← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 158

Sashe 62

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A can gida kuwa da kuka wurjanjan Baba Jummai t shiga bayan mai adaidaita sahu ya sauke ta. Amirah na alwala a bakin famfo tayi maza maza ta ƙarasa kafin ta nufi Baba Jumman tana tambayar ta me ya faru?
"Kada ki ga irin tijara da wulaƙancin da yar uwar ki ta mun saboda na tsaya mata a gaban sirikar ta da ta tasa ta gaba ta na zagin iyayen ku shi ne ta kore ni wai zan kashe mata aure" Baba Jumman ta faɗa tana sake rushewa da kuka. Bakin Amirah har kunne ta karɓi jakar Baba Jumman ta na cewa
"Mu je, kin kuwa ci sa'a Abba ya na nan" ta wuce falon Abba Baba Jummai ta bi ta. Tiryan tiryan tun daga zuwan ta gidan da abubuwan da ta gani da wanda ta ji har zuwa yau ɗin da rashin kunyar da Haliman ta yi mata duk babu wanda ta manta bata zayyanawa Abba da Mama da ke sauraron ta ba.

Amirah ta ce
"Alhamdulillah, sanda na faɗa ta ce ƙarya na ke yi yanzu ai ba ta gurin balle ta dake ƙarya ta wa. Ai wlh dama ni na san tun da aka yi na farko ya ga an masa shiru..."

"Baki da hankali ko Amirah? Wa ya kira ki gurin nan ma da farko balle har ki buɗe baki waaa kina magana se kace kin ga sa'an ki a nan? Wu ce kafin na kwaɗa miki mari a gurin" Mama ta katse ta cikin tsawa, baki ta tura ta tashi tana waigen su. Ita da ta so ta sake ƙarawa abun gishiri ta yanda Abba ze fusata kawai ya kashe wannan ƙaddararren auren na Halima kowa ma ya huta amma Mama ta kora ta waje.

Bayan fitar Amirah Abba ya dubi Baba Jummai da ke aikin goge hawaye ya ce
"Kiyi haƙuri Hajiya Halima ba ta kyauta ba kuma se na saɓa mata akan hakan ki je cikin gida nagode". Kallon Mama ta yi Maman ta gyaɗa mata kai alamar ta yi abin da Abban ya ce dan haka ta miƙe ta fita. Ta ɗauka a yanda ta zayyana musu abin da yake faruwa da Haliman za su birkice ne take su kira waya su ce ta taho ko kuma ma takanas a tashi wani ya je ya taho da ita amma saɓanin haka sai ta ga kowannen su kamar ma basu kama abubuwan da ta faɗa ba ko dai ma sun ɗauka ƙarya kawai ta shirga musu ne shi yasa Abban ya ce ta tafi cikin gida.

Haushin kan ta ne ya kamata, ita da ta san da Haliman da iyayenna ta duk jirgi ɗaya ya kwaso su ba wani damuwa suka yi dan an ci zarafin su ba ina zata haƙiƙan ce ta tare musu faɗa? Bata shiga cikin gidan ba kamar yanda ya ce mata ta ɗauki Jakarta da Amirah ta aje mata a tsakar gida ta yi tafiyar ta, gara ta je ta faɗawa uwar ɗakin ta ta yuwu ita ta fisu kan gado ta kuma fi su hangen matsalar da Haliman ta ke ciki tunda taga su abun be wani shalle su ba.

Bayan fitar Baba Jumman Mama ta sauke ajiyar zuciya ta ce
"Gaskiya na gaji da lamarin auren nan na Halima, zan ɗauki komai amma ban da wulaƙanci da kuma tozartawa. Idan wancan karon Amirah ce ta faɗa ta ƙaryata ta yanzu ai Baba Jummai ba zata mata ƙarya ba to gaskiya ba za'a yi na uku da ni ba babu dole a ciki, su da suke da abun zagi ba'a zage su ba banga dalilin da mu zasu ringa zagin mu ba" ta ƙarasa tana huci. Murmushi Abba da ke kallon ta ya yi ya ce

"Yanzu me kike so a yi Amina?"
"Gida zata taho tun da ba daina son ta muka yi ba da zamu bar musu ita suna gallaza mata, shi ya mata yan uwan sa su mata uwar sa ta yi abun ya yi yawa ai ba zan ɗauka ba" ta bashi amsa a fusa ce tana laluben lambar Halima a wayar ta. Gyara zama Abban ya yi ya ce

"Amma yanzu da kunnen ki kika ji ta ce shi Bilal ɗin ya ce ta taho gida, kin ha ta taho ɗin? Hakan ya nuna miki tana son zama da Mijin ta a kowanne yana yi. Ni ba goyon bayan Halima nake yi ba ban kuma ƙarya ta abin da Amirah ko Jummai suka faɗa ba amma ki sani ba zan taɓa yankewa Halima hukunci akan abin da ya shafi rayuwar ta da shaidar wasu ba. Ita take zaman aure, da daɗi babu ta zaɓi haka ba kuma ta taɓa zuwa ta ce ya mata wani abu ba dan haka na sakawa raina tana zaune lafiya da Mijin ta.
Son da take masa ya saka na amince na aura masa ita kuma duk ranar da ta nuna bata da ra'ayin ci gaba da zama da shi zan wuce mata gaba na rabata da shi"

"Yanzu dai me kake nufi Abba?" Mama ta faɗa tana kallon sa, sai ya miƙe tsaye ya ce
"Ki cire idon ki da kuma kunnuwan ki akan abin da wani ko wata yake kawo miki akan Halima. Har idan ba ita ta zo ta faɗa mun matsala ba, a guri na lafiya lau ta ke zaune dan haka babu wata magana da zan saurara" yana gama faɗar haka ya shige ɗakin sa.

