← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 151 OF 158

Sashe 151

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Zulaiha ya bari ya koma can gurinsu Hajja, itama ya tarar tana bacci. Su Anty Habiba harda wasu daga cikin yan uwan Hajjan suna gurin Fadila ce kaɗai babu suka wuce gida tareda Anty Amina ta ɗebowa Hajjan abubuwan da zata buƙata daga can suka biya gurin Bilal suka tarar da yan uwan Zulaihan Ummanta da ƙanwar Umman Anty Habi sai Nuratu da Mijinta. Har sannan bai farka ba. A nan ya bar Anty Amina ya wuce ya kai kayan Hajjan, haka sukayi ta jigila tsakanin Asibitoci biyu har dare kafin yan dubiya suka wuce gidajensu sai masu jinya aka bari.

Abinda ya saka ya ɗan da sakewa Zulaiha fuska jin tace zata kwana da Bilal ɗin daya ce ta wuce gida shi zai zauna tace Aa har kaya ma taje ta ɗakko shima ta haɗo masa abinda zai iya buƙata idan ya farka. Sai lokacin ya tambayeta motar Bilal ɗin fa? Tace masa ita dai data fita nemo wanda zasu taimaka mata bata ganta a wajen ba.

Washe gari da Asuba Bilal ya farka gaba ɗaya dan ya farka da yammacin jiyan amma suka sake mayar dashi bacci saboda jinin bai sauka yanda suke buƙata ba. Jikin yayi kyau sosai dan da kansa ya tashi ya shiga banɗaki dukda dai yaba dafe kansa da yace yana sara masa har sannan. Tarar dashi ido biyu da Abubakar yayi ya saka yace a basu transfer kawai su koma can gaba ɗaya likita kuma bai ɓata lokaci ba ya basu aka ɗauke shi a Ambulance shi dai Bilal kallonsu kawai yakeyi dan tunda ya farka bai yi wata doguwar magana ba har aka kai shi ɗakin da Hajja take a Retainership.

Bayan da Anty Amina taje aka ɗauketa itama daga General Emergency da aka fara kaita aka mayar da ita can tunda suna da file kuma account ɗin su is loaded, ɗaki ɗaya aka kwanar dasu, ganin Hajja da har sannan bata ko motsa ba ya saka ya magantu ya shiga tambayarsu mai ya sameta?

Sai yammacin ranar Hajja ta farka wannan ya saka hankalinsu ya sake kwanciya sai dai bata ko yi awa ɗaya ba jiki ya sake rikicewa kuma aka rasa abinda ya sameta sai daga baya wata nurse ta lura da kumburin da guiwarta tayi baby ɓata lokaci aka wuce da ita X-ray, ashe faɗuwar da tayi ne karayar da tayi a guiwar wancan lokacin ƙashin ya sake gocewa dan dama lallaɓa ƙafar kawai takeyi tun lokacin ba wai ta koma dai-dai bane. Sabon ɗori aka sakeyi mata sannan aka raba musu ɗaki da Bilal saboda yan dubiya da likitan yace surutansu zasu dameta, shi kansa Bilal ɗin sun ƙi su barshi ya samu isasshen hutun da yake da buƙata balle ita da aiki ya dawo sabo.

Sai da suka kwana uku a Asibiti kafin Fadila da Mijinta sukaje. Allah ne kawai ya ɗorata a kansa, duk irin kuka da kururuwar data ringayi bayan Abubakar ya kirata a waya ko kallonta Ahlan ɗin bai yi ba daga ƙarshe data ishe shi ya kamata ya mata shegen duka wanda dama ya riga ya zame mata tamkar abinci, idan bata ci da safe na zata ci da rana ko da dare sai dai idan Allah bai saka tayi kuskuren da yaga ba zai iya ɗauke ido ba.

Tunda yan rakiyarta suka gama ficewa daga gidan ta tashi ta gyara kwalliya tayi amfani da duk wasu abubuwa da aka bata saboda lokacin ta fita falon saman ta zauna tana jiran Ango da sai da dare ya fara nisa kafin ya shigo gidan ya kuma fara da kwance mata jakar tsabar rashin mutunchi da tijarar daya tanadar mata.

Bai ko iya jira gari ya waye ba, a daren tana naɗe kan kujera tana dakon zuwan Habibinta su murji soyayya cikin aminci. Burinta ya cika tayi irin auren da take fata, ta samu matashin mai kuɗi kuma kyakkyawa ga gida na nunawa sa'a da kayan alatu cike duk masu yi mata dariya da cewar alhakin Umar tsohon mijinta ne yake bibiyarta gashi nan tunda suka rabu ta kasa samun miji shi kuwa tuni yayi aure har matarsa tayi haihuwa biyu basu san tanadin da Allah ya mata ba yanzu sai su banbance tsakanin ita da shi waye yafi wani samun cigaba?

Tana tsaka da wannan tunanin ta ji ana kwarara mata kira kamar yaƙi daga ƙasa, da fari bata ɗauka muryarsa bace sai da ya fara hawowa saman sukaci karo a bakin ƙofa zata fito yana shirin shiga ya kuwa kwaso ashar ya watsa mata yana tambayar shi ɗin sa'an uwarta ne da tana ji yana kiranta amma tayi masa banza?

Mamaki ya saka ta cewa
"Lafiyarka kuwa Ahlan? Mai kasha haka?" Take kuwa ya naɗe hannun riga ya gwada mata aikin marasa lafiya na gaske. Ya mata dukan tsiya sannan ya tankaɗa ƙeyarta ciki ya kwanta da ita cikin mafi ƙasƙancin yanayi sai kace wata dabba kafin ya tsallaketa yayi ficewarsa bata sake sanya shi a ido ba sai washe gari da yamma zuwa lokacin tayi kuka har idanuwanta suna neman su daina gani ba kuma ta jira wani ya biya mata karatun ba ta fahimci in da kwaɗaiyi da son zuciyarta data mahaifiyarta ya jefo ta.

