← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 145 OF 158

Sashe 145

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Anty Ummi ce ta leƙo tace na fito mu tafi, na tada Inayah kafin na ɗauki Sharifa muka fita, nayi tsaye ina kallon Dr Salman a raina ina mamakin zaman me yakeyi da har sannan bai tafi gida ba? Tare muka fita muna gaba yana binmu a baya har muka hau babban titi kafin kowa ya kama hanyarsa. Bayan mun sauke Mama Anty Labiba ta fara mun taratsi wai dama mutumin nan Oga na ne shine na masa wata gaisuwar jeka ka mutu?

"A hakan kike so su baki aiki idan kin gama service ɗin alhalin bakya mutunta Oga? Wlh daga yanda naga yana kallonki na san yaji haushi tun wuri ma ki san ta yanda zaki fara bashi haƙuri". Ni dai ban ce mata komai ba har muka isa gida, Amir da baiyi bacci bane ya ke gaya mana Uncle Faisal ya zo ga saƙo can ma daya bayar a ajiye mun.

Sai da nayi wanka nayi shirin bacci dan munci abinci a gidan Uncle Mudassir kafin na buɗe saƙon da Faisal ɗin ya kawo mun, customized pouch ne na wayata, sai water bottle mai kyau shima da sunana a jiki da kuma jotter mai kama da diary. Na cire asalin pouch ɗin wayar na saka sabon ina murmushi. Shi da ya ce yanda yake jin Khadija a zuciyarsa (Matarsa) ba zai iya yi mata kishiya ba amma kuma na rasa dalilin zuwan da yakeyi da ƙananan kyaututtukan da yake yi mun, duk sanda zai zo gidan sai ya taho mun da wani abu amma kuma ya ce shi ba zawarci na yakeyi ba.

Gyara kwanciya nayi bayan na kashe filila na rufe ido na amma bacci ya gagara ɗaukata, tunanin haɗuwarmu da Bilal jiya ya shiga dawo mun. Tashi nayi zaune na jingina bayana da allon gadon haɗi da rungume ƙafafuwana na zubawa wardrobe ɗin dake kallona ido ta cikin duhun daya mamaye ɗakin.

Babu wata alama data nuna kewa ko damuwa a tattare da Bilal, dukda na sani shi ɗin gwani ne gurin iya ɓoye labarin zuciyarsa ta yanda yake matuƙar wahala ka iya karantar yanayinsa ta cikin ƙwayar ido ko a kan fuskarsa amma nayi tsammanin na tsinci wani abu musamman da nake yawan jin ana faɗar Maza sukan shiga wani hali idan suka rabu da matansu musamman idan ya kasance su suka zalinci matan amma ya akayi ni a kaina abin ya zama akasin haka?

Babu wata damuwa a tattare da Bilal, idan ma ba idanuwa na bane sai naga kamar har haske ya ƙara da kyau alamar bashi da wata matsala a rayuwarsa. Idanuwana suka kawo ruwa nayi saurin share su kafin su fara ɗiga sannan na koma na kwanta ina jan numfashi ta baki a ƙoƙarin kwantar da zuciyata. To wai ma mai zai dame shi ne bayan yana tareda Duniyarsa? Abar ƙaunar sa ya kuma rabu da kaskar da liƙe masa ai dole.

Cusa kaina nayi cikin pillow na saki kukan dana kasa haɗiyewa. Na yarda shi dai Bilal bai taɓa so na ba kawai ni nayi ta cusa kaina na kuma kasa gane hakan tuntuni. Nasha ji da karanta labaran mazaje sa suke cin amanar matayensu da wasu a waje amma ban taɓa cin karo da irin Bilal ba, yanzu nake ganin kamar ma da gayya ya bada ƙofar da zan fahimci abinda yake aikatawa har ma kuma ya barmun shaidar da ko na ci gaba da zama dashi to fa ba zan sake samun kwanciyar hankali ko nutsuwa a tareda shi ba.

Idan na tuna musayar kalamansu da Jalilah da kuma ganin da nayi musu a cikin gidana sai in kasa gane dalilin daya saka har yanzu nake jinsa a zuciyata. Ya kamata ace tun da daɗewa ya fita a raina irin azabar daya ganawa zuciyata har ma da gangar jikina amma dukda haka amma a koda yaushe cikin yi masa uzuri nake. Rabuwa da hawayen nayi sukayi ta shatata tsayin lokaci kafin na tashi na ɗauro alwala na shiga jera raka'oi har saida naji nauyi da ƙuncin daya tasarma mamaye zuciyata ya sauka. Na daɗe a zaune ina tasbihi da yiwa annabi salati har saida idanuwana suka fara rufewa kafin na shafa addu'a na haye gado ban ko ƙara ko minti biyu ba bacci mai cike da nutsuwa yayi awon gaba dani.

Alhamdulillah, tunda ubangiji ya lamunce mun na durfafi kai masa kokena koda ace guguwar ƙaunar dana rasa yanda zanyi da ita akan Bilal ta taso mun dana kalli gabas zanji komai ya wuce tunanina ya saitu na dawo kan hanya.

Washe gari ta kama asabar kusan wuni nayi ina aikin yiwa Al'amin da Inaayah snacks da zasu kai makaranta a gobe Lahadi zasuyi picnic shine kowanne ɗalibi zai kai wani abu daga gidan Anty Labiba tace nayi musu cake da samosa. Sai yamma lis na gama nayi wanka, bayan sallar magriba ina azkar na kunna Data dan yinin ranar gaba ɗaya ban hau online ba, ina kallon saƙonnin da suke ta shigowa, number da na gani ta saka na ɗauki wayar da sauri ina dubawa.

