← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 158

Sashe 42

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kwana uku tsakani Hajja ta dawo, ita da aka ce zatayi sati biyu. Tun ana gobe zata dawo ɗin Bilal ya gaya mun dake naje gida na samo yan kuɗi se nayi amfani dasu nayo cafane nayi mata girki yan da naga Anty Labiba tana yi idan surukar ta tayi tafiya ta dawo zata mata girke girke ta kai mata. Da wuri suka iso dan asubanci suka yo kamar sanda zasu tafi, da la'asar bayan ya dawo aiki yayi wanka na kwashi kwanuka ya goya ni a mashin muka tafi gidan, rabon ayi. Da ace nasan abin da yake jira na a gidan da ban yi giggiwar zuwa mata sannu da zuwan ba. Da Yaya Uwani wadda Bilal yake bi muka fara cin karo a soro zata fita mu kuma zamu shiga, da fara'a na shiga gaishe ta, irin kallon banzan data watsa mun haɗi da tsaki yasa jiki na yayi sanyi laƙwas nabi bayan Bilal da dama be tsaya ba.

"Yanzu ke har kina da kunyar da zaki sake tako ƙafar ki cikin gidan uban Fadila?" Kalaman da Hajja tayi mun maraba dasu kenan. Nayi zukuɗi ina ƙoƙarin tantance in da maganganun ta suka dosa amma na kasa se kawai na zura mata ido ina jin irin fisaji da cin mutunchin data ke mun a maganganun nata nayi nasarar gano akan Fadila takeyi. Bani kaɗai ba hatta iyaye na dake can gida basu san wainar da ake toyawa ba se da suka amsa rabon cin mutunchi a gurin Hajjan,
"Daɗin abun tun kafin uban ki yasan zeyi arziƙi a duniya uban Fadila yayi da har zaki mata gorin gida gidan ma na ɗan uwanta da idan ya faɗi ya mutu yanzu tana da gadon sa. Ko da yake ba laifin ki bane, laifin sa ne daya barki kika bararraje har kike tunanin kin ci gida se wanda kika ga dama ze shiga ya zauna" ta faɗa tana kumfar baki.
Sautin kukan da na keyi ƙasa ƙasa ya ƙaru, a duniya ka mun komai karka zagi iyaye na ko kaci mutunchin su.

"Haba Hajja ki bari mana ya isa haka" naji muryar Bilal, se na ɗaga kai na kalle shi dan ban taɓa zaton yana ɗakin a tsaye Hajjan take mun wannan tijarar kuma yayi shiru ba.
"Yanzu kana tsaye kana ji ana tuhumata da laifin daka aikata?" Na faɗa cikin kuka, ya kalle ni yace
"Ban gane ba?"
Kan Hajja na juya ina kukan nace
"Allah shine shaida ta ban kori Fadila ba, idan kuma zata faɗi gaskiya ni ko kallon banza be haɗa ni da ita ba balle nace ta bar gida. Ina ruwa na da zaman ta? Shi me gidan ai gashi nan shi yace baya buƙatar zaman ta kuma Allah shaida sanda ya kore ta ma bana gurin kuma kana tsaye kana kallo ana tuhumata ba zaka faɗi gaskiyar abinda ya faru ba" na ƙarasa ina kallon Bilal daya tsuke fuska yana muzurai.
Hajja ta rafka salati ta shiga tafa hannu tana cewa

"Ba shakka yau naga in da ake bariki, kai Bilal uwarka Halima na magana se ka rufe ni da duka saboda ma mata ƙazafi". Maimakon ya kare ni se gani nayi ya juya ya fice daga ɗakin gaba ɗaya ita ko kamar an iza wuta taci gaba da maganganu tana faɗar duk abin da yazo bakin ta. Daƙyar ina ganin dishi dishi na miƙe jin tijarar bame ƙarewa bace, Allah ya taimake ni ina fita daga gidan na samu Napep kai tsaye na wuce gidan mu. Ina rusa kuka na shiga gidan ba tare da na ko sallami me Napep ɗin ba ya biyo ni yana tambayar kuɗin sa.

