← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 158

Sashe 12

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A lokacin a wasa na ɗauki zancen mukayi dariya kawai ina ce masa "wannan ai hurumin ka ne, idan za kayi ko ana go be ranar ne ba zamu kasa samar da abin da yammata za suyi amfani dashi ba tun da kasan shi ankon dinner dama ba da yawa ake yin sa ba" ya ce
"Shi kenan Allah ya kai mu lokacin na gaya miki har idan da hali babu abin da ba za ayi ba Halims ki na raina soyayyar da naki miki".
Ranar Alhamis aka aiko wa Mama daga gidan Baba Salahu akan ranar Asabar za a kawo lefen Sauda, ni se da naji aiken na tuna da batun wani abu a aure wai shi lefe. Ko da wasa bamu taɓa zancen da Bilal ba, be mun maganar ba ni ma ban masa ba ni hankali na duk ya tattare akan ya kammala gini shi yasa ma na manta da wani batun lefe ƙila. Bayan yaron ya tafi Mu'azzam yake ce mun
"Ke kuma se yaushe za a kawo naki lefen? Ni wai Mama bikin nan yana nan kuwa dan ban ga ana wani shiri irin za a aurar da yar fari ba ko dama duk bula ce da ake nuna an fi son ta akan mu?"

"Bana son sakarci Mu'azzam wane irin magana ne zaka ce an fi son ta akan ku?" Mama ta kwaɓe shi se ya ce
"To yanzu dai ya maganar bikin akwai ko babu in san shiri na?" Wai se na ji Mama ta ce masa
"Ga ta nan ai se ka tambaye ta ni ma ban sani ba". Tsabar dariyar shaƙiyanci se da ya faɗo daga kan kujerar da yake zaune ya ce
"Ai ko dai se dai a tambaye ta, kullum fa ina laɓe wa naji hirar da suke wlh Mama ki tashi tsaye da addu'a lamarin Halima fa kamar akwai saka hannu"

"Wai Mu'azzam me yasa bakin ka bashi da saiti ne?" Mama ta sake faɗa yace
"To wlh ita take forcing maganar auren nan mutumin nan kullum yazo uzurin safe daban na rana daban ina ji jiya yana ce mata wai ya siyi interlocks an je ɗakkowa motar tayi accident duk sun farfashe kiji fa wata jahilar ƙarya ko a gidan uwar wa ma yake ginin oho dan dai ban ga in da aka nuna a unguwar su aka ce na sa ne ba"
"Tashi ka bani guri Mama" ta kore shi ya fita yana surutansa se da ya maido ƙofar falon ya rufe kafin Mama ta kalle ni tace
"Saura kwana nawa ya rage biki ne Halima?"
"Kwana hamsin da uku Mama" na bata amsa kai tsaye, ta girgiza kai tace
"Madallah, kwana hamsin da uku amma shiru babu wani motsi daga gidansu yaron nan shi be ce komai ba iyayensa ma basu ce komai ba ko kuma kun ɗaga ranar ne bamu sani ba?"

"Ai suna ta ci gaba da shiri ne Mama mu ne anan har yanzu ba'a fara komai ba" na faɗa kai na a ƙasa. Tayi murmushin daya fi kama da yaƙe tace
"Haka ne, to Allah ya nuna mana lokacin da rai da lafiya. Ki shirya kayan ki cikin satin nan zaki koma gidan Labiba kafin lokacin bikin". Baki na tunzura gaba nace
"Gaskiya ni Mama ki barni nayi zama na a nan kin san dai Anty Labiba yanzu ta canza ba wani so na takeyi sosai ba". Banza ta mun, ta wuce ɗaki ina mita amma kuma dana zauna nayi tunani nan na gano ƙila gyaran amare za a fara mun shi yasa tace na koma can dan na san Mama da kunya hali na ne ma yake sakata magana in ba dan haka ba ba wani shiga sabgata take yi sosai ba. Nan da nan na fara haɗa kaya da yamma nace mata zan tafi tace Aa na bari se gobe haka ko akayi washe gari da azahar nayi ƙaura zuwa gidan Anty Labiba.

"Ni kam Halima ko kin ce masa kin yafe lefe ne babu labari? Sannan na zata zuwa yanzu ai ze ce azo a ga gida ko saboda musan irin tana din da zamuyi" Anty Labiba dake kallo na ta faɗa. Ina danna waya ta na ce
"Ban san san da zasu kawo ba Anty, gida kuma akwai sauran aikin da ba'a ƙarasa bane shiyasa amma nasan da zarar an gama ze yi magana aje a gani gidan ai ba wani wahalar jere zeyi ba" nan na shiga wassafa mata yanda tsarin gidan yake. Tayi shiru kawai tana kallo na kafin tace

"Kin je kin gani kenan" na kalle ta jin kamar ta rafko ni se na wayan ce nace
"Haba dai. A waya dai kullum idan yazo yake nuna mun duk abin da a ka yi". Tayi shiru kamar ba zata ce komai ba har na fidda ran zata sake magana kafin naji tana cewa

"Amma kina ganin wannan hanyar da kika bi me ɓillewa ce Halima?" Na kalle ta na ce
"Wa ce hanya kenan Anty?"
Gyara zama tayi ta fuskan ce ni da kyau tace
"Halima, ita mace da kike gani abu kaɗan ke in ganta rayuwar ta haka nan ɗan abu kaɗan ke sakata a taskun rayuwa. Dace ko rashin dacen abokin zama wato miji abubuwa ne masu matuƙar tasiri a rayuwar ya mace. Gidan aure shi ne aljannar duniyar mace, idan tayi da ce na ƙwarai ta rabauta haka nan idan ta kuskure shikenan rayuwarta ta shiga walagigi ita da samun nutsuwar duniya se dai idan ubangiji ne ya ƙaddara mata wata rayuwar bayan jarabtar data faɗa".

