← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 158

Sashe 92

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Ni wlh duk sai jiki na yayi sanyi da al'amarin, anya kuwa ba gidan ƙananan mutane ka nemo auren nan ba Bilal?"
"Shi ɗin shine me matsala Kawu dan baka san irin wahalar da suke sha a hannun sa bane wlh mutumin bashi da kirki amma mahaifinsu ai kace k sanshi mutumin kirki ne haka mahaifiyar su ita kanta yarinyar na gaya maka munfi shekara goma tare tun tana yar yarinya dan haka halayyarta babu wacce ban sani ba babu wata matsala wlh" Bilal yayi saurin faɗa, Kawu Sani ya gyaɗa kai ya ce
"Toh Allah ya tabbatar da Alkhairi ya sa anyi a sa'a, gobe idan Allah ya kaimu zanjw in samu Hajjan in mata bayani".
Sosai yayi masa godiya kafin ya cika shi da kuɗaɗe sukayi sallama ya wuce yana jin farin ciki na ratsa shi ta ko ina.

Gidan su Zulaihan ya wuce dan bashi da wani buri kuma a yanzu illah ganin fuskarta kuma a matsayin matarsa. A kan kwana sukayi clashing da Alhaji Saleh da Anty Labiba, fes ya gansu kamar yanda suma suka ganshi sai da yaji kamar yayi reverse ko yayi layar zana ya ɓace ɓat kawai daga gurin. Tun da suka dawo unguwar duk ranar da zaizo gurin Zulaihan tunda aka tashi hanyar da ake shigowa ta can baya sai yayi doguwar Addu'ar Allah ya saɓa haɗuwar sa da duk wani wanda ya sanshi a unguwar kuma yana cin sa'a addu'ar sa tana karɓuwa dan sau ɗaya ya taɓa haɗuwa da Alhaji Salen har suka gaisa a lokacin ya ce masa gurin wani abokinsa ya zo can ƙasansu bai kuma damu ba dan ya san ba lallai ma ya ce mata ya ganshi ita ɗin ma sau ɗaya ya taɓa hangen motar ta lokacin ma da mashin yake zuwa ya kuma gota gidan sosai ya waigo ya hango ta fito ya san kuma bata ganshi ba amma a yau ɗin sai yake jin kamar duk wanda ya kalle shi zai gane abinda yake faruwa.

Haka yaja mota jiki ba ƙwari ya wuce yana hangensu ta mirror, ita kuwa yi tayi tamkar ma bata ganshi ba har sai da Alhaji Saleh yace mata
"Kamar Bilal ne ya wuce a waccen motar ko?"
Ta ɗan juya ta kallo bayan motar tace
"An ya kuwa? Bilal ai bashi da mota".
"Ina ganin sa jefi jefi a wannan motar, a nan ɗin ma mun taɓa gaisawa sau ɗaya yace gidansu wani abokinsa yazo can ƙasa". Cikin rashin mayar da hankali tana danna waya ta ce
"Allah sarki".

Bilal kuwa ganin Zulaiha ya mantar dashi haɗuwar su dasu Anty Labiba. Sun daɗe a mota suna hira cikin shauƙi dan basu farga da lokaci ba har sai da Ummansu ta turo Nuratu ta buga musu glass lokacin sha ɗaya har da rabi da wasu mintuna kafin ta wuce ta barshi yana ƙoƙarin saita nutsuwarsa kafin ya tayar da motar ya wuce gida. A hanya yana tafe shi kaɗai yana tunani, so yake ya kori waswasin da shaiɗan yake ƙoƙarin cusa masa amma kuma tunanin yana nema yafi ƙarfin sa.

Bai tsammaci yanda Zulaihan ta sake dashi a tashin farko da irin haɗin kan da ta bashi ba. Sai ya tuna irin wannan haɗuwar tasu ta farko da Halima, yanda ta ringa rawar jiki a lokacin har ƙarar bugun zuciyarta ya ringa ji numfashinta yayi ɗumi baka buƙatar a faɗa maka a matuƙar tsorace take lokacin. Sun fi ƙarfin wata shida kafin ta fara gane kan harkoki sosai dan ko kiss bata iya ba shi ya koya mata fara tarayyarsa da Jalilah kuma ya sake fayyace masa tsakanin macen da ta saba da maza da yawa da kuma wacce namiji ɗaya ta sani, akwai banbanci sosai domin duk ƙwarewar matar aure ba zata kamo ƙafar macen bariki ba.

Guri ya samu yayi parking abubuwan da suka gabata suka fara dawo masa daki daki. Ita ta fara kawo hannu jikin sa, shi bai ma yi niyyar yi mata wani abu ba a yanzu ba bayan riƙe hannunta amma ta ringa shige masa ƙila da bai kama kansa bama ya biye mata da a motar zasuyi mai gaba ɗayan. Ji yayi zufa ta fara tsattsafo masa duk da sanyin AC da ta cika motar, can wani ɓangare na zuciyarsa ya ayyana masa ba abinda yake zato bane Zulaiha ba zata taɓa zama irin waɗannan matan ba. Ya santa tun ƙuruciya ya kuma yarda da tarbiyyarta hakan ba zai taɓa kasancewa halinta ba. Da wannan tunanin ya ringa tausar kansa har ya samu nutsuwa duk da ba wai tunanin ya barshi gaba ɗaya bane ya kasa cire kokonton gaba ɗaya amma ganin idan ya bari shaiɗan yayi galaba akansa ya saka masa wasi wasi na banza wanda ba gaskiya ba dole ya kore komai ya tada mota yaci gaba da tafiya.
[4/22, 4:01 PM] Hauwa Galadima: *KURA A RUMBU*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 39*
Ko da ya koma gida daƙyar tunanin yanda Hajja zata karɓi zancen auren daya ɗaura ba tareda saninta ba ya danne waswasin da zuciyarsa ta dasa masa akan Zulaiha. Wayarsa ma kashewa ya sakeyi bayan daya shiga gida bai kuma kunnata ba sai washe gari gurin ƙarfe goma bayan daya shirya zuwa gidan Hajjan in da daga can kuma yake so ya biya gurin Halima. A tsakar gida ya tarar da Hajja tareda Fadila suna duba kayan da kallo ɗaya ya musu ya fahimci daga gurin Jalilah suka fito dan yanzu ta lalata Hajjan da suturu masu tsada. Yana shiga kuwa ta ɗago baki washe tana amsa masa sallama ta ce

