← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 158

Sashe 122

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Daga nesa ya hango amaren sun fito daga wani gida, Nuratu kallo ɗaya ya mata kuma ko kaffara ba zaiyi ba ya san Faruk ne ya ɗinka mata leshin jikinta daga zubinsa har ɗinki ya san ba siyayyar waccen matar da Zulaihan ta ringa cewa wai ta san gayu da ita suka so siyayyar lefenta bane abin baƙin ciki tasa amaryar ko da daga nesa yake hango su atamfar data saka da aka yiwa wani ɗan iskan ɗinki da ko a mafarki ba zai yarda Zulaiha zata saka irinsa ta fita ba kallo ɗaya ya mata ya fahimci roba ce ko ma leda.

Cikin fushi ya taka mota ya bar gurin yana gani kuma ta ringa kiransa amma yaƙi amsawa ƙarshe ya kashe wayar ya wuce hotel ɗin daya kama tun da aka kashe kayan Halima.

Bayan sallar isha'i aka kai Amarya, gidan Hajja suka fara zuwa da ita abun dai ba girma balle arziƙi ko ɗan abincin da akeyi na yan kawo amarya hanawa tayi a basu balle kuɗin siyan baki haka suka wuce suna zagin Hajjan aka garzaya da ita gidan Bilal.

Yan kawo Amarya dai sukayi ta santin gida domin a gurinsu Zulai fa tayi goshi. Dama kuma ai gida da kyansa kuma ko kayan da aka saka a ciki sunyi kyau kawai dan an saba ganin wanda suka fi su ne shiyasa yake ganin gurin bai yi masa yanda yake so ba.

Da suka ga Bilal ɗin da gaske yake ba zai ƙara komai a gidan ba kamar yanda ya ce dole safiyar Asabar ɗin suka yanko labulayen da su Fadila suka ce tsofaffi ne aka kafa, ya dai fi babu dukda basu wadaci gurin ba a winduna biyu kawai suka saka da yake kuma an saba ganin gurin cike da labulaye sai yayi haske fayau yan uwansa suka ringa taɓe baki suna kallon gurin babu wannan haɗaɗɗun kujerun da carpet na alfarma da frames da aka ƙawata bango dasu balle Cinema TV irin ta Halima haka suka bar gurin ga dai Tv stand da yake haɗe da kujerun da Center table amma ko center carpet babu alamar sun kawo tunda ko da ba'a shimfiɗawa saboda kar a tattake yayi datti amma dai ana ajiyewa a gefe yanda kowa zai san dashi.

Dama kulle kitchen sukayi sai kace wani abin arziƙi suka zuba ta window wanda suka sawa ransu sai sun ga komai suka ringa leƙawa. Haka aka watse yan uwan Bilal suka tafi da gulma ana ta yi masa Allah ya ƙara. Kowa cewa yake da matarsa ta rufin asiri kuga jarabar daya kwaso wannan amarya kana kallon idonta kasan kunya bata isheta ba amma maganin Hajja kenan har da shi kansa ɗin dama kuma ai haƙƙin Halima baiwar Allah ba zai barsu ba.

Wanda ma basu san Haliman bata nan ba lokacin suka sani anan kuma labarin sakin ya fita amma su Fadila suka ringa ƙaryatawa suka ce tana dai gidansu tayi yaji amma bai saketa ba Huwaila wacce take auren Kawun Halima a Galadanci kuma ta ce aure fa babu shi dan taji labari a cikin gida an ce saki biyu ma ya mata ga kuma babbar shaida har ya saka wata a gidan idan yaji kawai tayi ai ba zata kwashe kaya ba balle a saka wata matar a ɗakinta.

Sai gurin sha ɗaya kafin ya shiga gidan dan a yanda ya wuni cikin ɓacin rai ji ya ringayi ma kamar karya koma amma daga ƙarshe dai ya tattara ya tafi babu rakiyar aboki ko ɗaya ya shiga gidan bayan ya tsaya ya siya mata tsire da yoghurt sai lemuka dan sanda ya je gurin mai naman kaza ta ƙare shi kuma ya gaji bai ji zai iya tafiya wani guri nemo mata kaza ba.

Tsakar gidan kaca kaca kamar anyi yaƙi, ga ƙofar falon a buɗe sai uban hayaniyar ƙawayenta da yake jiyowa mamaki ya kamashi har sai da ya duba agogon hannunsa sha ɗaya har da rabi ta gota, basu da hankali ne? Ko a gidan suke nufin zasu kwana da har suka kai wannan lokacin?

A waje ya bar motar ya shiga ya ɗauki tsintsiya ya fara share gurin dan ba zai iya kwanciya bacci gidansa da wannan bolar ba kuma ya ajiye motarsa a ciki, ya gama ya jona mesa a famfo ya hau wanke gurin a ransa yana ayyana yau zaiga ƙarshe haukan ƙawayen Zulaihan da ita kanta. Yana wanke gurin suka fara fitowa harda ita duk sukayi turus suna kallonsa, wata mai shegen kauɗi ta ce

"Dama na ce muku naji an buɗe get kuka ce babu wanda ya shigo ai". Bai ko kalle su ba ya cigaba da abinda yakeyi sai da ya ji muryar Zulaihan cikin fushi tana cewa

"Yanzu tsabar wulaƙanci ka shigo gidan kana jin ƙawaye na kuma ka san ku suke jira amma ba zaka iya shigowa ku gaisa ka sallame su ba shine zaka hau wani aiki sai kace boyi boyi?"

