← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 158

Sashe 134

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Da sassafe mutane suka buga mun gida, na fita na same su suke sanar mun da sun siyi gidan ne kuma su ba'a faɗa musu ma da akwai yan haya a ciki ba dan mutumin tafe yake da yara da zasuyi masa shara su wanke gidan wai amarya za'a saka nan da sati ɗaya dan ya ce zuwan da yayi na ƙarshe lokacin ana aikin gyaran gidan kuɗi ne bai cika ba sai yanzu aka bashi muƙullin gidan".

Bilal ji yayi kamar ba hausa mutumin yakeyi masa ba, lokaci ɗaya kuma tunaninsa ya tafi akan tabbas sai dai idan asalin wanda aka siyi gidan a gurinsu ne suka sake siyarwa da wani kuma Jalilah ce zata warware wannan matsalar tunda ita ya san waɗanda ta siyi gida a hannunsu shi takardu da muƙulli kawai ta bashi idan bai manta ba tace gidan na saurayin wata ƙawarta ne.

"Ka kwantar da hankalinka Alhaji in sha Allahu yanzu zan kira asalin wanda na siyi gurin a hannunsa duk yanda ake ciki zaka ji ni" ya bashi amsa cikin kwantar da murya. Alhaji Lawan ya ce

"Gara dai, dukda ni kam na haƙura dan idan baka manta ba sai da nayita nanata maka bana son rigima, idan ka san gurinka akwai rigimar gado ko ta gwamnati akansa ka faɗa mun dan na shiga irin haka banji daɗi ba ƙarshe sai asara na ɗauka dan filin gomnati ne mutumin yayi ginina ciki na siya amma kace babu komai, to ni dai na haƙura ka dawo mun da kuɗi na kawai ka riƙe gidanka, dama tun safe na kira lawyer na na shaida masa komai zaizo ya sameka yanzu haka ka gammu har munci ƙarfin kwashe kaya daga gidan dan haka ina sauraron kuɗi na" daga haka ya katse wayar ba tareda ya bari Bilal ɗin ya sake cewa komai ba.

Tsaki Bilal yayi bayan daya sauke wayar daga kunnensa yana cewa
"Ai da sauƙi ka tunda ka saba ɗaukar asara wannan karon ma haka zakayi haƙuri wlh".

Jalilah ya sake kira, wayar na dab da katsewa aka ɗaga ya sauke ajiyar zuciya sai dai kafin yayi magana muryar Namiji daya ji ta saka murnarsa ta koma ciki

"Tana cikin uzuri, idan saƙo mai muhimmanci ne ka faɗa sai a sanar mata" mutumin da muryarsa ta nuna ba asalin bahaushe bane ya faɗa. Tunani ya tafi akan wane uzuri takeyi? Ba zai wuce tana tareda wani namijin suna lalata ba dai ya san, yayi tsaki wani abu mai kama da kishi ya taso masa murya a cuskule ya ce

"Ka ce mata Bilal ya kira kuma uzurin gaggawa ne".

Gidan Hajja ya wuce, ya tarar da ita da Fadila da tulin kaya dangin atamfa, leshi da materials suna ta dubawa bakin nan kamar zai tsage saboda murna ko sallamarsa duk su biyun ba su ji ba saida ya shiga cikin falon kafin suka lura da shi.

"Yawwa kamar kasan dama yanzu nake so na kiraka ka zo" Hajjan ta faɗa bayan data amsa sallamarsa. Yana kallon kayan ya ce

"Waɗannan fa?"
"Lefen ƙanwarka ne" ta bashi amsa tana tura masa wani ɗaurin kuɗi da a ƙalla zasu iyayin miliyan ɗaya ko sama da haka. Cikin muryar data bayyanar da farincikin da take ciki tace

"Miliyan biyar ya bata kuɗin lefe da sadaki, kaga siyayyar da tayi akwai wasu a ɗaki da kuma sauran da ba'a kawo ba ga dai abinda yayi saura nan sai ka haɗa ka siya mata kayan ɗaki irin na Halima da aka fitar dan ka san ba ƙaramin gida zata shiga ba. Hassadar da kayi mata ka ƙi ka mata hanyar abokinka gashi ta zame mata taki Allah ya kawo mata wanda ya dokeshi a arziƙi".

Shi dai kallon Hajjan kawai yakeyi harta kai aya kafin ya ce
"Yaushe Fadila ta samu miji har aka karɓi sadaki bamu sani ba? Kuma su Baba Sani ne suka karɓa ko su Yaya Aminu?"

"Uwar su Baba Sani da Aminu ce ta karɓa, ni ce zan zake soko Sani a cikin sabgata? Ai har abada wlh. Kuma Fadilar budurwa ce da sai wani ya karɓar mata sadaki ko me? Kai ma ɗin abinda ya sa na faɗa maka yanzu saboda kai zakayi kayan ɗaki ne idan ba haka ba cikin yan gayya zaka fito sai ya rage kwana biyu ɗaurin aure kafin a sanar muku" Hajja ta bashi amsa. Ya sauke ajiyar zuciya ya ce

"Allah ya sanya alkhairi, zan kuma bayar da gudummawa abinda ya samu amma batun nayi mata kayan ɗaki bai taso ba tunda dai ba'a faɗa mun da wuri ba balle nayi tanadi dan bani da wasu kuɗi a halin yanzu".

Hannu Hajja ta shiga tafawa tana salallami yanda kasan wacce taga bala'i tsirara kafin ta lailayo ashar ta watsa masa tana cewa

"Lallai Bilal, ni zaka kalli tsabar ido na kace mun baka da kuɗin da zaka yiwa yar uwarka kayan ɗaki amma ai kana da kuɗin yiwa yar iskar fitsararriyar matsiyaciyar matarka ko?"

