Sashe 56
Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
"Daga magana se ki fara yi wa mutane kuka, gaskiya ta na faɗa miki, in ba sata kike sona yi na baki ba ya kike so na yi? Ni ban hana ki kiyi ba idan kina da kuɗi, amma ni dai bani da abin da zan baki. Ban da ma bakya tsoron Allah duk kuɗin da ake baki ki na ɓoye wa ni ban saka miki ido na ce ki bani ba shi ne har zaki iya buɗe baki ki tambaye ni wani abu. To ba ni da su, idan ma saboda yan uwana na da zasu zo ya sa ku dafa tsiyar ku ku cinye su ma za suyi na su a gida babu lallai ma kowa ya zo, Ni ta kuɗin ragon suna na ke yi ba wani can shirmen abinci ba" ya sa ke jan tsaki kafin ya fice daga ɗakin yana ci gaba da mita.
Haɗe kai na yi da guiwa na shiga risgar kuka na ma rasa takamaiman tunanin me zan yi? Me ya canza Bilal haka? Ko kuwa dama can haka ya ke ɓoye mun asalin halayyar sa ya yi se bayan da mu ka yi aure tukun na?
"Kiyi haƙuri uwata, wannan kukan ba ze kawo miki mafita ba sai dai ki sake jefa kanki cikin wata damuwar" Baba Jummai ta faɗa, ban san sanda ta shigo ɗakin ba amma yana yin yan da ta yi maganar a sanyaye jikina ya ba ni duk yan da akayi ta ji yan da mu ka yi da Bilal tun da ba a hankali yayi maganar ba kuma ƙofa a buɗe ta ke. Hannu na sa na shiga share hawayen amma suka ƙi tsayuwa, ta zauna gefe na tare da da fa ni ta ce,
"A kwana biyun nan na fahimci abubuwa da yawa dangane da zaman ku uwa ta. Ina yawan jin zancen mijin ki a bakin Hajiya tun ma kafin kuyi aure amma na ɗauka kawai dan basa son haɗin ku ne amma yanzu na fahimci sun fi ki gaskiya.
Magana ta domin Allah, a ɗan zaman da nayi da ku na fahimci mutumin da dangin sa duk yan da aka yi sun so ne su mayar da ke daddawar ɓurma, ke kuma So da ƙuruciya ya rufe miki ido kika kasa gane hakan".
"Kallon rashin fahimta nayi mata dan ban taɓa ji ba balle na san ma'anar kalmar da ta faɗa daga ƙarshe; ta ci gaba da cewa
"Ko a ƙauye ban taɓa ganin in da ake haka ba. Haihuwar fari dai ko mutum shi ya yankewa talauci cibiya yana hoɓɓasa da taimakon dangin sa ya yi abu na bajinta balle wannan yaron da duk wanda ya kalle shi ya san babu rashi a tattare da shi sai dai mugunta kawai ta hana ya yi miki abin da ya kamata. So ya ke yan da ya aure ki ki zame masa hannun jari komai iyayen ki su ringa ɗakkowa suna baki toh ni dai ba zuga ki na ke yi ba amma tun da sauran hasken rana duhu bai cimmiki ba ki ki farka ki kuma ƙwatarwa kan ki yan ci domin har idan kuka miƙe a haka tabbas ke zaki sha wahala musamman da ya kasan ce ya riga da ya gane son da kike masa ya fi na sa".
Mayar da kai na nayi ƙasa kawai ina sauraron ta, zuciya ta na so ta kama abin da take faɗa amma kuma wani ɓangaren ya kore maganganun nata. Kullum haka suke cewa Bilal ba ya so na ni kuma ba zan taɓa yarda da hakan ba. Abin da na jaddadawa zuciya ta shine Bilal ba shi da kuɗi sannan ya na da matsalar rashin iya tantance kalmomin da ya kamata ya yi amfani da su a magana shi ya sa yake faɗar kowacce irin magana ta zo bakin sa ba tare da ya taunata ba, wannan kuma ɗabi'ar mutane da yawa ce ba shi kaɗai ne haka ba. Wannan tabbacin na bawa kai na ya kuma kore tasirin da maganganun Baba Jummai suka so suyi a ƙwaƙwalwa ta.
"Bilal ya na so na, kuma na san ba shi da shi ne shi ya sa amma babu abin da ba ze yi mun ba Baba Jummai" na bata amsa ina murmushin da be kai zuci ba, ta ƙura mun ido kafin ta ce
"Yanda ki ke kyautata masa zato Allah ya bawa maraɗa kunya a sanda zai samu wadatar yi mikin" daga haka ta miƙe tana gyara goyon Al'amin kamar yanda Abba ya ce ba za'a saka masa wani sunan iyayi ba a kira shi da hakan. Tana rufe mun ƙofar na sake fashe wa da kuka, ni ya ke cewa ba ni da tunani kuma ba ni da tsoron Allah na ɓoye kuɗi ban ba shi ba.
