Sashe 11
Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A ɓangaren Bilal ma dai shiru ne, nayi zaton yanda nake cike da ɗoki shima hakan ce zata kasance dashi amma sam ba haka ba. Kullum yazo bashi da zance se na gini, ya rasa ya ze yi, kaza ya ƙara tsada se ya kashe kaza akan yin abu kaza kuma shi bashi dasu ko waya ya kira ko na kira shi zancen kenan har na fara gundura da jin sa daya fara akwai se in bashi uzurin zan yi wani abu na kashe wayar. Ban sake shan mamaki ba se wata rana daya zo bayan shan ruwa yake nuna mun ci gaban aikin da akayi a wayar sa se na ga babu banbanci da wancan zuwan da mukayi, fulasta kaɗai aka ƙarasa se wiring ɗin ruwa da yace anyi.
Rai na ya so su, tun ku san sati ɗaya kenan Hansa'u take ta mun magana akan ya kamata mu fitar da anko in gaya wa Bilal ya bani kuɗi muje kasuwa. Nasan haka akeyi to amma tausayin sa da nake ji da yanda kullum yake ƙorafin gini ya hana shi sakat yasa nace bazan tambaye shi ba ƙarshe se Abba na tambaya da Mama ta ji ma tace ba yanzu ba in bari se bayan ƙaramar sallah tunda bikin ze kama bayan babbar sallah ne da kwana goma a lissafi. Ni ina ta tunanin ƙila ma an kusa gama fenti ashe shi tafiyar hawainiya ma yake yiwa aikin. Kasa daurewa nayi nace masa
"Yanzu tsahon lokacin nan ashe babu abin da aka ci gaba a ginin nan? Yau fa sauran kwana casa'in da biyar ace ba'a ma ɗakko hanyar kammala gini ba balle a fara sauran hidimomin biki?" Se ya kalle ni yace
"Wace irin magana kike yi haka Halima? Ashe ma baki yaba abinda nake yi ba kin san tsadar kayan gini kuwa a wannan zamanin? Karfa ki manta Halima ni nake yiwa kaina komai ba wani bane yake tallafa mun sannan hidimar nan ba iya tawa bace ba sanin kanki ne ga auren Naja ni zan mata kayan ɗaki bayan kuma albashi na kin san ba wata hanya ce dani ta samun kuɗi ba". Nayi shiru saboda na hango gaskiya a cikin tasa maganar shima, ba shi da matallafi se Allah ga kuma hidimar ƙanwar sa kamar yanda yace ita ma abar dubace.
"Shi yasa tun farko na guji a saka mun rana ba tare da na gama shiri na tsaf ba, kuma da aka je ma ni shakara ɗaya nace aka tashi aka sa wata shida bayan an san ba lallai na shirya a wannan lokacin ba" ya sake faɗa kamar cikin fushi. Se na kalle shi na ce
"To me kake nufi yanzu?"
"Ni babu abinda nake nufi kawai raina beji daɗin yan da kika raina ƙoƙari na bane har kina cewa wai duk tsahon lokaci babu abin da nayi".
Shiru kawai nayi ina kallon sa na rasa ma abin da zan ce har ya gama yayi shiru dan kansa. Haka dai ba daɗi muka yi sallama ya tafi, ko abincin da nayi niyyar bashi ban ɗauko ba shima kuma be tambaya ba, da asuba ma be kira ni ba har gari ya waye gurin ƙarfe goma se kuma duk naji na damu. Nasan dai ba wata magana na gaya masa da ya kamata ace ta masa zafi ba amma hakan nan na danne zuciya ta albarka cin son da nake masa na kira shi.
"Raina ya ɓaci Halims, ya za ayi duk fafutukar da nakeyi akan naga nayi komai cikin rufin asiri amma kina rai nawa? Ke baki ga girman gidan bane ba kiga irin tsarin da aka ɗakko ba?" Ya faɗa bayan dana gama ban baki. Nace
"Gaba ɗaya ka juyawa magana ta manufa ne amma ni ban raina ƙoƙarin ka ba kawai a nawa tunanin dai zuwa yanzu ko za'a ce da sauran aiki to ƙarashe irin wanda ma be zama dole ba. Kuma ni da zan baka wata shawara kaji, me ze hana ka mayar da hankali kawai ka gyara iya ɓangaren da zan zauna a ciki? Tun da dai mu biyu ne kawai a cikin gidan ko da ace ka gyara can ɗin ma ba lallai ace za'a yi amfani dashi yanzu ba. Kawai ka barshi ka tsayar da hankalin ka a guri ɗaya ina ganin ze fi".