Runtse idonsa yayi dan sosai yaji zafin kalaman data jefi Zulaiha da su, yana ji ta ringa sababi tamkar zata aro baki tana zagin Zulaiha da iyayenta dashi kansa.

"Karka ɗauka shirun da nayi maka kafi ƙarfi na ne ko kuma bani da yanda zanyi da kai, wlh Bilal; kaƙi yin abinda nace a lokacin zan nuna maka asalin kalata daka manta. Tunda ka auro yar iskar yarinyar nan ka ɗaga waya ka kirani ma ya zama sai sa'a balle ka tako ƙafarka ka zo cikin gidan nan sai dai idan taka ce ta kawoka, to ba duniya na haifawa kai ba, babu kuma wasu yan iska da basu tayani shan wahala da rainonka ba da zasu fini jin daɗinka a yanzu dan haka kayi duk yanda ka so nima ba zan fasa yin abinda na so ba" tana gama faɗar haka ta shige ɗaki ta barsu.

Yana tafe yana lissafa sabon jidalin daya same shi, yanzu tsakani da Allah a ina Hajja take so ya nemo kuɗin da zai yiwa Fadila kayan ɗaki a sati uku kuma ma wai irin na Halima ita ya san nawa ake siyar da irin kayan ne?

Gurin Nasir ya wuce suka sake tattauna batun gidan yana sake nanata masa
"Wlh Alhaji Lawan bashida daɗi, rufin asirinka ɗaya kuɗin sa ya fito tunda ya ce ya haƙura da gidan idan ba haka ba ina jiye maka tijarar mutumin nan wlh"

"Ai sai dai yayi koma menene ciniki ne kuma ya biya an bashi gida da takardu ya rage tsakaninsa da su can suje wanda yafi ƙarfi ya mallaki guri" Bilal ya faɗa, Nasir dai bai sake ce masa komai ba ya kamo wata hirar wacce batayi tsayi ba Bilal ɗin ya masa sallama ya wuce dan gaba ɗaya babu abinda yake jin daɗi yanzu komai ya masa zafi mafita kawai yake nema.

Yawo ya ringayi a gari har yamma kafin ya koma gida har sannan kuma Zulaiha bata dawo ba dukda ba sabon abu bane dama idan ta fita kawai sai an ganta. Kitchen ya shiga ya duba ko zai samu abinda zai ci dukda ya san da wahala, ya gama buɗe-buɗen kwanukan daya gani amma babu komai a ciki ya wuce ya buɗe freezer yana tsaki, bai taɓa shiga kitchen ɗin bai samu abinda zai ci ba a sanda Halima tana nan. Bayan leftovers da take ajiyewa ga kayan ƙwalama kala-kala har sanda aka janye mata tallafi daga gida in dai ta samu kuɗi ko yaya ne sai tayi wani abun na taɓawa ta ajiye kuma duk shi yake cinyewa har idan ta rigashi ta cinye abinda yayi saura ma ya samu bakin yin masifa.

Da mamaki ya kalli cikin freezer dake danƙare da kayayyaki, kaji, jan nama, kifi kala-kala gasu nan. Ya rufe yaja baya ya tsaya yana tunanin daga ina aka samo su? Domin dai tun cefanen farko daya mata irin haka ta cinye bai sake siyowa da yawa irin haka ba, da Halima ce sai ya ce daga gidansu aka kawo mata amma Zulaiha fa, ya sani kaf danginta na uwa da uba babu mai iya yi mata haka.

Fita yayi daga kitchen ɗin har zai fice daga falon gaba ɗaya kuma ya fasa ya wuce ɗakinta. Yanda kasan ɗakin Namiji ko ina an zubar da kaya wankakku da masu datti, ya ringa yamutsa hanci yana tattare mata kayan sai yaji ɗakin ma har wani tashi yakeyi. Tsaf ya gyara kayan daya kwashe ya ɗaure mata su a zani dan ko laundry basket bata da shi, ya cire bedsheet ɗin da ya fi wata ɗaya akan gadon sai da ya sha lalube kafin ya samo wani ya shimfiɗa.

Wardrobe ɗin tata kanta kamar ta yara komai da mazauninsa daban, ya ringa hasaso wardrobe ɗin da take a gurin da ƙatuwar gaske data sha ado da mudubi kowanne compartment da abinda take sakawa a ciki, ɓangarorin atamfa daban hala lace da sauran kayanta ga ƙamshi Halima ko bata fesa turare ba a hakanta ma ƙamshi takeyi.

Gefen gadon ya samu ya zauna yana shafa goshinsa da hannu ɗaya, sanda suke tare ya raina tsaftarta, a hakan gani yakeyi bata iya ba ko shara tayi in dai yana nan sai ya sake maimaitawa ko idan tanayi ya ringa kushewa kenan ya ce nan bai sharu ba bata goge can ba can batayi kaza ba sai kace ba mace ba aikin gida ma ace shi Namiji ya fita iyawa duk idan yayi mata hakan sai dai tayi murmushi kawai bata taɓa nuna ɓacin rai ko tayi fushi ba sai dai ma ta nuna jin daɗi dan tana yawan faɗa tsaftarsa tana cikin abubuwan da take so a tattare dashi.

Tashi yayi idonsa ya sauka kan drawer dake saman mudubi wacce sai an lura da kyau sannan za'a gane ana iya buɗeta, ya buɗe ido cike da mamaki yana kallon abubuwan da suke ciki, rafar yan dubu-dubu daya gani ya ɗauka guda ɗaya ya shiga juyawa a hannunsa kafin ya mayar ya ajiye ya ɗauki wata yar kwalba data ja hankalinsa.
Chapter 134 · 0% Book details