← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 111 OF 158

Sashe 111

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 47*

"Ashe baka da mutunchi kai mutumin banza ne ban sani ba? Ban taɓa zaton haka kake ba, ashe abinda kake aikatawa kenan a bayan idon mu kana can kana zubar mana da mutunchi kana tozarta kanka; matan banza kake bi Bilal?"

Ya dafe in da ta mare shi ba tareda ya bari sun haɗa ido ba ya ce
"Ni wlh ba wasu mata da nake bi Hajja sharri kawai suka mun". Wani marin ta sake kai masa ya goce ta ce

"Yanzu kake da bakin kare kanka kenan? Ni zaka kalla ka ce sharri ake maka saboda ka raina ni mai ya sa a gabansa baka ce ƙaryar aka maka ba?

Karka ɗauke ni shashasha, ko da kaga a gabansu na kareka ina sane, na kuma san uban Halima ba zai maka ƙarya ba idan ma ƙaryar yake babu yanda za'a yi Aminu ya yarda da maganar nan ba tareda ya samu hujja ba dan ni na raba ku da su suna ƙaunar ku ba yanda za'ayi kuma a haɗa baki da shi ayi maka irin wannan ƙazafin" sai ta rushe da kuka tana cewa

"Ba yanda banyi akan ka auri yarinyar nan ba amma duk in na tayar da maganar sai ka kawo wani uzurin ka kauce alhalin ita burinta kenan kuyi aure yanzu da ace tun farko auren kukayi wane ɗan iska ne zai samu abun faɗa akanmu?

Amma yanzu ka lalata mana zuri'a ka kuma janyo mana abin gori a gari wannan wane irin tozarci ne? Tsabar lalacewa kuma har gidanka na aure kake kai macen banza ai dole Halima ta bar gidan baiwar Allah muna nan muna ɗaukar haƙƙin ta ashe ita kaɗai ta san baƙin cikin da take ƙunsa bayan gallazawa da azabtarwar da kake mata".

Yanda ta dage tana masa faɗa ba shi ba hatta Anty Amina ta sha mamaki domin ba zaka taɓa zaton Hajjan da take ɗaure masa ƙugu yana duk iyashegen daya ga dama bace wannan yanzu ta shiga tashin hankali har da kuka akan maganar da ta ji ba.

Shi dai Bilal kansa na sunkuye yana tsiyayar hawaye ya kasa sake cewa komai, Anty Amina ta kalli Hajja ta ce

"Duk wannan maganganun da kikeyi ihu ne bayan hari Hajja domin ke kika bashi ƙofa tun farko kika bashi goyon baya akan duk abinda yake aikatawa. Tun farkon ganina da yarinyar sai da na ce bata mun ba,

Zubin ta da wayewarta tafi ƙarfin kula namiji irinsa ga uban hidimar da take masa sai dai idan tana da wata manufa akan hakan. Amma me kika ce? Ɗan ki ya isa kowacce mace ta so shi ta kuma yi sha'awar aurensa, babu tunanin komai ke da shi kuka mayar da ita saniyar tatsa tayi ta kashe muku kuɗi, kin san ba shi da wani dalili na zuwa Abuja amma kullum yana hanyar can idan anyi ƙoƙarin nusar dake ki ce muma hassada zamu masa.

Ko sau ɗaya baki taɓa tunanin ita ɗin a ina take samun kuɗin da take bashi sannan aikin me yake mata da zata ringa masa irin wannan wadaƙar kamar a bishiya take tsinko kuɗin.

Na sha miki magana Hajja, babu inda son zuciya zai kaiki ƙarshe sai dai ya janyo miki ɓacin rai amma baki ji ba tun akan Hafiz, yanda kika ringa biye masa kina zubar da girman ki kuna roƙon yaron nan har sai da kuka ƙure shi ya janye jikinsa sannan ya sake kamo muku wani kifin kuka juya kanta. Ki godewa Allah ma da ya zama ƙwadayin nasa iya bin mata ya kai shi ba maza ba da..."

"A'uzubillahi wace irin magana ce wannan mara daɗi Amina? In sha Allahu ba zanga wannan baƙin cikin a zuri'ata ba" Hajja ta katseta. Anty Amina ta taɓe baki ta ce

"Ƙwadayi da son duniya su suke kai mutane ga halaka sai daga baya su zo suna dana sani mara amfani, yanzu dai ƙwai ya fasu kowa ya ji warin, Halima kuma da a kullum baku da abin zagi da aibatawa sai ita kinga irin abinda ta shanye ta rufawa ɗanki asiri.

Ita kuma wacce kike haƙilon ya auro mikin ku cigaba da shan romo anyi walƙiya yanzu kun san wacece ita. Kuma na san harda haƙƙin Halima da ya fara bibiyarku, Fatana ɗaya ubangiji ya rufa maka asiri ya sa ita wacce ka wulaƙanta uwargidanka akanta ka kashe duk kuɗin haram ɗin da ka samu akanta da iyayenta karta zame maka kara da kiyashi dan wlh jiki na bai bani kayi dacen mace ba" ta ƙarasa tana miƙewa tsaye da alama ta gama abinda ya kawota.