Da yammacin ranar kuma ya ƙarasa warware mata komai, kamar yanda ya sanar mata shi tun farko bai yi niyyar aurenta ba, rashin amince masa da batayi a waje bane ya saka ya canza shawara dan tunda yawunsa ya tsinke to fa ba zai haɗiye ba sai ya ɗanɗana shiyasa ya yanke shawarar aurenta da niyyar ya saketa bayan burinsa ya cika amma kuma bayan faruwar komai yaji tayi masa yanda yake so dan haka ya fasa ba zai saketa ba sai dai ta sani babu soyayya a zamansu, zata zauna ne kawai a matsayin abun biyan buƙatarsa domin ita ɗin bata kai ya kirata da matarsa ba.

"Sharaɗin zaman lafiyarki a gidan nan na farko ban yarda wani daga cikin makwaɗaitan danginki ko uwarki suzo gidan nan ba, balle aje kan ƙawaye ko wasu tarkace hakanan kema ba zaki fita ko ina ba" ya faɗa mata. Ya lissafa mata sauran Sharuɗan sa, ta ringa kuka tana roƙonsa daya taimaka mata ya sawwaƙe mata amma yace bai san zance ba ko tana so ko bata so sai fa ta zauna dashi kuma ya ƙwace wayarta. A ɗan lokacin nan taga bala'i ganin idonta, babu rashin ci babu na sha ga muhalli mai kyau Ac har ta isheta kuma bata isa ta kashe ba idan ya so mugunta haka zai ƙure sanyin duka Ac gidan idan kuma yan iskansa suna kusa yace ta cire kayanta tayi ta yawo tsirara yana kallonta bata isa kuma tayi ko jimm kafin ta aikata abinda ya umarceta ba zai rufeta da duka duk ya canza mata kamannin fuska saboda mari da hauri da ƙafa.

Yau ɗin ma tayi mamakin yanda tana zaune kawai ya shiga yace ta shirya suje duba Hajja. A hanya toshe kunnuwanta kawai tayi saboda cin mutunchi da zagin da ya ringa mata da iyayenta kuma bata isa ta yi ko tari ba balle ta mayar da martani.

Kallonta suka ringayi kamar sunga wata baƙuwar halitta, ga dai Lace har Lace a jikinta da mayafi na garari amma sai tayi daban a cikin kayan kai idan ba wanda ya mata mugun sani ba ma ba lallai a kallo ɗaya ka gane Fadilan bace. Hajja dai sai ido, duk inda Fadilan ta motsa sai ta bita da kallo kawai ko sannun da take mata ta kasa amsawa. A ɗar ɗar Fadilan ta ringa gaishe su tana satar kallon Ahlan ɗin daya kame a gefe yana kallonsu a ɗage kamar yaga kashi, sai da ya mula kafin kuma ya musu gaisuwar jam'u kuma ta raini wai
"Sannunku" sai kace ba yayyen matarsa ba harma da iyayenta dan akwai ƙannen Hajja biyu da matan Baba Sani a gurin.

Daƙyar ta iya tambayar Yaya Bilal suka ce mata yana ɗakin dake kallon wannan, ta saci kallon Hajja wadda da alama mamaki ne ya kulle mata baki kafin cikin murya tsantsar ladabi ta ce masa suje can ɗakin su duba Bilal. Rafar yan dubu-dubu guda biyar ya zaro ya ajiye akan drawer dake gefen gadon kafin ya juya cike da taƙama ya fice daga ɗakin duk suka rakashi da ido itama ta bishi simi simi kamar marainiyar kyanwa.

"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un mun shiga uku dama haka mijin Fadilan yake?" Anty Habiba ta faɗa tana tafe hannu, nan ta buɗewa masu jira fili suka fara sakin maganganun da suka cika musu baki, Anty Amina ta miƙe tana cewa

"Amma dai kun san nan ba gurin mayar da zance bane ko? Dan Allah ku fita, dama ai sun ce anyi yawa a ragu haka ko ta samu ta koma bacci ta huta".

Su Fadila kuwa ɗakin da Bilal yake suka shiga, ita ta fara shiga ya tsaya yana amsa waya. A nan ta tarar da Abubakar, sai da tayi dagaske gurin danne kukan daya so ƙwace mata dalilin ganin wanda take ganin shi kaɗai zai iya cetota daga bala'in da take ciki amma bata isa ta faɗi wani abu a yanzu da suke tareda Ahlan ɗin ba. Gaban gadon da Bilal ke kwance ta isa tana amsa sannu bayan ta gaida Abubakar daya zuba mata ido cike da mamaki yana kallonta, ta gaisa Zulaiha dake zaune gefensa dai-dai nan Ahlan ɗin ya shigo ɗakin da sallama kamar bashi ba.

Fuska a sake ya miƙawa Abubakar hannu suka gaisa kafin ya matsa gaban gadon yana yiwa Bilal dake kallonsa kamar ya samu Tv sannu.
Gyara tsayuwa yayi kafin ya shammaci Zulaiha da ganinsa ya saka tayi suman zaune ya mintsineta a gefen ciki. Ba ƙaramin ƙoƙari tayi gurin hana kanta yin ihu ba, sai ta mike da sauri ta fice daga ɗakin ya zauna a inda ta tashi yana sake yiwa Bilal sannu ya gyaɗa masa kai alamar amsawa.
Chapter 151 · 0% Book details