← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 158

Sashe 121

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai dare Anty Labiban ta dawo da akwatunan kayana harda uniform ɗin NYSC na nan take labarta mun sunje sun kwashe kaya.
Har shara da mopping mukayi, duk albarka da arziƙin da kika je da shi gidan mun kwashe abin mu. Ni wlh badan Yaya Fauziyya ta hana ba so nayi a nemo yan gwangwan muyi musi gwanjon ƙofofi da windunan gidan tunda da kuɗin Abba aka siya amma tace wai ba haka ba. Haka kitchen cabinets ɗin nan nayi takaici Allah bana jin ma zan haƙura sai na koma an ɓalle su"
ta faɗa sai ta bani dariya ma.

A hankali na fara sakawa kaina dangana na shiga Iddah, dama kuma washe garin da akayi sakin da yamma sai ga period wanda na tabbatar damuwa ce ta matso mun da shi domin akwai sauran lokacin zuwansa. Anty Labiba ta ringa cewa
"Ai gara kiyi ki gama tun kafin ɗan akuyar ya ce zai waiwayoki dukda ko da uwarsa yake tafe bai isa ya ce zai maidake kafin ki gama iddah ba wlh Mu'azzam zan saka ya sake tare shi a hanya ya masa dukan tashi kasha gishiri ya ƙarasa miki ɗayan kawai a huta" ni dai jin ta kawai nake ina murmushi, wani nishaɗi naga tanayi, ba ita ba, har Mama da mukayi waya jin muryarta nayi a washe ba kamar lokutan baya ba tana ta ce mun

"Babu komai ki kwantar da hankalinki komai kika ga ya faru a rayuwa da sanin Allah addu'ar da muke yi muku kuma a kullum in sha Allahu ba zata faɗi a banza ba kada ki wani saka danuwa a ranki".
Allah sarki ni, ana baƙin ciki da mutuwar aure amma nawa kowa aka faɗawa sai dai yayi hamdala haɗi da yi mun barka, ɗaya daga cikin fargabata na kar ayi mun dariya ta kau domin dai da alama tausayi na ma ake ji a maimakon kuma a zageni yanda nayi tunani sai barka ake mun kamar wacce ta fito daga hannun kidnappers.

Hankali na ya sake kwanciya ganin har sati ya ƙare Bilal bai sake turo mun da wani saƙo ba sannan babu wanda ya zo ko yayi waya daga ɓangarensa akan yara, dama fargabata ta biyu kenan ace za'a rabani da su sai dai na samu nutsuwa dan Abba da kansa da na ce masa Anty Labiba ta ce za'a mayar masa da su Al'amin ya ce Aa in kwantar da hankalina wasa take babu wanda ya isa ya rabani da yarana.

BILAL

Allah Allah ya ringayi Asabar tayi Zulaiha ta tare ko zai huta da masifar mita da bani banin da suka tasashi gaba, shi gaba ɗaya ma ya kasa ganewa al'amarin, naira miliyan uku ya bata kuɗin lefe da hidimar biki amma daga kan kayan gadon da suka ɗora masa zuwa sauran abubuwan da ta sake bijiro masa da su sai da ya sake kashe wata miliyan ukun harda ɗori akai.
[5/15, 8:13 AM] Zainab Madawaki Dahiru: *KURA A RUMBU*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*7061838488*
*Opay*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 51*

Ranar Alhamis suka je jere ko ya ce ganin gida tunda dai shi yayi jere, yan buhun hunan da suka je da abinda suka kira kayan kitchen tsabar takaici kallo ɗaya ya musu ko gaisuwa mai kyau basuyi ba ya fita ya barsu da yayyensa banda Anty Amina da sukaje tarar masu jere. Bai san munafukin daya gayawa Hajja shi ya siya mata kayan ɗaki ba ai kuwa ya sha tijara wannan kuma ya sake ruguza ɗan shirin da suka farayi ta kuma ja masa kunne akan ba fa zata saɓu ba, ita da wahalar haihuwa da raino can wasu a gefe da cin moriyar arziƙin sa dan haka daga wannan idan ya kuskura ta sake jin magana makamanciyar wannan tabbas za'a ji su a rana.

Kayan kitchen dai tarkace suka jera yanda ka san a ƙauye, shi rabon da yaga Risho wlh ya manta amma sai gashi wai shi aka kawowa Zulaihan. Tunani ya ringayi a ransa a ina ma za'a samu kalanzil dan bashida tabbacin har yanzu ana siyarwa. Yanzu banda tsiya ina laifi ko camping gas ne ko 1kg su siya mata kai shi wlh gara ma a haɗota da murhun kurfoti ya fi wannan Risho ɗin da suka kawo masa gida.

Ta ce masa suna da labule dan ita ta faɗa masa kalar labulen ma da zai zaɓi kujeru ta kuma ce akwai carpet, fridge, Tv harma da gas ɗin amma bai ga ko ɗaya ba haka yan jere suka zo ziƙau daga su sai tagayyararrun kayan kitchen ɗin su.

A haka kuma bayan sun koma ta kira shi murya ba walwala tana masa ƙorafi wai an ce mata gidansa na Goron dutse zata zauna.
"Kai da ka ce mun a Rijiyar zaki gida na ya ke ya akayi kuma yanzu akace in da Maman Al'amin take zan zauna?" Ta faɗa, a sama yake dan gaskiya lamarin jeren nasu ya ɓata masa rai yanda baiyi tsammani ba. Duk miliyoyin daya kashe mata ace wannan abun za'a kawo masa tsabar rainin wayau?