Aje wayata nayi na fuskan ce ta dakyau nace "Me kuma ya faru Anty?"
"Babu abin da da ya faru Halima. Ima tunatar dake ne abin da ya kamata ace a shekarun ki kin fahimta amma naga kamar baki sani ba ko kuma kin manta. Shin na tambaye ki Halima, tun da kike ki taɓa ɗaga hannu kin roƙi ubangiji zaɓi cikin tarayyar ki da Bilal kuwa? Kin taɓa yin istikhara kin nemi aga jin ubangiji cikin al'amarin ku?"

Shiru nayi ina kallon ta lokaci ɗaya kuma jiki na yayi sanyi tiɓis. Tayi murmushin tace
"Nasan amsar ki Aa ce"
"Wallahi ina addu'a Anty ke ma ai kin sani" na katse ta se tace
"Ban ce bakya addu'a ba ce miki nayi akan lamarinki da Bilal kina neman zaɓin Allah eh ko a'a shikenan amsar, ko da yake idan ma kina yi ba zaki taɓa fahimtar abin da ake haska miki ba saboda kin ri gada kin sakawa zuciyar ki shi ɗin shine alkhairin naki".

"Wallahi Anty ina addu'a, kullum nayi sallah se nace idan da alkhairi cikin tarayya ta dashi Allah ya tabbatar mana" na faɗa tamkar zan saka mata kuka se tace
"Na yarda. Halima, lokuta da yawa mukan take gaskiya cikin sani mu kai kan mu ga halaka. Muna runtse ido daga gaskiyar da take gabanmu mu ringa hangen gabanta ko bayanta sannan idan an samu aka si muyi kuka muce ƙaddara ce. Tabbas rayuwar mu gaba ɗaya tsararren al'amari ne amma dukkan musulmi ya yarda da tasirin addu'a mun kuma yarda addu'a tana sauya mummunar ƙaddara zuwa kyakykyawa ko kuma ta sassauta muninta.

Ki sani ko da ace kina addu'a muddin a zuciyar ki akwai abin da kika rigada kika ƙudurce shi ne matsayar ki ai ba zaki ma Allah wayo ba. Idan abun Alkhairi ne lafiya lau ubangiji da zuciya yake amfani se ya baki, idan ma ba alkhairi bane tun da har a ranki baki yarda ubangiji ne me bayar wa kuma ya hana ba kika saka wani ƙulli se Allah ya barki da iyawarki, ba zan yi katsalandan cikin al'amarin aure ba domin sirri ne amma zan sake gaya miki ki nemi zaɓin Allah da zuciya ɗaya Halima. Allah ya sani ban ji a jiki na tarayyar ki da Bilal alkhairi bace be kuma nuna wasu alamomi da zasu ƙaryata tunanin mu akan sa ba. Kiyi amfani da ɗan lokacin daya rage miki Halima kiyi tunani kuma kiyi addu'a, kar ki bari so ya rufe miki ido ki kai kanki in da zaki ƙare rayuwarki kina nadama. Cutuwarki bake kaɗai zata shafa ba har da mu dan Allah Halima ki yiwa kan ki gata tun da sauran lokaci ki haƙura da yaron nan. Barin Bilal ba fitar numfashi daga gangar jikin ki bane, kin rayu kafin wanzuwar sa yanzu ma idan ki ka barshi babu abin da ze same me ki se alkhairi Halima. Amma shawara ce ban miki dole ba" Anty Labiba ta ƙarasa maganar muryar ta tana karyewa se ta miƙe tana share hawaye ta shige ɗaki, haka take tana da saurin karaya abu kaɗai ke fito da raunin ta. Na bita da kallo har ta shige ɗaki ta maido da ƙofa kafin na lumshe idanuwa na ina tariyo maganganunta ina kuma fassara su tare da aje kowacce a muhallin daya daveyda ita.

Yanzu aka fara tafiyar.
Shin kun hango sarewa a lamarin Halima kuwa? Zata yarda ta bar Bilal kamar yanda makusantan ta suke fata?
Me nene haƙiƙanin matsayin Halima a gurin Bilal? Shin ya ɗauke ta tamkar yanda ta ɗauke shi ko kuwa dai hasashen da ake mata akan sa gaskiya ne?
Allah shi yasan karatun bebe, haka kuma Allah shi kaɗai yasan gaskiyar dake zuciyar Bilal dan gane da Halima, shin So ne da gaske ko kuwa akwai wata boyayyar manufa da be bayyana?
Ana zaton wuta a maƙera, Bilal fa ze iya bawa maraɗa kunya cikin tafiyar nan ku dai ku kasance tare da alƙalami na domin warwarewar duk wani zato da zargi da yake yawo tsakanin zukatanku.

Domin cigaba da karanta littafin KURA A RUMBU wanda ze zo a manhajar TELEGRAM da Whatsapp(only when subscribers reach 100) ki aika naira 800 kuɗin karatu mallakin mutum ƊAYA zuwa asusun 1840175439
Access Bank, se a tura shaidar biya zuwa 07061838488.
Babu nadama cikin tafiyar nan da yardar Allah. Zamu ilimantu, mu nishaɗantu sannan mu ɗan sha takaici kaɗan.

Albishir, kiyi joining FANS GROUP na KUNGIYAR MARUBUTA MATA ZALLAH domin samun garaɓasar karanta ƙarin pages uku Free 💃🏼💃🏼💃🏼💃🏼
[12/19/2024, 7:55 PM] Hauwa Galadima: KURA A RUMBU
(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)

LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)
Chapter 12 · 0% Book details