Sashe 21
Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Murna fal zuciyata, se da na wana shi iya yanda naji ya mun kafin cikin shagwaɓa nace na haƙura.
"Nagode Halims kuma alƙawari, ba dai akwatin lefe bane? To ki biyo ni bashi in sha Allahu zan biyaki da dozen ma ran da kika haifar mun Bilal junior ko little Halims" se na rufe ido na cikin kunya jin Nasir na cewa
"Daga gobe ne ai zamu fara irgen lokaci" ganin zasu fara shaƙiyancin yasa Hansa'u da takaici ya hanata cewa komai tun tsaiwar mu tace dare yayi mu shiga gida. Haka muka raba dare muna waya da Bilal yana faɗa mun irin murnar da yake ciki da yanda ya tsara goben mu zata kasan ce. Na ringa juyi a gado ina jin kamar goben tayi mun nisa.
Washe gari aka tashi da shirin ɗaurin aure, yini da kai amarya duka a ranar za'ayi. Da wuri muka koma gidan su Hansa'u ni da ƙawaye na da muka kwana tare har sanda muka fita kuma ledojin lefe ma na zube a falo na dai ji Goggo Habi na cewa Anty Labiba a kwashe waɗannan kayan tsiyar kafin mutane su fara shigowa a samu na yayatawa a gari. Sanarwar ɗauruwar aure a tsakanina da Bilal yana cikin abubuwa ma fiya daɗi da kunnuwa na suka taɓa sauraro tsayin rayuwa ta. Tsabar farin ciki bayan da nayi sujudushshukur se kawai na zauna na fashe da kukan murna. Ƙarfe biyar muka tafi Galadanci in da aka haɗa mu da sauran cousins ɗina biyu iyayenmu maza suka mana nasiha daga can kuma bayan magriba aka ɗauki kowa zuwa gidan mijinta.
Kwata kwata na kasa yarda wai yau nice na zama matar Bilal? Da su Anty Labiba zasu tafi ta riƙe hannu na tana cewa
"Buri ya cika kin zama matar Bilal Halima, se kiyi haƙuri domin yanzu wata rayuwa ta daban zaku shiga ba wacce kuka saba da ita a waje ba. Yanzu ne za kuyi zaman gaskiya da gskiya halin kowa ya fito, zaki iya tarar da Bilal a yanda kika tsammaci samun sa koma fiye da haka ki na kuma iya tarar da akasin hasashen ki ma'ana yazo miki da wasu halaye na daban da basu kika sani a tare dashi ba. Fatan mu yanda kika masa halacci ya maida miki, kiyi haƙuri da duk abin da zaki ji ko ki gani duk wani gidan aure da kike gani da kalar ƙalubalen sa haƙurin da ma'aurata suke yi shi yake lulluɓe komai kiga tamkar ba'a saɓawa. Mace ita take mayar da gidan ta dausayi ko ta mayar dashi filin yaƙi. Yanda kika ɗora mijin ki haka ze miƙe. Idan kin tafi dashi ta laluma zakiji daɗin sa in kika koya masa hargagi da masifa har tsufa hara ze ringa miki dan haka ki koyi ta yanda zaki ringa bayyana fushi idan ranki ya ɓaci. Ina miki nasiha da kiyi koyi da halin Mama, na tabba har kike riƙi halayanta na gari badai a kawo ƙarar ki ba. Ina sake maimaita miki da kiyi haƙuri Halima, kiyi haƙuri kiyi haƙuri ki ƙara da haƙuri Sadiyayye. Yanzu ba zaki gane haƙurin me nake nanata miki ba. Allah ya albarkaci rayuwar auren ki, Allah ya mallaka miki Bilal ya hane shi da yi miki butulci irin na maza" se ta fashe da kuka muka rungume juna daƙyar aka raba mu suka tafi ya rage saura ni da ƙawaye na.
Dubu hamsin abokanan Bilal suka bada kuɗin siyan baki ga ruwa da lemo katan katan da kayan shayi, a cikin kuɗin Hansa'u ta cire dubu goma ta saka mun a jakata, itama se da muka sha kuka kafin muka rabu ya rage daga ni se Habibi na cikin gidan mu. Faɗar irin tarairayar dana samu a gurin Bilal ɓata baki ne, tamkar ƙwai haka ya ringa riritani yana shayar dani madarar soyayya har ya samu nasarar maida ni cikakkiyar mace jikin mu ya ƙara sa zama abu ɗaya kamar yanda zukatan mu suka daɗe a tare. Washe gari haka ya wuni tare dani duk da yan uwanmu da suka fara zuwa tun safe da nashi dangin be fita ba se da yamma tayi aka zo kawo gara sannan ya fita ana idar da sallar isha'i kuwa ya dawo.
Haka rayuwa ta fara miƙawa, tsakanina da Bilal a kullum so da shaƙuwar mu ƙara karfi yakeyi. A sati guda da auren mu ina jin da ace wani kuskure ya gifta har ya zamana ban auri Bilal ba da bazan taɓa yafewa kaina ba. Bilal ƙarshe ne gurin iya tattalin mace, ya iya soyayya. Irin soyayyar nan me tsayawa a rai da kake wuni cikin shauƙi da tunani ita Bilal yake gwada mun. Se da muka kwashi sati biyu ban da sallah babu abin da yake fitar dashi daga gida tun da komai muna dashi babu ce kaɗai ba'a sako mun a cikin garata ba har da soyayyen nama da dafaffen kayan miya da ɗanye se dai idan zan yi girki kawai na ɗiba. Baƙi yan ganin ɗaki ma sun haƙura saboda yanda baya kunyar idon kowa haka ze zauna a cikin su ko kuma ya riƙe ni a ɗaki se dai su gaji da jira su tafi. Dake dama dangin sa ne masu zaryar ni nawa tun da aka kawo gara babu wanda ya sake zuwa se ranar dana yi kwana biyar ne Gwaggo Habi tazo mun sallama zata koma Birnin gwari.