Abinda ya ringa sake hasalashi yanda zuciyarsa ke ta hasko masa zamanin Halima, sai da akayi sati ana mata jere idan ya shiga gidan a lokacin har baya son ya fita ga yanda Abokanansa suka ringa kambama abun yana masa daɗi gidansa kamar gidan wani sarki amma yanzu ko gado da kujerar daya siya da kansa a can gurin ya gansu masu kyau amma da aka kawo aka zuba sai ya gansu kamar bola, kujerun sukayi wani yan tsurut a falon ba kwarjini irin na kujerun Halima haka ɗakin ji yayi ransa ya baci daya kalli kayan sai ma ya gansu kamar tsofaffi toh ya saba ganin Made in Turkey a ɗakin, katako da gilasai suna dalle masa ido da hasken su.

Kitchen ɗin kansa da yake shiga yayi ta ɓuruntu ga utensils kala kala yanzu sai tsalli tsallin multi colored kwanuka da rabinsu na roba ne.

"Eh na canza shawara a nan ɗin zaki zauna" ya bata amsa. Ta ce
"Lallai, a gida ɗaya zaka haɗa mu? Gaskiya ba zai yuwu ba tun wuri ma ka sake shawara dan ba haka mukayi da kai ba tun farko".

Kamar ya ce mata
"Ke kika sani" amma gudun ɓacin ranta da yakeyi dukda haushinta da ya cikashi haka ya kanne ya ce

"Wa ya ce miki gida ɗaya zaku zauna?"

Acan ɓangaren Zulaiha da tana sane da cewa Haliman bata gidan kawai so takeyi taji gargar ɗin maganar ta ce

"Gashi kuwa an ce a gidanta aka mun jere"

Wai aka mata jere, tsaki yayi ya ce
"Kuma suka ce miki tana gidan ko sunga kayanta a ciki?"

"Ni ban tambaye su ba wannan, kuma sun ce wai gado ɗaya aka saka kuma ɗaki biyu ne kuma ba'a saka labulaye ba" ta sake soko wata maganar. A hasale ya ce

"Kina ji Zulaiha, nayi iya yina abinda yake haƙƙina da ba nawa ba duk na haɗa na miki. Daga yanda suka ga gidan duk abinda babu ko bai muku ba wlh sai dai kuyi da kanku amma tsinke ba zan sake siya in saka ba".

Muryar Ummansu ya ji daga gefe tana salati kafin ta rufeta da faɗan da bama gane mai take cew yake ba dan haka ya katse wayar sannan ya kasheta gaba ɗaya. Duk Halima ce ta janyo masa, idan da bata kwashe kaya ba ai da bata tona masa asirin gida ba, gurin da yake jin sa kamar Villah, baya shakkar kawo ko wanne irin baƙo, su Hafiz da Jalilah da suka juƙu da naira suke kuma shiga gidaje na alfarma sai da suka yaba kyau da tsarin jeren Halima amma yanzu gida ya koma kamar wani sansanin yan hijira a idonsa. Yayi tsaki a fili ya furta

"Wlh sai kin gane kurenki, sai kin san kin ɓata mun rai".

Rana bata ƙarya aka ce sai dai uwar ɗiya taji kunya in ji hausawa, haka ne kuwa domin Asabar ɗin da ake ta kira ta zo a ranar kuma yan uwansa suka ɗan yi yini a gidan Hajja itama amarya a can gidansu ranar sukayi yinin wanda dukda rantsuwar da yayi akan ba zai sake kashe mata ko sisi ba sai da ya karya ya kai musu buhun shinkafa dan kusan azahar sukaje zai nunawa Abokinsa Alhaji Sani da zasu je ɗakko amarya gidan ya tarar da mata har ƙofar gida suna ta zuba hamma ga yara nata koke koken yunwa wata nata bala'i an san ba'a da abinda za'a girka akan me aka kai musu goron gayyata su ba'a barsu sun dafa a gidajensu sun ci ba an kawo su nan ana musu izaya da yunwa.

Kunya da takaici suka sake turnuƙeshi amma haka ya koma bayan ya sauke Alhaji Sani da ya kasa shiru ya ce
"Kai kuwa Bilal wane rufa ido aka maka kaje irin gidan nan neman aure? Ka san fa akwai banbanci tsakanin Talauci da kuma Tsiya, to kai dai da alama gidan matsiyata kayo aure wlh da matarka ta rufin asiri yar manyan mutane haka kawai ka jajibowa kanka abinda zai dameka".

Shiru ya masa zuciyarsa na kumbura da fushi har suka rabu tsabar rainin wayau daya sauke shi sai ce masa yayi ya tuna ma yana da uzuri ba zai samu zuwa ɗakko amaryar ba amma zai kwatantawa Lamin gidan su sai su je. Haka ya wuce ya je ya siyi shinkafa da kayan cefane ya koma ya kai babu kunya kuma suka karɓe kamar dama ana jiransa ba ko arziƙin godiya kuwa sai ma wata tsomararriyar mata da yaji ama cewa Habi ce take ce masa wai ai da ya haɗo da ko ƙashi ne abincin ya fi zaƙi.
Chapter 121 · 0% Book details