Sashe 95
Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Hajja kin fi kowa sanin irin son da nake yiwa Zulaiha amma a haka na haƙura da ita saboda kin nuna bakya so a wancan lokacin, Hajja kin san yarinyar nan bakay buƙatar na sake gaya miki komai akanta aurenta tamkar jahadi ne zanyi saboda na taimaketa kuma idan kika duba tsahon lokacin da muka ɗauka tare tana jira na tun banyi aure ba har kuma nayi auren bata haƙura ba kuma yanzu nace na zan aureta ba ai zai zama kamar na yaudareta ne kuma dama ai Hajja munyi yarjejeniya dake na faɗa miki duk idan na samu dama a gaba zan aureta kuma baki ce ba haka ba".
Kukan da ya fi na farko Hajjan ta sake fashewa dashi shi kuma ya sake laƙwashe murya ya ce
"Hajja kin san bana miki musu duk abinda kika ce ko bana so ina yinsa, dan Allah zan roƙe ki ki mun wannan alfarmar ki barni da Zulaiha, ina sonta nayi miki alƙawari ko me kike so zanyi amma kiyi haƙuri dan Allah kada ki rabani da Zulaiha" ya ƙarasa yana zamowa gabanta ya dafa guiwarta hawayen da yake kokawa dasu suka gangaro akan kuncinsa.
Cikin kuka Hajjan ta shiga cewa
"Yanzu ita wannan yarinyar ya zakayi da ita?"
"Kada ki damu kanki da batun Jalilah Hajja"
"Ba maganar karna damu ba, wlh a kanta zan iya ɓata maka rai Bilal wlh" ta katseshi, sakw marairaicewa yayi ya ruƙo hannunta ya ce
"Haba Hajja yanzu har kin fi son wata bare a kaina kenan?"
"Kai da ka nuna mun iyakata Bilal da raina ban mutu ba ka zagaya ka ɗaura aure har kana da bakin cewa na fifita wani a kanka? Ai ko da bana so har idan dagaske kana martabani a matsayin uwarka ya kamata ka gaya mun, amma shikenan, dama gashinan ƙanin ubanka ya fara cewa ni mai son zuciya ce na saka ka auro waccen yarinyar ga yanda ake ciki yanzu ina so na sake turaka ka auro wata ba'a son ranka ba shiyasa ka zagaya kayi aure baka gaya mun ba, shikenan kaje ba zan hanaka ba amma ba'a son raina ba" ta miƙe tana kuka wiwiwi ta wuce ɗaki.
Gaba ɗaya ji yayi kansa ya kulle dan ko maganar da Kawu Sani ya shiga yi masa sauraronsa kawai yake amma baya gane komai cikin abinda yake faɗa, ƙarshe kawai ya miƙe ya fice daga falon. Auren da take so ta saka albarka a ciki ma ya ya ƙare balle wannan da tace bata so?
Kwanakin da suka biyo baya gaba ɗaya Hajja ta ɗauke masa wuta ko gidan yaje daga sallama bata sake ce masa komai duk kuma magiyar da zaiyi da bata haƙuri ba zata tanka masa ba abin sai ya zame masa goma da ashirin dan yanda ya tsammaci lamarin Halima zai zo masa da sauƙi sai kuma abun ya sha banban. Washe garin daya sake komawa da yamma haka nan ya ƙara ci kiranta a waya amma bata amsa ba daga ƙarshe ma ta kashe layin gaba ɗaya, ya tura mata text duka babu amsa haka ya haƙura ya tafi ga ta ɓangaren Zulaihan itama ba wani sauƙi, fushi ta ɗauka dashi tun akan zancen waccen daren shi ya ƙwafe yana jira ta kira ta bashi haƙuri irin yanda ya saba da Halima amma har aka kwana aka kusan wuni shiru bai ji ta ba.
Haka nan sonta dake azalzalar zuciyarsa ya tilasta masa kiranta kuma ko kafin su shirya sai da ta masa tatas ta amayar da duk abinda yake cikin ta kafin ta kammala da gargaɗi akan karya sake mata irin haka wai kuma abin takaici ba yanda ya iya ya bita da ban haƙuri shikenan suka shirya har a daren yaje gidansu kuma kamar yanda tace tunda ba'a masa gwaninta ta daina nuna masa kulawar hakan ce ta faru dan ƙin yarda ma tayi su zauna a mota sai a soro sukayi zancen.
HALIMA
Ba ƙaramin ƙarfin hali nayi gurin danne zuciyata naƙi amsa Bilal ba, so nakeyi na tabbatar da matsayina a gurin sa, ko da ya tafi zuwansa na farko na ringa ji kamar na kirawo shi na ce ya dawo amma da naga har dare ya tsala safiya tayi bai sake kirana ko tura mun sa saƙo ba sai ba raina kaina na kuma fara tausayin kaina akan igiyar zaton dana ƙulla na cewar Bilal ɗin dagaske yana ta tawa mutane kawai suke ganin ba haka ba. Na ji sanyi har raina daya sake dawowa sai dai kuma ban biyewa zuciyar da ta ringa azalzata akan na karɓi uzurin sa ba. Na tambayi kaina wane uzuri zan masa ne ma tunda shi dai bai furta ko nunawa a aikace cewa ya yarda yayi mun laifi ya kuma nemi da nayi haƙuri ba maimakon haka a kalaman da yake turo mun sunfi kama da wanda yake jaddada mun cewar ya san ba zan iya rayuwa babu shi ba dan haka dole nayi haƙuri na koma masa kuma ko kusa bai ma nemi cewar na bashi dama mu zauna ko zai wanke kansa ba aa kawai cewa yakeyi nazo mu koma gida tabbacin ko a jikinsa ma shi ya manta da duk abinda ya faru.