Daga Hajja har Bilal ɗin kallonta kawai suka ringayi har ta nufi ƙofa kafin ta tsaya ta waiga ta kalle shi ta ce
"Karka ɓatawa kanka lokaci kace zaka koma ka bawa Halima haƙuri ko iyayenta domin ba zasu saurareka ba. Ka kuma fi kowa sanin mahaifinta kaifi ɗaya ne, yanda ya toshe kunnensa a sanda kowa yake faɗin baka dace da yarsa ba ya ɗauke ta ya baka haka a yanzu da ya buƙaci ka sakar masa ita bana zaton ko duniya zata taru akansa akwai wanda zai saka ya haƙura ya barka da ita. Yanda ya ce ka kai masa takardar sakinta salin alin kayi idan kuma ka shirya tonuqar asirinka wa duniya baki ɗaya ne toh kayi gardama" daga haka ta buɗe ƙofar ta fita ta barsu.

Hajja ta kalle shi ta ce
"Ko me za'ayi karka kuskura ka saketa kaji na gaya maka". Sai ya ɗaga kai da sauri ya kalleta, sai kace ba Hajjan da bata da wani buri illah na ta rabashi da Haliman ba amma kuma bai san dalilin ta na canza ra'ayi a yanzun ba dan haka ya ce

"Amma me yasa kika ce haka Hajja bayan baki da wani buri illah na ganin na rabu da Halima a yanzu?"

"Ko a da ina so ku rabu yanzu na canza shawara. Ba zaka saketa ba, saboda idan suka samu abinda suke so zasu tona maka asiri ne su watsa labarin a duniya, idan kuwa kuna tare dole su yi shiru domin sirrinka sirrin yar su ne idan kuma suka fitar ba iya kai kaɗai zasu zubarwa da mutunchi ba" Hajjan ta faɗa. Ya buɗe baki da niyyar magana dai dai lokacin Abubakar ya shigo daga tsayen da yake ya ce

"Tamkar ba ke kika gama kuka yanzu kina masa faɗa ba Hajja. Wai menene jin daɗin ki akan rayuwar ƙunci da baƙin cikin da Halima takeyi a gidan sa? Me yarinyar nan ta tsare miki?"

"Ai duk ita ce sila, idan da ya samu abinda yake buri daya aureta a ina zai je ya haɗu da wannan tsinanniyar yarinyar harta koya masa abinda ba halinsa ba? Dan haka yanda ta zama silar ɓacin sunan sa haka zasu zauna tare su kwashi baƙin ciki ba ta isa ta rabu da shi ba wlh" Hajjan ta bashi amsa sai Abubakar ya watsa hannu irin ko oho ɗin nan ya ce

"Ai kuwa sai ku shirya kwasar baƙin ciki ke da shi domin ko yaƙi Allah sai ya sakar musu yar su, kuma tun yanzu ku fara tattara duk abinda kuka san kunci na waccen matar dan wlh ba zata barka ba, kada ka ɗauka ka fita wayo, ka yaudareta kayi aure sannan ka salwantar mata da dukiya kaci banza na san kallonka kawai take kuma zata yi lokacinka nan ba da daɗewa ba".

Sai da cikin Bilal ya juya ya zurawa Abubakar ido zuciyarsa na bugawa fat fat kamar zata huda ƙirjinsa ta fito. Yanda Abubakar ɗin yake magana kamar yana da masaniya akan gidan Jalilah daya siyar da shagon ta da yake shirin siyarwa a yanzu.

Ya sadda kai ƙasa yana jin Hajja na cewa
"Idan ta fasa yin lokacinsa bata ƙaunar iyayenta, roƙon ta yayi ko me? Dan Allah karta fasa ta kuskura ta zo nan ta ce zata yi mana wani hauka taga yanda akeyi shegiya karuwa mai lalata yaran mutane" ta cigaba da sababi.

Abubakar dai fita yayi ya basu guri Bilal ɗin ma jiki a mace kamar wanda ya sakko daga iskokai ya miƙe da niyyar barin falon. Hajja ta ce
"Ka dai ji abinda na gaya maka ko kotun ƙoli zasu kaika kada ka kuskura ka saki Halima, sannan itama waccen ta tare a satin nan dan karma tsautsayi ya saka magana ta fita su ce wani abu dan wlh basu isa ka gama wahalta musu wani abu ya gifta su ce za'a warware auren nan ba ko zaka saketa sai mun fanshe wahalar da ka musu sun maido maka da komai tukunna".

Shi dai ya fita mamakin Hajja na neman kashe shi. Sai kace wahainiya. Kwantar da sit yayi bayan da ya shiga mota ya kwanta haɗi da rufe idonsa yana jin ina ma yana da damar maido da lokaci?

Ya daɗe yana hasashen irin wannan lokacin na tonuwar asirinsa sai dai bai taɓa zaton zai riske shi ba saboda yanda yakeyin komai a tsare, a nasa wayon kuma ya zata zai iya yin komai har ya gama cikin sirri ba tareda wani ya san mai ya aikata a rayuwarsa ba.

Halima ce ta fara kawo masa cikas, da ace bata duba wayarsa a waccen ranar ba da duk haka bata faru ba amma ko da akayi hakan bai taɓa zaton cewa zata iya tona masa asiri ba.

Zuciyarsa ce ta raya masa
"Idan kai ne ka ganta a irin yanayin data kamaka jiya zaka iya cigaba da rufa mata asiri?"
Chapter 111 · 0% Book details