Kallo ɗaya ya mata ya wuce ya kashe famfo dan ya gama abinda yakeyi. Gurin ya masa yanda yake so dukda hancinsa yana jiyo masa wari wanda ya tabbatar daga banɗaki dake tsakar gidan ne amma yanzu ya gaji sai da asuba zai bi ta kansa. Fita yayi zai shigo da mota ya hango masu gadi sun tsayar da wasu motoci biyu sun hana su shiga layin suna ganinsa Iliya ya nufe shi Basiru kuwa ɗauke kai yayi sama dan ko yanzu da zai shigo a wanda ya ce masa komai a cikin su tun ma waccen ranar idan ma basu ga dama ba wani lokacin sai yayi ta horn kafin zasu buɗe masa ya fita ko ya shiga layin.

"Wai yammatan da suka kawo amarya zasu ɗauka" Ilyas ɗin ya faɗawa Bilal, sai ya koma ciki ba tareda ya ce masa komai ba suna tsaye curko curko murya kamar wanda aka cusawa tsumma a baki ya ce
"Ana jiranku a waje" ya juya abunsa.

"Lallai ma Bilal, wato wulaƙanci ka tasarma yi mun a daren nan kana nufin ba zaka basu kuɗin siyan baki ba ko me?" Zulaiha ta buɗe murya bata ko duba dare ba balle kasancewarta amarya, ƙawarta Suwaiba da suke kira Suby ce ta jata suka koma cikin falo ta ce

"Ke fa banza ce Zulaiha, so kike ki ruguzawa kanki shiri kenan a wannan daren? To wlh kibi a hankali karki tunzura shi ki ɓallowa kanki ruwa bayan kin san dama a ruwan kike"

Tsaki Zulaiha tayi ta ce
"Kin san bana ciki da abu ta kazan uba, na gaji da pretending wlh gara in warware masa tun wuri ya shiga hankalinsa ya kuma kama kansa"

"Ai sai ki bada himma, ni ba wannan ba kin dai saka abun nan ko?" Suby ta sake faɗa ta kuma yin tsaki ta ce
"Na saka mana"
"Toh asha amarci lafiya karki manta kuma ki rage mana kaza dan da wuri zamu zo" suka tafa kafin suka fito lokacin sauran har sun fita Bilal ya shigo da mota yana ƙoƙarin rufe gida da muƙulli. Harda rusunawa Suby tayi ta gaishe shi amma bai ko kalleta ba ya buɗe ƙofa ta fita ya mayar ya rufe. Kai tsaye ɗakin sa ya wuce bayan ya shiga falon da ba ya ko son ganinsa a yanzu ya zube mata ledojin daya shigo dasu.

Zulaiha kuwa dama ɗaki ta wuce abunta ta fara shiri a ranta tana ayyana yanda zata ci kan uwarsa a faɗarta tunda ya rigada ya zo hannu zai san bashida wayo. Ta gama shiri ta fito falon ta zauna tana ƙarewa gurin kallo tana tsaki, da ta san ba zai saki jiki ya mata irin jeren data zata ba wlh da bata biyewa Umma ba kuɗi zata cire tawa kanta abu na birgewa tunda tana da shi. Tsaki ta kuma ja mai ƙarfi, sai lokacin ta lura ashe ko Tv ba'a saka mata ba. Wayarta ta buɗe ta lalubo wata number babu fargaba balle tsoron komai ta danna kira kamar mai wayar kuwa yana jira ya ɗaga daga can ya ce

"My baby, irin wannan kiran ba zata haka kamar kin san kewarki ce ta hanani bacci wlh"

"Ƙaryar banza, to karka manta dai matar aurece ni yanzu kuma ba shashanci na kira muyi ba" ta faɗa a wani dake, daga can ya sheƙe da dariya ya ce

"Su matar aure manya, to ina angon naki kike waya ƙarfe sha biyun dare?"

"Tv nake so" ta faɗa masa dalilin kiran ya tambayeta inchi nawa ta faɗa masa bata bari ya ja hirar kamar yanda ya so ba ta katse bayan ta gaya masa da safe Suby zataje ta karɓa ta taho mata d ita idan zasu zo.

"Ina son fridge da cooker gas ma amma su ba gobe ba sai an kwana biyu" ta sake faɗa yayi ƙasa da murya cikin barikanci ya ce

"Wannan sai kin kawo mun ziyara tukunna sai ki zaɓi waɗanda kike so ki tafi da su".

Motsin taɓa ƙofa ya sa tayi saurin katse wayar ta kasheta gaba ɗaya ma ta gyara zama yanda tayi kuma ba zaka taɓa hasaso alamun rashin gaskiya ko wani abu a tattare da ita ba.

Bilal ya samu guri ya zauna kamar mara lafiya yana kallonta, ya rasa abinda ya sa ya kasa jurewa ya zo, sonta yake kamar rai can ƙasan zuciyarta yana raya masa ya shareta amma ya kasa har ya kwanta haka ya taso ya taho wai yaga taci abin da ya ajiye mata ko bata ci ba?

Murya ba amo ya ce
"Kinci abincin ne?"
"Ka bani ne?" Ta mayar masa da tambaya tana wani tsare shi da ido, a ransa ya shiga karanta a'uziyya yana ayyana mutanen nata ne suka motsa kenan. Ya matsa ya shiga ware ledojin, ta kayan tea sai lemukan da har sun fara hucewa tsiren ma yayi sanyi ya buɗe mata yana cewa

"Bismillah, ba'a samu kaza bane sai wannan".

Sai da tayi dagaske kafin ta danne ashar ɗin data taho bakinta, tsire za'a kawo mata a siyan baki?
Chapter 122 · 0% Book details