mama na zaune ta bini da kallo bayan da na mata sallama. A compound muka haɗu da Abba da alama fita zaiyi, naji kamar na juya amma ya rigada ya ganni dole na ƙarasa na amsa masa tambayar da yake mun akan ina zanje.

Shi ya sauke a gidan Anty Labiban, kamar mai tunanin zan tafi wani gurin bai matsa ba sai da na shige gidan nayi murmushi kawai ina cewa "ko Abba ya zata guduwa zanyi ne ya kasa ya tsare".

Ban ɓoyewa Anty Labiba dalilin zuwana gidan ba, tayi shiru tana kallona kafin ta ce
"Wace shawara kika yankewa kanki Halima"

"Ban rigada na yanke shawara ba Anty amma In sha Allahu yau zan sanar da ke matsayata". Tayi jimm kamar tana so ta ce wani abu amma kuma ta fasa sai ta ce

"Toh Allah ya sa muji alkhairi" na amsa da "Amin".
"Zaki tanadar masa wani abu ne?" Ta tambayeni, sai da nayi ɗan murmushi kafin na ce

"Sniper kika tanada ko green leaf?"

Ta fashe da dariya ta ce
"Daga abin kirki?"
"Ai ko shi na san sai yayi shakkar cin wani abu a gidan nan yau" na bata amsa ta wuce kitchen tana cewa

"Toh ai shikenan, bari in ɗorawa mijina abinci yana hanya". Tashi nayi na bita na kama mata aikin, hirar duniya muka taɓa tun ina amsawa kaɗan kaɗan har na ware abinda na manta rabon da inyi doguwar magana irin haka harda dariya inaga tun ranar dana dawo daga Camp ɗin NYSC.

BILAL
Tamkar zai fasa kuka ya faɗawa Nasir inda Halima ta ce su haɗu,
"Tare zamuje amma" ya faɗa Nasir ya ce

"Wa? Ni? Idan ka ganni a lahira toh kaini akayi. Ai kayi mai wuyar tunda har ta amince ku haɗu ai akwai haske a lamarin kawai kaci gaba da addu'a shine ya rage yanzu".

Bilal ya goge zufar da ta keto masa dukda sanyin Ac daya cika motar kafin ya ce
"Toh dan Allah zaka rakani gurin Kawun su Zulaiha, ta ce yana son ganina yau saboda ita ma na kashe wayata tun safe idan ba haka ba addabata zatayi da kira".

Dariya Nasir yayi ya ce
"Ita amaryar ce tun yanzu ta fara isarka? Ikon Allah. Haɗe rai Bilal yayi ya zaro wayarsa daga aljihu ya kunnata tun bata gama saituwa ba kuwa sai ga kira ya faɗo ko suna bai fito ba alamar contacts ɗin ma basu gama booting ba amma ya gane number Zulaiha ce. Ya nunawa Nasir yana cewa

"Ka gani ko?" Ai kuwa Nasir ya bushe da dariya ya ce
"Bala'i, sai kace bokanya? Ta hango ka kunna wayar a madubinta. Alamar yayi shiru Bilal ya masa kafin ya amsa wayar, yanda kasan ɗan da ta haifa tanaji ya amsa ta ce

"Wannan wane irin kut****uba ne zaka kashe waya ayi ta kiranka ba'a samu?"
Chapter 113 · 0% Book details