← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 158

Sashe 28

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin ƙoƙarin danne kukan dake son ƙwace mun na gaishe shi ya amsa sannan yace
"Mudassir ya kira ni yanzu, wani abu kika yiwa Bilal ɗin da har ya yanke miki wannan hukuncin?" Se kawai na fashe masa da kuka. Be hana ni ba nayi me isa ta har naji na samu ƙwarin guiwar yin magana sannan nace

"Ban masa komai ba wlh Abba. Kawai dai tun da aka buɗe registration ɗin da naje suka ce se na kawo marriage certificate da sauran takardu na shaidar ina da aure na gaya masa yace ze je ayi, har aka kusa rufewa beyi ba da na sake masa magana shine ya fara faɗa wai na dame shi ranar na zo mukayi magana da Mama Uncle Mudassir yana nan shine yace kawai muje nayi ai ba za'a tsaya jiran sa ba. Ina ga wannan ne yasa yayi fushi ya kuma ƙi tsayawa muyi magana ma balle ya fahimce ni, ni kawai na haƙura Abba tun da dai be yarda ba" na ƙarasa ina sake fashewa da kuka.

Shiru Abba yayi na yan sakanni kafin yace
"Kin haƙura da service ɗin Halima?"
"Toh Abba ya zanyi? Yace be yarda ba kuma ai ba zan tafi ba tare da izinin sa ba" na faɗa cikin kuka, se Abba yace
"Haka ne, toh Allah ya taimaka ya kawo sauƙi cikin al'amarin. Se a ci gaba da haƙuri Allah yayi miki albarka" daga nan ya kashe wayar sa. Kuka sosai na sha bayan mun gama wayar har se da naji kaina ya fara ciwo kafin na rarrashi kaina nayi shiru.

A can gida kuwa bayan da Abba ya aje waya cikin ɓacin rai Mama dake sauraron duk maganganun su tace
"Shikenan abin da zaka ce mata Abba?"
"To me kike so na faɗa bayan wannan Amina? Tace mijin ta be yi mata izini ba, so kike yi nace ta take maganar sa ta fito ko yaya? Idan aka yi haka ai ba da shi muka ja ba umarnin Allah muka take. Tun da ita bata da dabarar da zata lallaɓa shi ta kuma haƙura ba shikenan ba duk wanda ze so mata tayi service ɗin ta haɗa takardun ta guri ɗaya ai ba kamar ita da tayi karatun ba, ki bar maganar nan kawai. Ai ba cewa akayi daga wannan karon shikenan an gama ba. Akwai wani lokacin sanda ya amince mata se tayi amma yanzun a barshi kawai" Abban ya bata amsa ƙarara kuma fuskar sa da muryar sa sun nuna ransa be masa daɗi ba shima da hukuncin da Haliman ta yanke. Tashi Mama tayi daga gurin kawai saboda ranta dake suya idan ta zauna ƙarshe zata sauke fushin ne akan Abban. Tana shiga ɗakin ta ta kira Anty Labiba ta gaya mata.

"Dan girman Allah Mama ki barta. Ai bata sako kowa a ciki ba bata nemi shawarar ki ba. Tun da dai haka taga ya fi mata se mu rakata da addu'a Allah ya bata sa'a amma kar ki wani ɓata ranki akan wannan abun" Anty Labiban ta faɗa mata.

Ina ji ina gani na haƙura da tafiya service duk a son farantawa Bilal. Ranar Juma'a la'asar ina zaune jigum ni kaɗai a falo na kunna tv, ido na ne kawai akanta amma sam bana fahimtar abin da ake yi a ciki. Na zata da Bilal yaga ban tafi ba ze fahimci na haƙura ne na bi umarnin sa ya sakko mu fahimci juna amma sam banga haka ba, babu abin da ya canza se ma ƙaruwa da yayi dan tun shekaran jiyan cefanen mu ya ƙare tas be siyo ba be kuma aje mun kuɗin da zan siyo ba ban ma ganshi ba balle na gaya masa shi kuma kusan sati guda Kenan dama baya cin abinci na dan haka baze ma san menene akwai da wanda babu ba. Kwana ukun da nayi jere ina cin mai da yaji har ulcer ta ta fara motsawa, ina so na fita na yi aike ina tsoron sake yin wani lefin.

Ana kiran sallar Magriba Bilal y shigo, rabon da na saka shi a ido na kwana huɗu kenan yau. Na bishi da ido kamar wadda taga sabuwar halitta, kamar ko yaushe yasha kwalliyar Juma'a cikin shadda se tashin ƙamshi yake. A kan kujerar dake kallon wadda nake kai ya zauna, na sauke ido na ƙasa ina sakin ajiyar zuciya jin idanun sa a kaina. Minti kusan biyu ganin yana zaune har sannan kafin na tattaro yamun baki na na jiƙa maƙoshina daƙyar na furta
"Sannu da zuwa".
"Yawwa sannunki da gida" ya amsa mun, se na ɗaga kai na kalle shi jin muryar sa a sake sak ba fushi ba ɓacin rai. Hannu ya miƙa mun alamar naje gare shi, ban motsa ba se hawaye da suka ɓalle mun kamar an kunna famfo. Shi ya taso ya dawo in da nake ya ɗaga ni tare da rungume ni nan na samu dama na ringa kuka kamar wadda aka aikowa da mutuwar iyaye. Shiga sallah da akayi yasa na janye shi kuma ya wuce ciki da sauri ya yo alwala.