"To ke me ye naki a ciki Mama? Ai kamar yanda Abban ya faɗa ne, tun da dai ita bata ga aibun abin da ake mata ba ko ta kawo ƙorafi ba kin ga ai lafiya lau ne a gurin ta, sai ki bar ta ki ci gaba da yi mata addu'a kawai tun da haka ta zaɓawa kanta. Dan Allah yan da ya bar maganar ke ma ki shafe ta kamar bata faru ba. Idan da ta ji zafin abin da aka mata kafin ma ace ta tafi zata yankewa kanta hukunci amma an ce ta tafin ma taga guri ta zauna se mu cigaba da bin ta da addu'a Allah ya shiga lamarin ya kawo rangwame" amsar da Anty Labiba ta bawa Maman kenan bayan da ta kira ta ta na mata ƙorafin yanda Abba ya bagarar da maganar da Baba Jummai ta kawo akan Halima.

****************
Farar shinkafa na dafa tun da akwai sauran stew, sai da na gama jere abincin a dining kafin na tuna da ban yi wankan yamma ba shima Al'amin ba'a masa ba. Ganin Bilal be dawo ba har na gama se na fita na shiga kiciniyar hura wutar dan ma ita cen busasshe ne kuma garin akwai iska, ruwan ma kaɗan na saka dan ya yi saurin tafasa na koma ciki na zuba abinci na ci dan yunwa nake ji sosai, sai biyar da rabi sannan Bilal ya dawo lokacin har ruwa na ya tafa sa dan haka na kwantar masa da Al'amin na yi shirin wanka na fita. A bokiti na ringa ɗiba ina juyewa a babban bahon da ke cikin banɗakin tsakar gidan, wani ruwan da zan zuba a flask da na wankan Al'amin na ƙara sannan na shiga wankan a raina ina mitar Baba Jummai da take cewa zan ga idan tana da amfani a guri na ko kuma ba ta da shi yanzu da ta tafin menene ban yi ba? Girki ko kula da Al'amin ɗin ko kuma saka ruwan wankan? Wankan ma gashi zan yi da kaina dama ai na mugunta ta ke yi mun ta yi jibga mun ganye idan nayi magana ta balbale ni dama masifa wai so na ke ta ringa mun jiƙa jiƙa na lalace ace ita ta cuce ni.

Ina wannan mitar a raina na ciro ganyen da na bari a ruwa ya juƙu gashi da ma ya yi laushi da safe da muka yi wankan na ji ta na cewa se an ɗebo sabo da yamma, ba tare da na ko girgije shi ba na yi bismillah na lafta a gadon baya na. Lokaci ɗaya na fasa ihu saboda wani azababben zafi ya ziyar ci fatata take baya na ya ɗauki raɗaɗi na jefar da ganyen a gefe na shiga tsalle ina shafo guraren da nake jin zafin a jikin fata ta. Bilal dake zaune falo yana wa Al'amin wasa jin ihu na ya fito da gudu dai dai nan kuma aka buga gidan. Banɗakin ya shigo yana tambayar lafiya ba bakin magana sai kawai na fashe da kuka ina nuna masa bayana yanda ya rafka salati bayan da ya duba bayan ya sa na sake fashewa da wani kukan ya ce

"Gurin ya yi jaa, ƙonewa kika yi?"
Zani na na ja na ɗaura kawai na fito ina cigaba da kuka shi kuma ya tafi ya buɗe ƙofa da ake ta bugawa. Hajiya Inna ce Surukar Maman Yusuf, ina durƙusa gaban kujera ina kuka dan sosai baya na yake mun raɗaɗi suka shigo falon tare, wai ashe idan an kwashe ruwan ya kamata na bari ya ɗan sarara kuma se an girgije ganye kafin a fara bugawa tana ganin ganyen kuma ta ce ai dole na ƙone saboda ganye ya gama dafewa. Daga ƙarshe da towel ta mun wankan ni dai har dare baya na be dai na mun raɗaɗi ba.

Ni na ce mata ba se an yiwa Al'amin wanka ba saboda yanayin garin akwai sanyi sanyi dama ba'a son raina ake masa wanka biyun ba se mura ta zo ta kama shi a barni da wahala, da zamu kwanta na goge masa jiki na saka masa kayan bacci kawai. Tsabar yanda yan ayyukan da na yi suka gajiyar da ni dan na kwana biyu ban ba ina kwanciya bacci ya kwashe ni. Cikin dare azababben kukan da Al'amin ya ke ya farkar da ni, na buɗe ido daƙyar ina kallon Bilal dake duƙe kai na ya na tashi na, daƙyar na yunƙura na zauna ido na ko buɗuwa da kyau ba sa yi ya miƙo mun Al'amin ɗin ya na cewa
Chapter 62 · 0% Book details