Se yayi shiru kafin yace
"Na yi tunanin hakan amma kuma bana son raini"
"Wane irin raini kuma?" Nayi saurin katse shi, se yace
"Ba zaki gane ba. Ki kwantar da hankalin ki za ayi komai kafin lokacin, naga alamar kin fini matsuwa fa Halims to ki cigaba da daurewa saura ƙiris ba zaki maimaita azumi a gida ba". Na rufe fuska kamar ina gaban sa nace
"Kasan bana son irin haka"
"Surutun kawai, zaki yi baya ni ne duk ranar da kika shiga hannu yarinya" ya sake faɗa se nayi saurin datse wayar jin yana neman sakin layi da azumi a bakin mu. Shikenan muka shirya aka ci gaba da azumi kwanci tashi har satin sallah ya kama.
Shakara biyar muna tare da Bilal be taɓa mun toshi ba har ga Allah wannan sallar na tsammaci ze yi tun da dai yanzu ai kusan na zama tasa za'a ce se dai shiru kake ji har sallah ta rage yan kwanaki babu wani labari. Ranar da ya rage kwana uku idi bayan an sha ruwa yazo kamar ko yaushe ina shirin zuwa gidan Anty Labiba zan kai mata saƙo daga nan na karɓo mana ɗinku nan mu ni da Mama. Tare da Bilal muka tafi, bamu jima ba muka dawo tun a hanya yake ce mun wai
"Iye yar gatan Abba da Mama. Yanzu duk ledojin nan kayan sallar ki ne, ni ina nan ko rigar da zan saka naje idi bani da ita. Takaici yasa na masa banza har ya sauke ni a ƙofar gida, na shiga na aje kayan sannan na fito mu kan ɗan taɓa hira kafin yayi haramar tafiya, dubu uku ya bani yace gashi nan nayi kitso da lalle.
"Na bawa Hashir sautun abaya, na ɗauka ze dawo lafin sallah se jiya yake ce mun wai jirginsu washe garin sallah ne kiyi haƙuri da wannan" ya faɗa bayan daya bani dubu ukun. Gashi dai ba wasu kuɗin azo a gani ya bani ba, a yanda nake tsaye ma ina da ninkinsu a jikina amma se naji daɗin kyautar tamkar wanda ya bani miliyan uku. Na ringa murmushi ina cewa na gode shi kuma ya basar wai akan 3k ai ba haka yaso ba in yi haƙuri da hakan kawai. Dana shiga gida haka na tarar da Mama ina dariya na bata kuɗin ta kalle ni ta kalle su da taji daga in da suka fito ina ga takaici ne ya saka ta dariya kawai tace ya kyauta. Washe gari tun da wuri na tafi gidan lalle kafin azahar an gama mun da daddare kuma naje gidan su Hansa'u ta yarfa mun kitso a nan naga abin arziƙin da Alhaji Bala ya kawo mata na toshi akwati guda harda kit kamar lefen bazawara ba abin da babu ciki tun azumi na tsakiya dama ya zo gaisuwar azumi nan ma ya kai musu sha tara ta arziƙi naji mata daɗi amma ba wai abun ya burge ni ba dan ni dai wlh da dai na auri dattijo kamar Alhaji Balan saboda kuɗi gara in ƙare a talauci tare da wanda nake so.
Ranar idi haka na shaƙe kuloli saiti biyu da abinci, ɗaya na Bilal ɗaya na Hajjan su na bawa Aliyu ne Adaidaita ya kai musu Mama dai kamar yanda tace taga ikon Allah amma tunda me kawo abincin yace babu ruwanta a bar ni nayi yanda naso sadaka ce dole ta kama bakinta tun da dama ni nasha wahalar girka miya, wai na da tuwo kuma matar dake mana duk sallah ce ta zo tayi. Da yamma Bilal yazo, mutumin da yace beyi ɗinkin sallah ba se gashi da sabuwar kwalliya ba wadda ya turo mun hotunan idi da ita ba. Daya tashi tafiya nan ma a karon farko ya bani rafar yan naira goma sabbi yace na bawa Imam da Amirah barka da sallah Mama kuma na gaya mata jibi zasu zo gaishe ta da abokanansa.
An ci sallah an cinye watan shawwal ya mutu har an shiga zulƙida ya raba a taƙaice ce dai ƙasa da kwanaki sittin a lissafin kwanakin ranar auren mu. Gidan Baba Salahu su Sauda da za ayi bikinmu tare suna ta shiru tu ni sun fitar da anko, sau ɗaya na yiwa Bilal zancen ina so zan fitar da ankon yace mun ya kamata kam na bashi tazarar sati ɗaya na ga ko ze mun wani abu amma naji shiru se kawai na share shi nayi amfani da kuɗin da Abba ya bani muka siyo Atamfa kala biyu, ɗaya ta kamu ɗaya ta yinin biki saboda rashin ta ido da na nuna masa se ce wa yayi
"To ina na dinner kuma? Ko ba zaki mana dinner ba Halims?"