← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 158

Sashe 79

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sallah nayi raka'a biyu kafin na ɗauki alƙur'ani da tsakani da Allah na kwana biyu banyi karatu da shi ba. Badan bana karatun alƙur'ani ba aa, na kan yi tilawar surorin dana haddace ko nayi amfani da wayata musamman idan zan tisawa Al'amin karatu. Ni da kaina naji nutsuwa sosai a ruhi da gangar jikina zullumin daya cika mun zuciya akan me Bilal yake a waya da yake ɓoye mun ina fara karatun ya barni. Sai da aka kira sallah kafin ya fito ya wuce masallaci daya dawo ina lura da yanda ya kame fuska ta yuwu yayi zaton zan masa maganar waya da kuma yaji banyi ba har na shirya Al'amin zan fita kaishi makaranta yace na bari zai kaishi suka fita harda Sharifa kafin su dawo nayi maza nayi wanka nayi kwalliya.

Bayan mun karya ya ce mun ranar Alhamis zai tafi Abuja kuma zai iya yin sati ɗaya zuwa kwana goma acan ɗin.
"Anty Sa'ada bata da lafiya ɗazu dana fita mukayi waya da Hajja take gayamun har an kwantar da ita a Asibiti jiyan dan haka Fadila zata tafi can ta zauna da ita kafin ta samu sauƙi" ya faɗa. Cikin fuskar jimami na ce

"Allah sarki Allah ya bata lafiya shiyasa bata zo duba Hajja ba ashe" ya amsa da Amin kafin ya ce
"Kinga idan Fadila ta tafi gidan zai zama babu kowa sai Abubakar kuma itama Hajjan jikinta ga yanda yake kusan komai sai an taimaka mata takeyi saboda ciwon ƙafarta"

"Abinda zanyi magana kenan dama nace toh Hajja fa idan Fadila ta tafi tunda itama tana da buƙatar ta" na faɗa, ya goge hannunsa da tissue kafin ya ce
"Na gaya mata zata dawo nan gidan ta zauna kafin Fadilan ta dawo".
[4/2, 8:52 AM] Hauwa Galadima: *KURA A RUMBU*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 08142548705* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 33*

Banji komai dangane zaman da ya ce Hajja zatayi ba dukda nasan ba jituwa mukeyi da ita ba amma kuma abinda yake so ne kuma wanda zai faranta masa ni kuma burina a koda yaushe kenan. Har ya fita ya kirani a waya yace na shirya gashi nan dawowa zamu fita tare, da nace masa Al'amin fa kar lokacin tashin su yayi bana nan sai ya ce ai ba jimawa zamuyi ba dan haka nayi maza na canza kayana na shirya Sharifa ina jin horn ɗin mota na fita. Raina fes na kame a gaban mota ina jin wani farinciki na ratsani.

Na daɗe ina hakaito irin haka nida Bilal ɗina mu ringa zagaya gari a mota nasan duk inda muka gilma sai an kallemu an kuma yaba dacewar mu dan sau tari na sha yin yunƙurin yiwa Abba magana akan ya siyamun mota sai kuma na kasa toh gashi lokaci yayi ya mallaka da kuɗin sa ma. Murmushi nayi ina kallon yanda yake murza sitiyari yayi irin zaman nan na yan birni sai ya ƙara kyau haɗi da kwarjini a idona. Na ƙara rungume Sharifa da ta fara bacci kafin na karyar da murya na ce

"To yanzu yaushe zaka fara koyamun mota?" Yi yayi tamkar nai ji ni ba har saida na sake maimaitawa kafin ya mun gajeran kallo haɗi da murmushi ya ce
"Ke da kika tashi gidanku cike da motoci har kyace baki iya tuƙi ba?"

"Idan da na iya ai tuntuni zaka sani" na bashi amsa ina kallonsa, sai ya ɗan taɓe baki ya ce
"Shiyasa ba'a haɗo miki da mota a gara ba kenan ko a siya miki daga baya". Yanda yayi maganar ya saka nayi shiru ba tareda na sake cewa komai ba tun kafin hirar ta canza akala zuwa abinda zai haddasa mana ɓacin rai. Ban sake crwa komai ba shima haka har muka isa Unguwar su Anty Labiba, sai da muka gota gidanta kafin murnar da na farayi ta koma ciki dan na ɗauka bazata zaiyi mun yau dai muje gidanta da ni da shi. Layin daya koma bayan su ya shiga na kalle shi na ce

"Na ɗauka gidan Anty Labiba zamuje" ba tareda ya kalleni ba yana ƙoƙarin tsayar da motar a ƙofar wani madaidaicin gida na masu rufin asiri ya ce
"Ai saiki sauke". Ban fita daga motar ba bayan ya sauka sai da ya mun magana dan ban san ina muka zo ba balle nayi garajen fita, ina tsaye ina ƙarewa layin kallo, duk gidajen gurin ƙanana ne na masu ƙaramin ƙarfi ba kamar can kan layin su Anty Labiban ba. Kofar wani gida mai ɗan dama dama akan sauran ya nuna na rufa masa baya, ya jera sallama sau biyu kafin daga ciki aka amsa tareda bayar da izinin shiga sannan ya shiga na bishi a baya ina ƙarewa gidan kallo.