Ranar da muka yi sati biyu tun safe ya ce mun zamu fita. Na ringa murna dan ji nake kamar na shekara a guri ɗaya, na ɗauka ma da wuri zamu fitan dan haka kafin azahar na gama girki na shirya se yace mun se da yamma. Tsaf muka shirya, tsakanin ni dashi se ka rasa tantance wanda auren yafi karɓa. Munyi kyau jikin mu ya murje muna ta ƙyallin amarci abun mu. Muna tsaye a bakin titi muna jiran abin hawa ya kalle ni yana murmushi yace
"Kin ga da ace Abba ya sako miki mota a kayan gara hankali kwance zamu fita muna yangar mu a titi".
Murmushi kawai nayi ba tare da nace masa komai ba, gidansu muka fara zuwa tamkar zasu cinye ni saboda ƙauna. A can mukayi sallar Magriba kafin muka wuce gidan mu Hajja nata mu tsaya mu ci tuwon dare yaƙi, a cikin dubu goman da Hansa'u ta cire mun na bata dubu biyar ta ringa murna kuwa. Har goma muna gidan mu saboda Abba be dawo da wuri ba. Na lura da yanda Mama take ta bi na da kallo kamar na canza mata, se da muka shiga ɗaki take tambaya ta komai lafiya dai nace mata ƙalau.
"Haka ake so aji, Allah ya baku zaman lafiya ya kaɗe fitina. Da go be su Imam suke cewa zasu zo amma tun da kun zo yau se su bari se wani sati" na mairairaice nace
"Haba Mama zuwan mu daban nasu daban ai, dama goben ya ce zeje wani ɗaurin aure jigawa nasan kuma zeyi yamma kinga sa tayani hira". Da zamu tafi Mama ta haɗa mun su kuka daddawa da kuɓewa wanda dama tace se daga baya za'a kawo harda dambun nama da kilishi. Abba ne ya ce Mu'azzam ya kaimu tun da dare yayi, naso ace mun biya gidan Anty Labiba amma tun kafin mu fita daga gida da na yiwa Bilal maganar cewa yayi ba yau ba, da muka fito kuma dare yayi shiyasa kawai na haƙura se wani lokacin. Da yake mun ci abinci wanka kawai mukayi muka kwanta rungume da juna kamar ko yaushe.
Washe gari da wuri ya shirya saboda ɗaurin abokinsa da yace tare sukayi karatun university. Khalil na da kirki sosai, tun daga Maiduguri ya zo mun biki kin ga ai ba naƙi zuwar masa ba nan dai da Jigawa" ya faɗa. Ina gyara masa zaman hularsa nace
"Ai kam dai ka kyauta, ba dan yanda kake ta nanata amincin ki dashi ba bazan yar da ka tafi wani guri yini guda ba tare da ni ba". Se da yaja hanci na ni kuma na shagwaɓe fuska kamar zanyi kuka se ya rungumeni yana cewa
"You have no idea on how much I'm going to miss you sugar, na faɗa miki kawai dan Khalil ne badan haka ba yau Sunday dai ɗaurin aure ko a ciki garin Kano ne se dai a mun haƙuri". Nema mukayi mu lalace a tsaye da soyayya se da wanda zasu tafi ya kira shi kafin ya sake ni duk ya kashe mun ya saka mun shauƙin son kasancewa tare dashi.
Se da na raka shi get ina masa addu'oi kafin na koma cikin gida, minti uku tsakani wayata ta shiga ƙara na amsa ganin shine yace
"Babe kin san guy ɗin nan wai motar sa babu mai se yanzu yake faɗa mun?" Nace
"Toh, Allah ma ya sa kun sani da wuri ai ba se da kuka hau hanya in da babu gidan man ba".
"Haka ne, amma yayi yawa ai, me yasa tun tuni be faɗa ba kawai yace mana za'a tafi a motar sa? Ai se yace dama zamu haɗa kuɗin mai kinga da se musan da lissafin sa" Ya sake faɗa. Se nayi murmushi nace
"To yanzu dear kwata kwata nawa ne zeyi muku full tank da kake wannan mitar, ka bad kuɗin a saka man ku tafi mana kaga fa lolaci yana ta ja kar ku makara kuma"
Ƙaramin tsaki yayi kafin yace
"Ni fa 2k kawai na fita da ita shima saboda ba'a son tafiya babu kuɗi. Kuma ATM ɗina jiya na manta shi hannun Abubakar dana bashi ya ciro kuɗi, amma bari mu dawo na gani na san bazan rasa yan canji dana bari a gida ba" daga nan ya kashe wayar. Tunanin kar su sake ɓata lokaci yasa kawai na cire dubu biyar cikin kuɗin da Abba ya bani jiya na riƙe a hannu na, ina jin tsayuwar mota na yafa mayafi na na fita muka ci karo a bakin get na miƙa mishi ina murmushi se ya karɓa tare da pecking goshi na ya juya yana ɗaga mun hannu.