Ƙarar waya ta ta sa na tashi na ɗakko ta, Anty Labiba ce. Sai da kirab ya katse wani ya sake shigowa lokacin na dai dai ta kaina kafin na ɗaga.
"Bacci kika fara ne?" Ta tambaya nasan kuma murya ta da ta ji ne dalili, na samu gangara dan haka na ce mata
"Eh wlh, na ga ji ne; na ɗan kishingiɗa ban ma san ashe bacci ya ɗauke ni ba"
"Sannu, toh ya kuka yi da Bilal ɗin?" Ta sake faɗa. Sabon kuka ne ya kusa ƙwace mun amma na danne shi da ƙyar na ce mata
"Ni fa ban yi masa magana ba Anty saboda kin ga fa wayar sa da aka ƙwace sun yi amfani da ita sun kwashe masa kuɗin account duka, kuma ba'a yi albashi ba ai se yaga rashin hankali na ma idan na yi masa maganar wasu kuɗi yanzu, sannan gashi ba shi da lafiya ko fita ba ya yi a zo a tara masa hayaniya a kai a babu daɗi".
"Kuma haka ne" ta faɗa amma se na rasa har ran ta tayi maganar ko kuma baƙar magana ta faɗa mun tunda na san halin ta sarai, a sanyaye na sa ke cewa
"Kawai a bar taron ko Anty tun da dama yawancin duk waɗan da zasu zo sun je tun muna asibiti wa su kuma sun zo nan gidan".
"Shikenan se ayi hakan, amma dai kin san yan Galadanci ko an ce babu taron suna ba zasu fasa zuwa ba kuma jiya Mama duk ta sake aika musu da yaji wanda ya manta ma kin ga an tuna masa, amma dai shikenan tun da mai gida ya ce ba za'a yi taro ba ai ba a zo masa gida ba bari na kira ta yanzu se a gaya musu a can gidan ku za'a yi sunan dama ai ba wani abu bane taron sunan a haɗu ne kawai a ci abinci ba lalali sai kina gurin ba".
"Aa fa Anty shi ba cewa yayi kar ayi ba" na yi saurin katseta kafin ta ƙulla wata maganar, ba ta ja zancen da tsayi ba ta mun sallama bayan da ta ce itama ai ba cewa tayi shi ya hana ba ta fahimci maganata kawai zasu yi taron su a gidan Mama shikenan. Ranar kasa bacci na yi har guraren ƙarfe uku sannan, maganganun Bilal suka yi ta mun yawo a zuciya, se da na ji kaina yana neman tarwatsewa saboda ciwo kafin na rarrashi kai na nayi bacci.
BILAL
A fusace ya fice daga ɗakin ya koma ɓangaren sa. A falo ya kwanta ya tada kansa da hannu biyu ya tafi tunani,
Waccen ranar da ya gamu da tsautsayi bayan sun rabu da Nasir ya koma gidan Hajja ya tarar da ita ta na shirin tafiya dubo Halima ya hanata, bayan sun koma ɗaki ta ke ce masa
"Amma yanzu idan ba mu je ba kar ace mun yi rashin kyautawa, musamman da Balarabiya ce matar ƙanin uban ta ta shigo har nan ta gaya mun kaga ai ko da kai ba'a kira ka ba ni ai an gaya mun ka bari kawai na je dai". Zama yayi ya kalallame ta da zance yana nuna mata ai matsayin su ya fi ace can wata za'a aiko ta faɗa musu kawai ta ƙyale su idan ma za'a je ɗin se gobe da safe tukunna tun da yanzu dare yayi. Har ƙarfe tara yana gidan Hajjan sai da ya ci abinci kafin yayi mata sallama ya tafi gida a bakin titi suka sake haɗuwa da Nasir ya ringa masa masifa da ya ce masa bai je asibitin ba har sannan amma ko a kwalar rigar sa ya ce shifa sai da safe sannan zai je. Sai da ya koma gida kuma gaba ɗaya ya kasa tsaye ya kasa zaune. Har ya kwanta ya ringa jin kamar hakan da ya aikata ganganci ne musamman da bai san me suka faɗa da suka je gidan ba kar wannan ƙin zuwan da zai yi ya sa a gasgata maganar su. Sha ɗaya tayi amma haka ya zura jallabiya ya fita. Bai kuma yi nisa da fita daga layin su ba wasu da bai san ko su waye ba suka tare shi, kafin ya yi ihu suka rufe masa baki su uku ne, mutum biyu suka masa dukan tsiya ɗayan ya haye mashin suna gama jibgar sa suka zare wayar sa suma suka hau mashin ɗin su ka arce.