Ƙaramin gida ne dan gaba ɗaya ɗakuna uku ne a ciki falle falle sai banɗaki da kitchen duka a tsakar gidan da rijiya amma tun daga waje zaka yabawa tsaftar mazauna cikinsa domin hatta da kwatar su tsaf take an yasheta haka tsakar gidan daya sha fasassun tiles tsaf yake babu ko tsinke banda tabarmar da wata mata mai matsakaicin jiki take zaune sanye da hijabi tana jan carbi da alama sallar walaha ta idar.

Cikin fara'a ta shiga yi mana maraba, na zauna gefen tabarmar Bilal kuma yaja kujerar tsugunno dake gefenta ya zauna yana sunne kai tamkar wanda yake a gaban surukai.
"Sannunku da zuwa" ta sake nanatawa cikin fara'a na gaisheta ta amsa tana jan Sharifa amma taƙi zuwa Bilal ma ya gaisheta haɗi da tambayarta ya ƙarin haƙuri hakan ya saka nima nabi bakinsa nayi gaisuwar dukda bani da masaniyar mace ce ko namiji ma wanda ya rasun.

Tashi tayi ta kawo mana ruwan pure water da biscuit ta bawa Sharifa, bayan ta zauna ta ce
"Amma bata san da zuwanka dan bata yi zancen ba kuma yanzun nan basu ma jima da fita ba". Ji nayi ƙirji na ya buga ras na ɗaga kai na kalli Bilal da cikin sa'a muka haɗa ido shima ni yake kallo kafin ya ɗauke idonsa ya bata amsa da cewa
"Eh ban gaya mata zanzo ba gaskiya munyo ta nan haka ne nace bari mu ƙaraso Halima tayi muku gaisuwa".

"Allah sarki aikuwa mungode Allah ya bada lada" ta faɗa ya amsa da amin ni dai ina sauraron su cikin kaina kuma ina ƙoƙarin tantance wacece itan da suke magana akai?
Shiru ya gifta na kusan minti biyu shi kansa yana ƙasa sai ita matar dake jan Sharifa da har sannan taƙi yarda da ita sai ya miƙe yana laluba aljihun sa yace
"Bari mu wuce Umma"
"Har zaku tafi?" Ta faɗa, na miƙe nima sai itama ta miƙe tsaye tana cewa
"Shikenan toh ku gaida gida Halima nagode Allah yayi albarka na amsa da "Amin" ina yin gaba. Ta gefen ido naga ya duƙa ya ajiye mata kuɗin da ban san ko nawa bane na ƙarasa ficewa ina jiyota tana ta jera masa addu'oi, na jingina da jikin mota ina sauraron fitowarsa gaba ɗaya kaina ya cika da tunanin nan ɗin ina ne dan dai ban taɓa ganin matar ba balle nace danginsu ce kai ko a labari bai ma taɓa cemun suna da yan uwa a nan unguwar ba dan da ace yar uwarsu ce tun sanda yake zuwa hira gurina gidan Anty Labiba zan san da zamansu.

Sai da ya ƙara kusan minti biyar ina hangosu tsaye a soro suna magana kafin ya fito yana wani ɗauke kai kamar baya so mu haɗa ido ya buɗe motar muka shiga, ban ce masa ƙala ba har saida naga yana ƙoƙarin sake wuce gidan Anty Labiba kafin na ce
"Amma na ɗauka zamu shiga ai ko a tsaye ne mu gaisheta".

"Sauri nakeyi zan wuce gurin aiki" ya bani amsa sai nayi saurin cewa
"Sai kayi tafiyarka idan mun gama mu wuce gida"
"Shi kuma Al'amin ɗin wa kika barwa shi?" Ya sakw faɗa cikin tsare gida, zan sake magana ya ce
"Da Allah ki kyaleni in kin shirya zuwa ki saka rana kije amma yanzu babu inda zaki shiga". Haushi yasa ban sake ce masa komai ba, ƙarin takaici na ɗauka gida zai mayar damu da ya hanani shiga gidan nata amma sai gani nayi ya faka a junction ya zaro dubu ɗaya daga aljihun sa ya miƙa mun, ina kallonsa ya cilla kan mota yayi gaba abinsa bayan mun sauka haka na tare Adaidaita muka wuce gida.

Yinin ranar da tunanin gidan da mukaje na yi shi, bai dawo da wuri na sai bayan sallar isha'i ya taho da jakar kayan Hajja da wasu abubuwan buƙatarta. A ɗaki na ajiye mata kayan, saida ya zauna cin abinci na kasa daure tunanin daya addabeni na ce masa
"Ni kam gidan su waye mukaje ɗazu ne?".

Yi yayi kamar baijin ba ni kuma na sake maimaitawa, ya wani haɗe rai ya ce
"Gidan Umma Zaliha ne ƙawar Hajja ce mijinta ya rasu sati biyu kenan". Kwata kwata ƙwaƙwalwata bata kama maganar ba musamman a yanda ya wani tsare gida kamar mara gaskiya, nima haɗe fuska nayi nace
"Wannan ɗin ce ƙawar Hajja matar da daga ganinta ba zata wuce sa'ar Anty Amina ba ma idan ma zata girmeta da kaɗan ne"

"Ƙarya na miki kenan?" Ya faɗa yana aje cokalin da yake cin abinci, na kalli gefe na ce
"Ni bance ƙarya kayi mun ba amma kuma nasan ba gaskiya ka faɗa ba tunda kake zuwa unguwar gurina ya akayi baka taɓa faɗa mun akwai ƙawar Hajja a gurin ba sai yau"
Chapter 79 · 0% Book details