← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 158

Sashe 87

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi mai sauti tayi daga can itama tace
"Haka ne, toh yanzu yaushe zaka zo?" Ya ɗan yi jimm kafin yace
"Ina da uzuri yau da yamma zan tafi Abuja idan na samu jirgi amma kwana biyu zanyi zuwa asabar da yamma ko lahadi da safe za dawo sai nazo". Shiru tayi bata ce komai ba, cikin kulawa yace

"Akwai wani abu ne?"
"Toh ai kana da uzuri kaga kuma ba zaka bari saboda ni ba" ta faɗa cikin rawar murya, sai yayi saurin miƙewa zaune daga kishingiɗen da yayi dan alamun kukan da yaji a muryarta lokaci ɗaya ya tayar masa da hankali yace

"Ki faɗa mun menene naji kamar zakiyi kuka ko kuɗi kike buƙata? Kayan abincin da aka kawo sun ƙare ne?"

Maimakon ta bashi amsa sai kawai ta fashe da kuka daga nan kuma ta kashe wayar gaba ɗaya. Ji yayi duniyar gaba ɗaya ta masa duhu hankalinsa ya tashi ba shiri ya tada mota ya cillata titi ya nufu gidan su Zulaihan dan jin ba'asin kukan da takeyi. Daya isa bai ko jira an masa iso ba bayan da yayi sallama ya faɗa gidan, suna zaune a ɗan ƙaramin falon su ita da ƙanwarta Jidda sai Ummansu jigum jigum ya samu guri shima ya zauna.

"Magana daka sani ce dai Bilalu ba wata ba, babu jimawa Yayan mahaifinsu ya fita daga gidan nan sai kaga irin cin mutunchi da tozarcin da yayi mata ya kuma yi rantsuwa akan ranar sadakar Arba'in ɗin Malam kowaccen su ta kawo miji a ɗaura mata aure idan kuma ba haka shi zai zaɓa musu wanda yaga dama ya ɗaura auren a ranar" Ummansu ta faɗa bayan da suka gaisa tayi maganar tana share hawaye da Hijabin jikinta.

Yayi shiru a ransa yana ayyana "wata sabuwa kenan". Duk sai ya rasa mai zai ce musu, ranar Arba'in ɗin Babansu nan da kwana Ashirin fa kenan ake nufi yanzu ta ina zai fara gyaro ɓarakarsu da Halima, Ya yakice Jalila, sannan a auri Zulaihan duka a kwana Ashirin?

Shirun da yayi ya saka Umman cewa
"Ai na san abu ne da kamar wuya amma shi kawun nasu ka sani mutum ne mai wuyar sha'ani babu yanda banyi akan na fahimtar dashi ba amma daga ƙarshe sai cin mutunchi ne ya biyo baya kuma na sanshi da magana ɗaya tunda yayi rantsuwa babu abinda zai saka ya karya ina ganin tunda abun ya kasance da haka sai dai ayi haƙuri kawai a karɓi ƙaddara a yanda tazo, kai ka haƙura ita kuma ta karɓi duk wanda Allah yasa ya zaɓa mata tunda ita Jiddah yaron da yake aurenta dama a shirye yake tana kiran sa ta gaya masa yace babu komai gobe iyayen sa zasuje ayi magana to ai kaga ba kamar kai ba da kake da uzuri kuyi haƙuri kawai".

Tashi Zulaihan tayi cikin kuka ta fice daga falon, Bilal ya bita da kallo yana haɗiye yawu daƙyar kafin ya mayar da kallonsa kan Umman tasu. Ya ma za'ayi ace ya haƙura da Zulaiha? Yarinyar da ya raini soyayyar ta a zuciyarsa tun bata kai munzalin data mallaki wani abu da zai kalla ya burgeshi har ya so ta saboda shi ba?

A sanyaye yace
"Aa in sha Allahu Zulaiha rabona ce Umma, kawai dai nayi zaton zaiyi haƙuri tunda wata huɗu ya rage ta kammala karatunta sannan sai a taso da maganar aure amma tunda hakan ta kasance babu abinda zai gagara in Allah ya yarda zanje nima na samu nawa iyayen". Albarka ta ringa saka masa har ya tashi ya fita, a soro ya tarar da Zulaihan tana kuka nan ya tsaya ya ringa rarrashinta da faɗa mata kalamai masu daɗi bai bar gidan ba har saida fushinta ya yaye tayi dariya sannan suka fita tare ya siyo mata Ice cream da Shawarma ya mayar da ita gida nan ma ya daɗe suna hira kafin ya mata sallama ya wuce yana jin kaso tamanin na damuwar daya wayi gari da ita ya yaye.

Shekararsu kusan goma sha biyu tareda Zulaiha tun tana JSS1 lokacin da yayi TP a makarantar su a lokacin Allah ya haɗa jininsa da yarinyar saboda ƙoƙarinta har kuma bayan daya gama gama saboda ita yaci gaba da zuwa duk sanda ya samu lokaci kafin daga baya zumunchin su yayi nisa ya zama har gidansu yake zuwa a hankali ya zama kamar wani babban yayansu kasancewar su uku iyayensu suka haifa duka mata yayarta ɗaya sai ƙanwarta ɗaya. A sannu sannu shaƙuwar su ta fara rikiɗa zuwa soyayya duk kuwa da cewa Zulaihan bata da wata suffa ko dalili da zai saka ya sota kasancewar kowa ya sani shi mutum ne wanda tsarinsa na auren mace yar gayu ne kuma wayayyiya wadda ta fito daga babban gida ita kuma Zulaiha cikin suffofi ukun babu wadda ta mallaka.

