← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 137 OF 158

Sashe 137

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta soka saboda Allah, ta wahalta maka da jikinta da aljihunta amma ka biyewa duniya ka yi mata sakayya da sharri, wlh ko bata buɗe baki ta nemi sakayya a gurin Allah ba haƙƙinta ba zai taɓa bari ka zauna lafiya ba ga kuma haƙƙin yayan daka barta dasu, baka san cinsu ba baka san shan su ba sutura, rashin lafiya, karatunsu babu wanda ka damu dashi.

Bana zaton tun ranar da suka bar gidanka ka sake sanya su a idanuwanka, idan baka dubi Allah ka sauke haƙƙinsu daya ɗora maka na dole ba ai ya kamata ko dan duniya da gobenka ka jiƙansu ta yanda kaima gaba lokacin da ƙarfinka ya ƙare zasu tausaya maka".

Har ya isa gida yana tilawar maganganun Abubakar kamar karatu, har ya wuce falon Zulaihan sai kuma ya koma a ransa yana jin babu daɗi dukda bai san dalilin hakan ba. Ƙofar a buɗe take dan haka ya tura ya shiga da sallama, Tv na kunne amma an yi muting volume falon kaca kaca daga gani baƙi tayi kuma bata ji zata iya gyara gurin bayan tafiyarsu ba ta tsallake ta barshi a haka.

Kayan dake zube ya tsaya yana kallo, kwalayen pizza, ga raps ɗin shawarma, ragowar kaza sai kwalaye da gwangwanayen lemo d sauran kayan ciye-ciye dai iri iri. Kayan daya gani a freezer waccen ranar suka faɗo masa dan haka ya wuce ɗakinta,
"Haba mana Babe" ya tsinkayi muryarta tana faɗa haɗi da ƙaramar dariya, burki ya ci a bakin ƙofa dan a buɗe ɗakin yake ya shiga kallon kan gadon ta cikin ɗan hasken da yake shigowa daga falo dan ta kashe fitulun ɗakin.

"Yes Babe cigaba I'm enjoying" ta sake faɗa tana sakin nishin daya saka gabansa faɗuwa, yanayin da tayi maganar da nishin da tayi sai ya zo masa tamkar ire-iren lokutan da suke phone sex da Jalilah. Nishin data sakeyi ya saka shi kiran sunanta da ƙarfi lokaci ɗaya kuma ya kunna fitulun ɗakin gaba ɗaya haske ya gauraye ko ina.

Zulaiha dake cikin bargo suna waya da Ahlan, guy ɗin data haɗu dashi ranar da sukaje siyan Shawarma da Bilal, har ga Allah tunda aka ɗaura mata aure tayi alƙawarin barin duk wasu abubuwa da takeyi kuma ta daina ɗin amma ita kanta bata san dalilin daya saka ta kasa tsallake tarkon Ahlan ba, ko da ya fara kiranta ta yaƙi zuciyarta akan ba zata zake amsawa ba dan har blocking layin tayi sai dai yana canza wani layin ya kirata ya kanainayeta da daɗin baki akan shi ba wata mu'amala mara kyau yake so su ƙulla ba kawai ta burgeshi ne yana so su zama yaya da ƙanwa shikenan ta biye masa suka fara waya.

A hankali kuma tunda dama biyu ce ta haɗu kafin ta ankara ya mayar da ita ruwa, dukda waya kawai sukeyi amma tun bata biye masa harta fara suke zantukan da basu kamata ba, ganin kuma ko hoto bai taɓa nema ta tura masa ba iya zancen wayar ne ya saka ta saki jiki ga kuɗi yana tura mata kamar bai san zafinsu ba dama kuma ta farayin broke ta kuma lura da take-taken Bilal shi ɗin ma dai irin sauran mazan da ake bayar da labari ne.

A waje kamar zasu tsinke kansu su bawa mace saboda ƙauna da zarar sun sameta kuma sai a fara zaman haƙuri, tunda sukayi aure watanni kusan huɗu kenan naira biyar bata shiga tsakaninsa da ita ba. Zai yi cefane duk abin buƙata zai siyo ya ajiye mata yana ƙorafi yana mita amma dai ba zai bata kuɗi a hannu ba, toh hakan ma bai dameta ba tana son sa a hakan kuma zata zauna dashi sauran buƙatunta kuma zata nemi kuɗi tayiwa kanta ita wannan ba zai zama matsala tsakaninsu ba tunda dai baya saka mata ido akan harkokinta ko abubuwan da yake ganinta da su.

A bazata taji saukar muryarsa; lokaci ɗaya kuma ta daskare a gurin da take tayi luf a kwance kamar matacciya dan hatta zuciyarta bata bugawa da kyau. Yaushe ya shigo gidan har ya shiga ɗakin bata ji ƙarar buɗe get ko dirin motarsa ba? Ta san dai dama a buɗe ta bar ƙofar falon dalili kuma saboda tana jiransa dan tayi duk yanda zatayi jarabar dake cinta taƙi ta kwanta, yana fita kuma ta koma ɗakinsa ta bincike tsaf amma bata gano abinda ya ɗauke mata ba dan tun ranar data dawo taga an gyara ɗakin tana dubawa bata ga abun ba ta san shi ya ɗauke su kuma tun ranar ta cewa Suby ta sake siyo mata wani amma wai ya ƙare a gurin matar sai an sake kawowa tayi baƙin ciki matuƙa dan ta lura ba zata taɓa samun haɗin kansa yanda take buƙata ba idan bada abun ba sai dai kawai ya jagwalgwalata ya barta da wahala.