Ba tareda kowa ya bani shawara ba na yankewa kaina shawarar ɗibar masa lokaci, zanyi ta jansa in ga iya gudun ruwansa. Shin zai fahimci kuskuren sa ya biyo ta sigar daya kamata ko kuwa zai cigaba da yi mun kallon ba zan iya rayuwa babu shi bane?
Na kwanaki huɗuya jera kullum yaje gidanmu daga zarar kuma yayi mun kira ɗaya ba zan bari yayi na biyu ba zan kashe wayar. Na zuba ido naga gudun ruwansa tunda har aka kwana huɗun dai salo ɗaya yake maimaitawa na kirana haɗi da tura mun text yana tunasar dani yanda yake a raina ba wai yanda ni nake a nasa ran ba in dubi wannan nazo mu koma gida. Nasan Mama ta san yana zuwa amma ko da wasa ɓata ce mun komai ba nima kuma ban ce mata ba a haka muka kwana huɗun a yini na biyar shiru tun Magriba nake tsammacin naga kiransa amma har sha biyun dare ta gota shiru babu shi babu labarinsa tils na cire rai sai kuma damuwa da ƙuncin da ban tsammata ba suka lulluɓe ni.
Washe gari haka na tashi sam babu walwala ba fara'a, komai ma baya mun daɗi dan ko abinci ɗan kaɗan na tsakura na ture saboda yanda nakejin komai yana mun ɗaci a bakina. Bini bini zan ɗauki waya in duba ko zan ga saƙon sa ko makamancin haka amma shiru har azahar tayi, bayan na idar da sallah ina zaune kan sallaya ina lazumi wayata ta shiga ƙara, tun da gari ya waye ko message bai shigo mun ba ina jin ƙarar wayar kuwa na zabura zuciyata tana raya mun Bilal ne dai dai lokacin kuma Mama ta shigo ɗakin. Wayar na duba ganin baƙuwar number ya saka zumuɗi na raguwa dukda haka bam cire tsammanin shi bane sai bayan dana kai wayar kunnena bayan na amsa naji murya daban ba tashi ba.
Zare wayar nayi na kashe ba tareda na amsa sallamar da wanda ya kira yayi ba, na saci kallon Mama jin tana cewa
"Iska dai tana wahalar da mai kayan kara" kafin tayi ƙaramin tsaki ta nufi ƙofa tana cewa
"Ga Mudassir can a falo yana jiranki". Jiki ba ƙwari na biyo bayanta, bayan mun gaisa da Uncle Mudassir ya tambayeni jiki na ya ce
"Na ɗauka kin karɓo posting letter ki Halima tuntuni ashe baki je ba". Ɗan ya mutsa fuska nayi na ce
"Uncle ba fa ni da lafiya, kuma ni ban ma san an fito daga camp ɗin ba". Daƙuwa yayi mun yana cewa
"Dan gidanku ni kike gayawa baki da lafiya tun yaushe kika samu sauƙi yau kwananki nawa da aka sallamoki daga Asibiti? Naga alamar har yanzu baki san inda yake miki ciwo ba Halima, satinki nawa a gidan nan? Ke ko ji bakiyi zaman ya isheki ba kina buƙatar samun abun da zai ɗebe miki kewa ko kuwa dai saboda kanki aka fara mutuwar aure shikenan sai ki zauna ki lalata rayuwarki a banza ba zaki gyara gobenki ba?"
Da sauri na kalle shi jin abinda ya faɗa na ce
"Ni fa Uncle aure na bai mutu ba". Ina kallo Mama ta jijjiga kai irin na zallar takaici shi kuma ya ce
"Oh har kina da bakin cewa aurenki bai mutu ba? Toh zaman uban me takeyi kusan wata biyu a gida?" Ya ƙarasa yana kallon Mama. Hannu biyu ta watsa ta ce
"Gaka gata ƙila kai tunda tana ganin kanka da gashi ta gaya maka zaman me takeyi tunda mu da ta raina ba yanda bamuyi ta girma da laluma ta faɗa mana mai ya faru ta taho gidan ba amma tace babu komai"
"Aa wannan kuma laifinku ne Anty, ai ƙarya ne wlh yarinya ta taho gida sama da wata ba wani ƙwaƙƙwaran dalili ni duk ɗauka ta ya saketa ne kuma abinda yasa kika ga ban ko yi miki maganar ba saboda naga babu amfani ne ko yanzun LGI ɗin ne ya kirani dan tuni an turo da relocation list har anyi posting nasu dake nayi masa maganar ta da in da nake so a kaita ya kirani akan bafa ta je ba har yanzu shiyasa ma kika ganni yanzu. Kuma shi Yaya Aminun ya zuba muku ido take ta zama bai ce komai ba?"
"Toh mai zai ce Mudan? Ita me auren an tambayeta tace babu komai shi kuma bai biyo baya ba haka babu wani nasa da yazo toh ta ina zamu san meya faru?" Mama ta sake faɗa, ni dai kaina yana ƙasa ina jinza ya kira sunana na sake sadda kai ƙasa sai da ya buga mun tsawa kafin na ɗago da sauri ya nuna ni yana cewa