Babanta Talaka ne liƙis wanda bai aje cin yau ba balle na gobe haka nan bata da wani kyau na azo a gani domin bata ko kai Halima ba balle ta kama ƙafar Jalila, tana dai da dirin jiki shima ba can ba, sanyinta da baiwar murya mai cike da shagwaɓa da Allah ya bata shine kaɗai abinda za'a iya cewa zai ja hankalin namiji gareta sai dai shi duk ba dan haka yake sonta ba gamon jininsu daga Allah ne.

Shi yayi ɗawainiyar karatunta tun daga junior secondary ya mayar da ita private daga ta gwamnati data fara har zuwa yanzu kuma da take ajin ƙarshe a Jami'a shi yake cigaba da ɗaukar nauyinta harda ƙanwarta Jidda, wata uku kenan daya siya musu wannan gidan da suke ciki watansu biyu da tareqa kuma a ciki mahaifinsu ya rasu.

Rashin samun haɗin kan Hajja ne ya hana shi ya auri Zulaihan tun bayan data kammala secondary domin Hajjan tace babu yanda za'ayi ya auro mata yar Allah baku mu samu, da wanne zaiji? Nauyinta dana yan uwansa ko kuwa na matarsa da danginta tunda kaf ahalinsu a binciken da aka mata an gaya mata babu mai samun cikakken ci uku a rana, ko hidimar da yakeyiwa su Zulaihan a lokacin a ɓoye yakeyi domin ya san muddin ta sani toh fa ba zata bari ba shiyasa ko da ta hana shi aurenta a lokacin bai matsa ba domin shi da kansa yana so ya aureta a sanda yake da damar bata kalar rayuwar da yake mafarkin sama mata saboda yanda yake tausayinta a ransa.

Yana son Halima har ransa saboda ita ɗin tsarinsa ce sannan kuma tana masa son da ya yarda da wahala ya samu qata mace da zata kwatanta masa irin sa sai dai kuma soyayyarta a zuciyar sa bata ko kama ƙafar yanda yake jin Zulaiha a ransa ba. Kusan kwatankwacin irin son da take masa ne shi kuma yakeyiwa Zulaiha har ga Allah kuma da ace ya samu irin damar da yake fata kafin ya aureta da Zulaihan zai aura ba ita ba. Sai dai a yanzu da al'amura suka kasance ba yanda ya so faruwarsu ba Allah ya ƙaddara ita Haliman ce matar sa ta farko ga kuma rabon da yake a tsakaninsu ya san ba zai samu matsala da ita ba idan ya auri Zulaihan daga baya. Toh amma yanzu komai ya lalace ya tashi daga yanda yayi hasashen faruwar sa kansa kuma ya kulle ya rasa ta ina zai fara gyarowa.

[4/9, 7:34 AM] Hauwa Galadima: *KURA A RUMBU*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 37*

HALIMA

Sati na biyu a Asibiti kafin aka sallameni zuwa lokacin kuma Alhamdulillah na samu sauƙi sosai ko in ce nayi matuƙar ƙoƙarin gurin yakice damuwar dake raina ko dan in samu na bar gadon Asibitin domin a zahiri basu da maganin matsalata kamar yanda kullum Dr yake nanata mun ni zan yiwa kaina maganin matsalata in cire koma menene na saka a raina yake neman halakani. Zama yayi ya mun karatun Yaya da ƙanwa kamar yanda ya ce,

"Ki dubi yanda hankalin iyayenki da yan uwanki duk ya tashi saboda ke, ki kalli yayanki da har yanzu basu san ina suka dosa a rayuwarsu ba idan kika bari damuwar wani can ta kasheki su kika yiwa asara domin tun kina raye dai kinga alamar cewa dake da babu a gurinda duk ɗaya tunda tun bayan da aka kawoki banga wani da aka nuna mun a matsayin shine mijin ki kuma nasan kina da aure dan haka kiwa kanki karatu Halima ki san mai ya kamace ki idan ma zaki mutu ki mutu akan abinda kike da daraja a gareshi".

Daga lokacin na fara ƙarfafar kaina domin dagaske na yarda idan na mutu iyayena da yayana suke kan gaba gurin asara yanda kuma suke zagaye dani kullum cikin nuna kulawarsu idan na cigaba da ɗaura musu damuwata na sani Allah zai iya kamani da haƙƙinsu. An sallameni da tarin gargaɗi akan abubuwan da zan kiyaye, muka koma gida na sake buɗe sabon babin zaman ɗaki domin bana son kowacce hayaniya yan dubiya da suke zirga zirga a gidan kuma takuramun sukeyi shiyasa na zaɓi da inyi zamana a ɗaki ko na samu damar yin tunanin da likita yace in daina amma ba zan iya ba ya zama tamkar mahaɗin rayuwata ne tunda ba zan iya buɗe baki in faɗawa kowa damuwata ba sai dai nayi ta tattaunata tsakanin ƙwaƙwalwata da Zuciyata.
Chapter 87 · 0% Book details