Na goge duka numbobinsa amma haddarsu bata goge a ƙwaƙwalwata ba dan haka ina gani na gane shine dukda wannan layin ba sosai yake amfani dashi ba a lokutan da yake yawan tafiya Abuja ne yake kirana dashi dukda banyi saving ba amma na haddace number.

Kife wayar nayi ba tareda na karanta abinda saƙon ya ƙunsa ba, na san ba zai wuce shirmen daya fara yi mun waccen ranar da muka haɗu ba ne zai cigaba ni kuma banida lokacinsa a yanzu.

Sai da nayi sallar isha'i kafin na tashi daga gurin na zuba abinci na fara ci kenan Anty Labiba tace mun wai Abba yana ta kirana bana ɗauka in kirashi yanzu hakan ya sa na tashi na ɗakko wayar.

Abban na fara kira bayan mun gama maganar da zamuyi har zan ajiye wayar zuciya ta ƙwadaita mun son ganin saƙon daya turo dan haka na shiga Whatsapp ɗin na buɗe.
"Na san ko duk duniya zasu juya mun baya ke kaɗai ce ba zaki gujeni ba My Halims, ina cikin wani mawuyacin hali ina kuma buƙatar taimakonki. Idan kin amince zaki taimakamun ki dawo mun da amsa cikin gaggawa ki kuma shirya zan tura miki da address ɗin in da zaki sameni, na tanadar miki da amsoshin da kika daɗe kina bukatar jin su daga gareni, duk abinda ya faru shiri ne na tabbatar kuma zaki fahimci haka idan kika saurari bayani na. Bilal ɗinki." abinda ya rubuta a saƙon kenan.

Guri na samu na zauna ina sake nanata karanta saƙon,
"Ni da kika ganni ina tarayya ne da mutanen dana san zasu mun amfani a rayuwa, da zarar amfanin mutum ya ƙare kuma zan ajiye shi dan ni bana son liability" maganganunsa na wani lokaci suka shiga dawo mun. A fili na furta

"Tabbas na shaida hakan, ya watsar dani a lokacin da yake ganin amfanina ya ƙare a gurinsa ashe kuma da saura". Blocking ɗin number na sakeyi dan dama nayi ban san dalilin daya saka na buɗe daga baya ba. Da naga tunanin yana neman ya hanani sukuni sai na ɗakko system ɗina na tura research proposal ɗin da Dr Sulaiman ya tura mun akan idan ina sha'awa na shiga ayi dani. Wannan ya ɗauke mun hankali har zuwa sanda na gaji na kwanta bacci.

BILAL
A tunaninsa ɓatan dabon da yayi shine mafita, Minjibir shine in da yake ganin zai iya zama na wani lokaci kafin abinda yake jira ya samu ya koma gida. Abinda kuma ya saka ya zaɓi can ɗin kasancewar gurin wajen gari ya sani da wahala ace ya haɗu da wata fuskar sani saɓanin idan hotel ya kama a cikin gari. Yayi tunanin ko dai ya kira Zulaiha ne yace ta taho? Amma kuma daya tuna Zulaihan ba wacce ya sani a baya bace sai ya fasa, baya zaton zata rufa masa asiri koda ya faɗa mata gaskiyar halin da yake ciki, ba ita ba ko yan uwansa ya san ba zasuyi shiru ba a yanzu a duniyar nan kaf Halima ce kaɗai wacce yake da tabbacin ko mutum ya kashe zata rufa masa asiri.

Ya kunna wayarsa amma ya barta a flight mode, tunani ya ringayi anya kuwa bayan duk abinda ya faru Halima zata sake dubansa? Zuciyarsa ta bashi ƙwarin guiwa akan fushin Halima akansa ba mai dogon zango bane, dukda shi da kansa ya tabbatar da yaga canji amma ko a shekaran jiyan ya hangi ɓurɓushin soyayyarsa da bata ida mutuwa ba a ƙwayar idonta.

Ya san mai take so, soyayyar sa da kuma tattali da kulawa da zarar kuma ta same su zata manta komai. Da wannan ƙwarin guiwar ya ɗora wani tsohon Data sim da ya siya bai zaci ma yana aiki har lokacin ba yayi recharging nasa kafin ya cire layukansa biyu da aka sanshi dasu ya zuba a zip ɗin jakarsa sannan yayi sub ya buɗe sabon Whatsapp da layin ya tura mata saƙo.

Tun yana tsammanin samun amsa har ya fitar da rai dukda cewar ta buɗe saƙon, ganin har tara ta gota bata ce komai ba ya yanke shawarar kiranta voice call amma cikin rashin sa'a bata online cikin jin haushi ya kashe wayar gaba ɗaya kafin ya kwanta yana juyi akan gado cikin rashin sanin madafa.

Kwanciya yayi yana lissafin mafita, ya sani ƙarshe Jalilah ta nemi ya biyata kuɗin kayan daya ɗiba dan bayan su duk wani abu daya mallaka masa daga haɗuwarsu zuwa yanzu kyauta ce ba kuma roƙarta yayi ba dan haka bata isa ta nemi wani abu daga ciki ba. Kuɗin kayanta kuma da kuɗin Alhaji Lawan basu wuce chicken change ba idan abinda yake jira ya sauka

Life time saving ɗinsa ya tattara, duk kuɗaɗen daya ringa samu a hannun Hafiz da Jalilah harda kadarorin daya siya duk ya siyar ya haɗa kuɗin ya zuba a hakar fitar da kayayyaki ƙasashen waje.

Tun kafin ya auri Halima akwai abokinsa Yahya ne da sukayi University tare shi Yahya yana harkar Import and Export na kayan noma irinsu Citta, Barkono, Riɗi da su Zoɓo.
Chapter 145 · 0% Book details