Be buɗe baki ya bani haƙuri akan abin da ya faru ko ƙauracewa gidan tsayin sati ɗaya da yayi ba amma ya nuna mun a aikace. Ya ringa tattali na yana ji da ni kafin kace me na manta da duk fushin sa dake zuciyata muka cigaba da zamanmu kamar wani abu be faru ba. A haka muka sake cinye watanni biyu wanda ya kama wata takwas kenan da auren mu. Shirye shiryen azumi ya kankama dan ana lissafin saura kwanaki biyar ko shida a fara azumin watan ramadan. A tsayin tashi na na saba a gidan mu muddin aka ce azumi ya gabato da wata ɗaya muke fara shirye shirye. Mama tana fitar da kayan kitchen ɗin ta a wanke komai ta ware waɗan da zata ci gaba da amfani dasu sauran a bayar sannan ta zuba sababbi wanda nasan Abba ne yake bayar da kuɗin. Kafin a ɗauki azumi kusan abin da baze ajiyu bane kaɗai ba'a siya a gidan mu a ajiye haka batun kayan sallah wani lokacin kafin a ɗauki azumi an gama mana ɗinki.

Tun da watan sha'aban ya kama nake yiwa Bilal zancen shirin azumi se ya ce mun se kace wani sabon abu kamar bamu taɓa yin azumi ba shirin me za'ayi? Dake muna da kayan abinci, buhun shinkafar dafawa uku aka mun ta gara data tuwo biyu, haka dangin su taliya zuwa mai komai uku har carton ɗin maggi da gishiri ban da ma dangin Bilal dake yawan zuwa dan dai cikin mutum biyu zamu iya fiye da shekara ma ƙila be fara siyan abinci ba. Duk kuwa sanda wani ze zo na dafa abinci na bayar ko be yi magana ba se naga ɓacin rai a kan fuskar sa, na rasa irin wannan hali da Bilal ya tsira akan abinci.

Sanda na buɗe buhu na biyu haka ya ringa bala'i wai na ɓarnatar da buhun shinkafa a wata shida a haka ma wai dan ba ita ake ci kullum ba da kenan a wata ɗaya zata ƙare. Yanzun shinkafa buhu ɗaya ta rage mana da saura kaɗan a buhun da be ida ƙarewa ba, ina so cikin azumi ko ba kullum ba na ringa dafa abinci ana yin sadaka amma ban san ko Bilal ze amince ba.

Na rigada nayi list na duk abinda zan iya buƙata da azumi se wanda ba a rasa ba jira kawai nakeyi ayi albashi na bashi ya siyo mana. Ranar alhamis aka fara yin albashi, a kunne na naji yana waya da wani ɗan gurin aikin su ya gaya masa sun samu ƙarin albashi. Har raina nayi murna saboda ina tunanin ƙarin da suka samu ze saka mu ƙara samun walwala tunda kusan cefanen gidansu a kansa yake dukda yayyen sa mata biyu suna auren masu wadata kuma ba laifi suna hidimtawa mahaifiyar su haka ƙanin sa Abubakar matashi ne me zuciya sosai amma kullum Hajja cikin kiran sa ya bata kaza ya kawo musu kaza abu kaza ya ƙare take be kuma gajiyawa ze ɗauka ya kai mata hakan yasa nake ɗauke kai ga yanayin yanda yake tafiyar da namu cefanen na ke kuma yin abin da naji ina so in har ina da kuɗi a hannu na. To Abban da yake bani kuɗin tun zancen NYSC na shima na fuskanci chanji a gurin sa, da wuya in je gida na tashi tafiya ya bani ƙasa da dubu biyar kuma se yace na ɗauki duk abin da nake da buƙata a gidan tun lokacin kuwa yanzu idan naje dubu biyu uku har dubu ɗaya bani yake yace na hau mota. Kasancewar na saba da ɗan riƙe kuɗi a hannu na yanzu kuma me banin ya fara janye mun tallafi yasa duk nake ji na a takure.

Ban bashi list ɗin da nayi a ranar alhamis ɗin ba se na bari washe gari juma'a gurin ƙarfe goma bayan ya gama shiryawa ze fita sannan na ɗakko masa takardar. Kwata kwata abubuwan dana lissafa a ciki basu haura na dubu goma sha biyar ba zuwa ashirin wanda kuma ina da yaƙinin zasu kaimu har bayan sallah da nisa ma. Ina murmushi cikin raina ina yaba zati da haiba irin ta Bilal. Kullum ƙara kyau da kwarjini yake a idanu na musamman da yayi yar kiɓa jikin sa ya cike ya zama cikakken magidanci yanzu, kullum ya fita cike nake da zullumin kar mata su bibiyar mun shi. Amma na yarda dashi na kuma san bashi da kwashe kwashe.

Jin yana mun sallama yasa na miƙa masa takardar ya karɓa yana juyata.
"List ne na abubuwan da zamu buƙata kaga yau za'a fara duba wata" na faɗa ganin yana kallona da sigar neman ƙarin bayani. Se ya buɗe takardar ya shiga bitar abubuwan dana rubuta
Chapter 28 · 0% Book details