← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 158

Sashe 2

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wata dariya nayi kaina ya fasu, irin kalaman nan na Bilal su suke ƙara saka naji duk duniya bani da sauran buri daya wuce na kasance matar sa idan hakan kuwa ta tabbata nasan na kere sa'a, ni da baƙin ciki har abada domin ko babu abinci irin wannan maganganun nasa sun isa su ƙosar dani.
Cikin murya me cike da shagwaɓa nace
"Bana son wasa"
"Wane irin wasa? Kina raina irin baiwar da ubangiji ya miki ko? Baki san hasken idanunki kaɗai sun wadaci a zauna a cikin ɗaki ba tareda an kunna fitila ba?" Ya sake faɗa yana mun kallon dake kashe mun jiki, sena juya ina cewa
"Ni dai barni haka muje ciki kaida baka jin daɗi ka tsaya kana ta surutu"
"Au, surutu ma nakeyi ko? Shikenan bari na koma inda na fito tunda yabonki da nakeyi sututun banza ne a gurinki" Ya faɗa yana ɓata fuska kamar ransa ya ɓaci nan da nan hankali na ya ɗaga na juya da sauri ina cewa
"Haba mana ya zaka ce haka? Nifa ina magana ne akan baka jin daɗi kana gajiyar mun da ƙafafunka da tsayuwa amma kaima kasan bana taɓa gajiyawa da sauraron kalamanka. Ni a duniya ma bayan karatun alƙur'ani akawai wani sauti da nake mararin sauraro ne bayan muryarka?"

Yanda yayi ya tabbatar mun yaji daɗin maganata yace
"A ina zan aje mashin ɗina, ko da yake ma baki ko lura dashi ba balle ki tayani murna"
"Wlh Yarima murnar ganinka da daɗin kalamanka suka sa kai kaɗai nake ji da gani a gabana. Mashin yayi kyau, Allah yasa lafiya ta kashe Allah kuma ya tsare ka daga sharrin ƙarfe da titi" ya amsa mun da
"Amin Halims". Seda na buɗe masa get ya shiga da mashin ɗin kafin muka jera zuwa cikin gidan tabbas nida Bilal haɗin nan da bature yake cewa *MADE FOR EACH OTHER*. Ko magulmata dan suke ganin bamu dace da juna ba suna faɗar haka ne ta wasu fuskokin da a ganinsu muka banbanta bawai a zahirance ba domin duk wanda ya kalle mu seya ce mun dace da juna, daga kuma sanda na haɗu dashi na yardarwa zuciyata tare aka halitto ruhikanmu babu kuma wani al'amari da ze raba mu face mutuwa.

Bilal ya ringa kallon falon kafin yace
"Amma gyaran gida su Anty Labiba sukayi?" Seda na miƙa masa kofin dana cika da ruwan lemon exotic me sanyi ya karɓa kafin nace
"Eh mana, gidan gefensu ne suka fitar da rabin filinsu shine ya siya yayi ƙari. Wannan falon ma ai sabon gini ne ka manta da babu shi"
"Lallai Alhaji Sale bayajin garin nan, a yanda ake kukan babu shi har ya samu rarar gyaran gida ba shakka ƙasar a hannunsu take" ya faɗa bayan daya shanye lemon. Shiru na masa dan nasan yanzu ze fara surutansa da basu nake son ji ba, ilai kuwa yace
"Yanzu me gida kamar wannan be ishe shi ba har ƙari yayo ni ɗan akurkin nawa ma tunda na kai linta na gagara cigaba, koda yake su yan oil and gas dama ai arziƙin ƙasar a hannunsu yake. Da ace muma za'a buɗa mana mu ɗan samu se kiga a wata shida na warware har na fara aje tumbi fa".

Da "uhm" na amsa shi na sauka na fara zuba masa soyayyar jallop ɗin basmati da taji gurzajjen karas da albasa na ɗora masa ƙirjin kaza in da yafi so da haɗin coslow daya ji kwai da madara da. Tun kafin na gama zubawa ya sakko kan carpet ya zauna yana cewa
"Kin san fa tunda kika ce zaki mun girki ko karyawar kirki banyi ba yau ciki na empty yake" nayi murmushi na aje masa plate ɗin ina cewa
"Ai da dai ka ci wani abun ko ba yawa bafa na so ka ringa barin mun cikin ka da yunwa ka sani"
"Ai na ɗauka da safe zaki abincin ne shiyasa da naga har goma tayi baki kirani bane ma nasha Tea" ya faɗa yana kai lomar farko bakinsa. Yanda ya lumshe ido yana tauna abincin kana gani kasan daɗin ya kai masa ko ina, seda yayi loma uku kafin ya kalle ni yace
"Wato Halims bana zaton a duniyar nan akwai macen data kaiki iya sarrafa abinci, wai carkwai maɗagwai. Badan kar inyi saɓo ba se in ce wannan abinci ko hurul'ayni ta dafa ai se haka".

Kaina ya sake fasuwa, na zuba masa zoɓo roba ɗaya ne na sata a fridge ɗin Anty Labiba yana cin abincin yana santi seda yafi rabi kafin yace na sakko muci na girgiza masa kai ina murmushi naci gaba da kallonsa yana zuba loma, yanda yake cin abincin ya kamata ace ya bani haushi irin yanda yake cika baki kamar wanda be taɓa ci ba amma kuma dake zuciyar cike take da so da begensa burge ni yakeyi ina ganin so da shaƙuwar dake tsakaninmu tasa baya kunyata yake iya cin abinci a gabana. Tas ya tada abincin da iri na mu huɗu ma ba lallai mu iya cinyewa ba, shi kansa ina mamakin sa dukda nasan maza suna da cin abinci amma na Bilal kam daban ne kodan yana ƙwallo ne?