Yanzun ma rasa yanda zatayi ya saka ta kira Ahlan ɗin da kanta, a falo suka fara wayar tsoron kada ya shigo ya saka ta dawo ɗaki sai gashi tayi gudun gara ta tarar da zago. Sunanta daya sake kira da takunsa da taji alamar yana matsawa kusada gadon ga Ahlan da shima yake ta Hello Hello jin tayi shiru, lokaci ɗaya ƙwaƙwalwarta ta kawo mata mafita cikin abinda bai wuce seconds biyar ba ta aiwatar, ta latse wayar ta kasheta gaba ɗaya kafin ta turata tsakanin kan gadon da katifa tayi juyi kamar a cikin barci ta cigaba da sakin maganganun da suka fi wanda ya fara ji girma.

Tsayawa yayi yana cigaba da kallonta a hankali kuma harzuƙa da fushin da ya taso masa lokaci ɗaya suka fara sauka kafin ya ya matsa ya shiga buga ƙafarta yana kiran sunanta amma kamar wacce yake zugawa sai ma wani motsi data farayi kamar wacce take tareda Namiji. Duka mai zafi ya ɗana mata a cinya, taji dukan har ƙwaƙwalwarta ba shiri ta wartsake ta tashi zaune zumbur tana sosa gurin idanuwanta suka kawo ƙwalla, Bilal dake tsaye a kanta ya ce

"Menene haka kike yi?"
"Kai zan tambaya akan me kawai ina bacci na zaka zo ɗana mun duka irin haka?" Ta faɗa yaye rigarta gurin daya doke ta ɗin, gefe ya ɗauke kansa dan har pant ɗinta sai da ya fito saboda janye rigar da tayi ya ce
"Bakiyi addu'a ba da zaki kwanta baccin sai wasu sambatu kikeyi marasa kan gado ga ƙofofi kin bari a buɗe kuma ko ina shara" ya nufi ƙofa. Ajiyar zuciya ta sauke a fili kafin ta bi shi da harara haɗi da yin ƙaramin tsaki ta koma ta kwanta tana shafa in da ya doketa. Yanzu da ace ya gane mai takeyi yau ina zata saka kanta? Gaskiya dole fa ta ringa takatsantsan kar taje kwaɓarta tayi ruwa tun ba'a je ko ina ba.

Tashi tayi tabi bayansa jin yana harhaɗa ledoji da kwalayen da suke falon, a nan ɗakinta ya kwana; tun kuma yanayin na son rai har dai yaga ita bata da geji ya tashi ya koma falo bayan yayi wanka ya barta tana tsaki bai kuma san yanda ta ƙare ba bacci ya kwashe shi.

Washe gari da wuri ya fita saboda tunanin daya kwana dashi a ransa, store ɗin da suka ajiye kaya yaje bai kuma ɓata lokaci ba dan a gurin ya tarar da wanda zai karɓi kayan ya buɗe suka ɗiba babu bata lokaci kuma suka tura masa da kuɗinsa cis yanda sukayi ciniki. Jin kuɗaɗe masu nauyi a account ɗin sa ya saka nutsuwa ta saukar masa duk wasu tunani da zullumi da yake fama dasu a kwanakin suka kama gabansu ya shiga sharholiyarsa, 1M ya bawa Fadila gudummawa wanda daƙyar Hajja ta karɓa tana zaginsa tana faɗar maganganu amma ya toshe kunnensa sauƙin daya samu gyaran daya tayar ayi mata kafin bikin Fadila nan da kwana goma da angon da kowa bai sani ba daga ita sai Hajja da Anty Habiba sai Anty Ladidi su suke shirin biki dan ko Abubakar da yake kwana a gidan ya ce bai san komai ba balle sauran.

HALIMA
Da wuri na tashi daga aiki ranar Alhamis, ƙarfe tara nake zuwa mu tashi ƙarfe biyu amma yau ɗin saboda monthly clearance da zanje ya saka na tashi karfe 12. Ina tsaka da wanke hannuna bayan na fito daga banɗaki, Juwairiyya wacce muke service a gurin tare ta shigo ta kalleni ganin na cire lab coat ɗina ta ce
"Ba dai guduwa zakiyi ba Halima?"
"Guduwa kuma sai kace wata ke?" Na bata amsa cikin raha tayi murmushi tace

"Ai da alama yau zaki zama ni ɗin sai dai kinyi wrong timing dan yanzu Dr Sa'id ya shiga lab ɗin mu ya ce kowa ya zama cikin shiri CEO yana hanya".

Ido na zare jin abinda ta faɗa na ce
"Kuma ya rasa ranar da zai zo sai yau da nake da uzuri? Tun fa last week aka ce zai zo?" Tana gyara fuskarta da powder ta ce

"Ai kuwa dai sai yau kuma wlh har waɗanda basu da duty yau gashi can Dr Sa'id yace a kirasu a waya duk kuma wanda bai zo ba ya ce babu ruwansa dan haka kiyi haƙuri kawai ki jira na san ba jimawa zaiyi ba".

Kamar zanyi kuka haka na koma office na zauna, tun last week aka ce zai zo Dr Sa'id kuma ya jaddada har ranakun da bamu da duty mu kasance cikin shiri za'a iya cewa mu fito saboda yace yana so ya gana da duka staffs ne idan ya zo. Ina duba agogo ina zabga tsaki, mutumin da aka ce an ɗakko daga Airport tun 12 gashi har ɗaya ta gota basu iso ba ko dai dama basu taso daga can Abujar bane lokacin da aka tafi ɗakko shin sai Allah. Da wannan mitar na tashi nayo alwalawa ganin zaman ba zai fissheni ba nayi sallah, ina addu'a Dr Sulaiman ya shigo office ɗin yana ganina ya ce na fito da sauri dan haka na shafa na miƙe shaf na manta ban mayar da Lab coat ɗin ba na fita da Abayar dana saka nayi sallah.
Chapter 137 · 0% Book details