"Kinga ɗan halak, yanzu muka gama zancenka ashe ma kana tafe". Kan kujerar tsuguno ya zauna yana gaisheta ta amsa cikin murna ta tura masa kayan tana cewa
"Ka ga abin arziƙin da yarinyar nan ta aiko da safen nan tayowa Fadila waya tace aje tasha a karɓo saƙo, ni har na rasa ma abinda zance gaskiya uwayen yarinyar nan sunyi sa'ar haihuwa kai dai Allah ya cigaba da haɓaka arziƙin kawai" ta ƙarasa tana ɗaga wani ɗanɗasheshen leshi da kana gani kasan an kashe kuɗi gurin siyan sa. Fadila ce ta fizge shi daga hannunta tana cewa

"Ni zan ɗinka wannan Hajja" sai ko ta maka mata harara tace
"Tunda ubanki ya bani ai sai ki ɗinki ko kuwa an rubuto sunanki a jiki? Ai na gaya miki na gaji da shuka dusa wlh, duk wata suturar arziƙi da ake kawowa ke kike ɗinkewa ki gama zaga garin ki dawo amma ko kare baze biyoki da sunan yana sonki ba" ta juya kan Bilal tace
"Kaima na rasa baƙin ciki ne ko menene ya saka nayi nayi ka tallatawa yaron nan Hafizu ita ai ba ƙi zaiyi ba amma ka ƙi, to wlh na fara gajiya da ganinki a gabana in sabon yaƙi samuwa sai ki nemo Sani ku sulhunta ki koma tunda dama ai ke kika ce sai ya sakeki ba wai son ransa bane".

Fadila ta miƙe tana zumɓuta baki ta wuce ɗaki tana cewa
"Allah ya rufa asiri ai ba jaka bace ni da zan maimaita aji". Shi dai Bilal bai ce komai ba Hajja taci gaba da ɗaga kayanta tana santi ta kimanta kuɗinsu, can ya nisa ya ce
"Hajja Kawu Sani ya zo kuwa?"

"Bai zo ba, ya dai kira ɗazu yace yau zai zo akwai maganar da yake so muyi. Ni dai na faɗa masa idan ma kuɗi zai roƙa babu dan dama nasan yanzu tunda akaga taurarinka sun fara haskawa Allah ya rufa mana asiri kuma za'ayo mana rubdugu to babu wannan maganar kuwa" ta bashi amsa. Sai ya shafa kansa ya ce

"Nasan ma ba zancen kuɗi bane ai kin san Kawu Sani bashida wannan halin"
"Lallai kai zaka gayamun halin Sani ashe, to idan ba maula zata kawo shi ba menene? Naga dai zancen tambayo aure ance sai nan da wata biyu to kuma me ze kawo shi?"

"Idan ya zo ɗin dai ai zakiji koma menene" ya bata amsa yana miƙewa, sai ta aje atamfar hannunta tana kallon sa tace
"To ko kasan dalilin zuwan nasa ne?" Da sauri ya girgiza kai ya ce

"Aa, kawai mun haɗu masallaci ne jiya yace mun yau zai zo nan gidan". Kuri ta masa da ido tana kallonsa kamar me son gano gaskiyar zancen sa kafin tace

"Da ganinka baka da gaskiya, to dan kaji da kunnenka idan ma zancen waccen yarinyar zaka turo shi ya mun kar ma ya ɓata lokacinsa dan zama kam kun gama gara ma ka bata takardarta tun da mutunchi".

Komawa yayi ya zauna yana fuskantar ta ya ce
"Amma Hajja wai mai yasa kike so sai ma rabu da Halima ne? Ni fa ba tayi mun komai ba hasalima ni na mata laifin da ya saka tayi fushi har ta tafi gidan sai kuma kawai in bita da tukuicin saki ai hakan ba adalci bane ba". Kamar bata ji shi ba ta shiga tattare kayanta tana mayar wa cikin leda, ya sake kwantar da murya yace

"To yanzu idan kika saka na saketa ya zanyi na zauna har wata biyu babu mata?"

Da sauri ta kalle shi kafin ta sauke kai tana sake tamke fuska tace
"Kai bana son iskanci da ɗiban albarka fa". Gyara zama yayi ganin kamar zai samu kanta ya ce

"Wlh ko yanzu da zan fito sai da maƙwafcina na jikin gidana ya tareni yana mun magana amma kinga ai ba zance mahaifiya ta bace tace kar na dawo da ita".
Chapter 92 · 0% Book details