Mun daɗe muna hira yana kashe ni da kalaman dake ƙara mun sonsa da ƙaguwar na zamto tasa, ina so ma sako maza zancen tunin da Abba yace na masa akan turo magabatansa a saka ranar auren mu kusan wata uku kenan shiru bece komai ba, yanda yake ta sako mun ƙorafin har yanzu wata shida kenan daya samu aiki wai ba'a fara biyansu albashi ba. Sati uku baya sukaje Abuja akayi capturing nasu IPPIS sun saka ran samun albashi a watan da aka shiga sedai shiru har anci kwana goma babu labari. Wannan dalilin yasa nake masa uzuri tunda koda ace an saka ranar bashi da ƙwaƙwƙwarar hanyar da ze tara kuɗin da ze ƙarasa gininsa har azo maganar lefe da sauran hidimar aure. Samuwar aikin dama da ita muka dogara to gashi kuma har yanzu ba'a samu yanda ake so ba amma kuma dukda haka kamar yanda Abba yace suzo a saka rana ko da shekara biyu suka ce lokaci ne da an kirashi ze zo yafi ace ayi ta tafiya haka babu cigaba. Tun muna ND 2 aka kawo kuɗin aure gashi yanzu satuttuka suka rage da mu gama HND.

Duk ƙawayena da muka fara karatu tare wasu sunyi aure harda yayayensu waɗanda basuyi ba da yawa da sa ranarsu da zarar mun ƙarasa karatu se waɗanda Allah be kawo musu mazan ba, a ciki kuma zan iya cewa nice kaɗai na fara karatu ina da tsayayyen saurayi dan tun ina SS3 muka haɗu da Bilal lokacin daya zo NYSC makarantar mu gashi ana lissafin shekaru kusan biyar kenan yanzu.

"Halims" ya kira sunana hakan ya ankarar dani zurfin da nayi a tunani. Na sakar masa murmushi ina gyara mayafin kaina daya zame yace
"Ina ta magana kinyi shiru akwai wani abun ne?"
Kai na girgiza masa ina murmushi nace "babu komai, ina sauraronka"
"Me na faɗa daga ƙarshe to idan dai kina jina?" Ya tambayeni, na sakeyin murmushi nace
"Cewa kayi kana so na" seya fashe da dariya yace
"Canka kikayi kawai saboda kinsan harshena baya gajiya da furta abinda yake cikin zuciyata. I love you whole heartedly Halims, wlh duk sanda nazo gurinki Allah kaɗai yasan yanda name yaƙi da zuciyata amma ji nake kamar karmu rabu, na masu na kasance tare dake a matsayin matata ta sunna".
Ƙasa nayi da kaina ina murmushi cikin jin kunyar kalamansa, ya matso kusa dani yana cewa
"Dagaske nake Halims, kinga rashin lafiyar nan da nayi duk magungunan da nasha ba wani aiki suka mun ba ina kwance se ince inama kina kusa dani nasan dakin shayar dani maganin dake tattare dake zan warke"

Zumbur na miƙe daga kusa dashi ina ɓata fuska cike da shagwaɓa kamar zanyi kuka ya fashe da dariya yace
"Matsoraciya, ke ba dama a ɗakko magana se ki wani birkice"
"Ni dai bana so" na faɗa ya miƙe yana cewa "Na bari My Halims, bazan sake ba. Amma da gaske a matse nake da son kasancewa dake. Ki tayani da addu'a akwai abinda nake jira da zarar ya tabbata za'ayi komai shikenan ki zama tawa ki dena mun ƙwalele kina hanani bacci da dare" ganin na nufi ƙofa yasa ya shiga dariya yana cewa
"Haba mana nace miki na dena ai yanzun ma baki nane ya suɓuce. Magriba tayi kizo muyi selfie na samu na rage zafi kar na tafi ina mafarkin kwalliyar nan taki". Dakyar na tsaya ya ɗauke mu selfie a wayarsa sannan yayi mun ni kaɗai, har munje bakin kofa yace

"Ban ma san me zanci ba da daddare ba wlh. Wai tuwon Anty Murja tayi bayan tasan bana so ga kuma baki na babu daɗi". A raina nayi murmushi nace "dama jira nake naji zakayi magana ko kuwa" a fili kuma nace
"Afuwan, ganinka ne duk ya rikitani. Bari nayi maka packaging sauran se kaci idan ka koma"
"Haba dai, su Amir ba zasu ci ba? " Ya faɗa kamar gaske. Sena wuce shi kawai a raina ina gulmar halinsa. Ko pure water na bashi seya tafi da sauran balle abinci shine zece wani su Amir ba zasu ci ba. A fararen robobi na juye masa sauran abincin da banda wanda na ɗanɗana da ina girkin ban sake jinsa a baki na ba. Roba uku na masa ɗaya shinkafa ɗaya kaza se coslow a ɗayar lemon ma na juye masa a gorar Faro na haɗe masa komai cikin ledar dana ɗakko.
Chapter 2 · 0% Book details