A ƙasa na zube ina cigaba da rusa kuka Mama dake kitchen ta fito kusan a guje tana tambayar waye? Gani na yasa ta ƙaraso da sauri ta ɗago ni cikin tashin hankali tana cewa
"Meya samu Bilal ɗin?". Se da naji numfashi na na neman ɗaukewa kafin na haƙura na dena kukan amma naƙi cewa komai tun Mama na tambayata harta tashi ta barni ta kira Abba a waya tace masa gani nazo ina kuka naƙi cewa komai yace mata karta kira kowa gashi nan zuwa. Ina kwance ina jan rai, wani irin azababben ciwon kai ya dirar mun lokaci ɗaya. Ina kwance riƙe da kai Abba ya dawo, tiryan tiryan na kora musu yanda akayi tun daga zuwan Fadila har zuwa yau ɗin. Mama ta zabga tsaki tace

"Tun wuri ki nemi yafiya ta dan wlh kin ɗauki alhaki na gaba ɗaya kin tada mun da hankali na ɗauka ma wani tashin hankalin ne ya afku" Abba ma miƙewa yayi yace
"Allah ya rufa asiri" daga haka ya fice daga ɗakin. Mama ta dira mitar ɗaga mata hankalin da kuka na yayi kafin ita ma ta fita ta bani guri. Se naga su abun ma be dame su ba kenan, ba ma wanda ya sake bi ta kai na se da akayi magriba Mama ta leƙo ni lokacin har baccin wahala ya fara fizgata kai na na ciwo sosai. Se da naci abinci nasha magani nayi wanka kafin na kwanta. Bilal be kira ni ba har kuma bacci me nauyi ya kawashe ni be zo ba se da safe Mama take cemun wai miji na yazo tayi ta tashi na ban farka ba shine yace a barni kawai.

"Se ki maza ki gama abin da zakiyi Mu'azzam ya kai ki gida dan jiya har gurin sha ɗaya yana nan se kace wanda aka ce za'a cinye ki" Mama ta faɗa. Nayi rau da ido nace
"Da yazo kin masa maganar abun da Hajjan su ta mun?"
"Ni kuma a wane hurumi? Wannan ai tsakanin ku ne kun fi kusa shikenan kuma saboda kinyi ba daidai ba maman mijin ki ta miki faɗa se na shiga na rama miki kike nufi ko me?" Mama ta faɗa. Se ko hawaye suka ɓalle mun ta miƙe tana cewa
"Kin so dai ki ƙarawa kanki wata damuwar banda haka wanda ya siyi rariya ai dole dama yasan zata zub da ruwa. Duk mutumin da Allah ya haɗa ka zama dashi se dai haƙuri da taka tsantsan kawai abinda ya rigada ya faru kuma ai ya faru se dai ayi rigakafin wanda be zo ba" ta faɗa tana ficewa daga ɗakin.

Ba dan raina ya so ba se dan rasa goyon bayan Mama na tattara Mu'azzam ya kaini gida da yamma na ringa share hawaye a hanya, an mun wulaƙanci na tafi gidan mu akan su shiga su ƙwatar mun yanci ba daraja sun koro ni yanda gobe ma za'a ji daɗin sake ƙala mun abin da ban aikata ba aci mun mutunchi da gangan. Yau na ga ranar Anty Labiba, ita kaɗai ce zata tsaya mun amma da nauyi abun daɗi be kaini gidan ta ba yanzu se na kwashi matsala naje mata.

A gida muka tarar da Bilal, Mu'azzam be shiga ba ya gama sauke mun kayan da ban san dasu ba a nan tsakar gida ya barsu yayi tafiyar sa. Ina ƙoƙarin saka key na buɗe ƙofar falo aka buɗe ta daga ciki Bilal ya fito a wani hargitse kamar wanda ya kwana be runtsa ba yana gani na ya wani rungume ni da ƙarfi se kace wanda ya shekara yana nemana se yau Allah ya bayyana masa ni, dana tuna yanda ya tsaya Hajjan su na zagi na ya bece komai ba take ido na ya kawo ruwa na shiga ture shi amma yaƙi saki na seka ɗauka ta da yayi cak ya wuce cikin ɗaki dani ina ƙoƙarin fizgewa be sake ni ba se da ya dangana ni da gado na fashe da kuka sosai ina matsawa baya ya biyo ni yana cewa

"Me kike yi haka Halims? kin san irin tashin hankalin da kika jefani jiya kuwa? Me yasa zaki tafi baki kira ni ba? Saboda Allah da kika je gidan me kika ce musu?"

Haɗe kai da guiwa nayi na shiga rera kuka, ya kaɗa ya raya nayi shiru na masa banza daya matsoni ze sakani jikin sa kuma zan fasa wani kukan na janye se ya haƙura ya barni yana cewa
"Ni dai karki jiwa kanki ko abinda yake cikin ki ciwo na barki bazan sake taɓa ki ba amma ki dena wannan kukan".
Chapter 42 · 0% Book details