← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 158

Sashe 91

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yau ɗin ma ni kaɗai ce a gidan Mama sun fita tareda Zainab da Sharifa dubo Inaayan Anty Labiba da bata da lafiya. Har na shirya zan bisu kuma kawai na fasa dan na san gidan nata ba zai rasa yan dubiya dan dangin Mijinta nasa raina abun taro ciwon kai wani yayi har idan sun samu labari haka zasu yo ƙungiya suzo a wuni ana cecekuce.

Waya ta dake gefe ta ɗauki ƙara, sunan Suhaila da na gani yana yawo ya saka na janyota na amsa da ƙaramar sallama. Daga can ɓangaren tace
"Ashe bacci kukeyi tun ɗazu ina ta buga ƙofa na ɗauka ma ko bakya nan". Na ɗan yi shiru kafin na fahimci abinda take nufi can gidana taje dan haka nace mata

"Ai kuwa dai bana nan wlh"
"Subhanallahi, dama Honey ya mun baki yace na kiraki kar nazo bakya nan gashi kuwa, idan ba nisa kikayi ba sai in jira ki dan wuni nazo miki yau" ta sake faɗa a ƙoƙarin ta ƙyaleni ta tafi sai na ce

"Ai kuwa nayi nisa ina can gidanmu wlh" na ajiye wayar bayan da tace mun "toh shikenan".
Tunani na tafi bayan na ajiye wayar shin Mijinta bai faɗa mata bana gidan bane ko kuwa shima bai sani ba? Amma dai da wahala yanda suke da Bilal ace bai sani ba dukda dai Aisha Matar Nasir ma ba'a fi kwana uku ba ta kirani tana tambayar ina gida ne zata zo nace mata Aa, ƙila bai faɗawa abokanan sa ba ko kuma ya faɗa musu matayen nasu ne basu faɗawa ba oho musu dai.

Jin an fara shirin shiga sallah da yake juma'a ce ya saka na miƙe na ɗauro alwala domin dai yanzu Alhamdulillah na hau saiti ina matuƙar ƙoƙari gurin dai daita ibadah ta da kuma yinta akan kari, ina raka'ar ƙarshe na jiyo sallamar Suraj daga falo, sai da na sallame kafin na fito har sannan kuma yana tsaye ya ce mun wai nayi baƙuwa tana waje amma basu buɗe mata get ba dan basu santa ba gashi kuma ni kaɗai ce a gidan sun ce ta kira ni a waya tana ta kira ban ɗaga ba. Wayar na ɗauko naga Suhaila ce ta kira har sau huɗu nace ya buɗe mata ta shigo dukda nayi mamaki ban zaci zata ce zata biyo ni nan ba.

Sai da na kawo mata ruwa na koma na zubo mana abinci kafin na zauna muka sake gaisawa tana kallo na tace
"Amma kinyi rashin lafiya Maman Dady?"
Nayi ɗan murmushi kawai ba tareda nace komai ba ita ɗin ma sakin maganar tayi ta kamo wata, bata bar gidan ba sai bayan la'asar har sannan kuma su Mama basu tafi ba sai na ringajin kamar kar ta tafi dan sosai kuma naji daɗin zuwanta dan Suhaila akwai hira, muna tsaye jikin motarta bayan dana rakata waje ta kalleni tace

"Kinga zan manta Honey yace idan mun haɗu da Bilal in ce yana gaishe shi kuma Allah ya bashi haƙuri idan laifi yayi masa haka da ya share shiz toh na bar miki sallahu tunda bamu haɗu ba" daga haka taja motarta ina tsaye harta fice daga gidan kafin na koma ciki raina cike da tunanin sallahun data bar mun. Yanda Bilal ya ɗaukaka Hafiz mai zai saka ace har yana cigiyarsa a gurina? Naga kusan kullum suna tare idan ba a office ba Bilal ɗin ze je can gidansa ko gurin siyar da motocinsa, na taɓe baki a fili na ce
"Sun fi kusa" daga haka na shiga tattare gurin da muka zauna bayan na gama na shiga kitchen na fara ƙoƙarin ɗora abincin dare ganin yamma tayi har sannan kuma basu dawo ba.

Ranar Juma'a ta kama sadakar Arba'in ɗin Mahaifinsu Zulaiha a ranar kuma kamar yanda kawunsu yayi alƙawari bayan an sakko daga masallaci ɗaiɗaikun mutane suka shaid ɗaurin auren Bilal da Zulaiha sai kuma Nuratu da Zahraddini angonga. A zauren gidansu aka ɗaura auren cikin mutanen da suka halarta kuma mutum biyu ne daga ɓangaren Bilal, Kawu Sani sai Baba Mudan shima kawunsu ne abokanan wasa suke da Kawu Sanin da kuna mahaifinsu Bilal. Shi kaɗai Kawu Sanin ya kira ya shaida masa komai suka tafi tare, basu baro gidansu Zulaihan ba sai ƙarfe biyar da wani abu saboda Kawunta daya tsayar dasu da waliyyan ɗaya angon ya nemi tayar musu da sabuwar rigima akan shi fa sai dai azo a ɗauke amare a yau ɗin domin bai ga dalilin da zai saka a ɗaura aure kuma a bar yara su cigaba da zama a gida ba. Daga Kawu Sanin har waɗancan waliyyan angon su kuma suka ce basu san zance ba domin aure yace azo a ɗaura kuma sunzo yara kuma basu gama gyara in da zasu ajiye mata ba idan da yasan haka ne sai ya bari ayi komai a nutse ba yanzu ya sake cewa zaiyi musu titsiye tofa sai a warware auren can ya aura musu duk wanda yaga dama tunda abun nasa kuma ya zama da ɗiban albarka.

Kamar hatsaniya zata kaure har saida matan cikin gida dangin Mamansu da da wata yayar Babansu suka fito ita ta tsawatarwa ƙanin nata ta basu haƙuri kafin suka watse kowa ya fito a fusace. Kawu Sani ya kalli Baba Mudan ya ce
"Anya Mudansiru mutanen nan na kirki ne kuwa? kaga fa yanda mutumin nan yake zare mana ido kamar wasu yayansa yana faɗa mana maganganu, ni wlh shaf na sha'afa na tambayi yaron nan ya ma yi bincike da kyau akan asalin yarinyar ko kuwa dan ni kwatancen da ya mun sai da muka zo naga ashe ba Sulaimanun da nake zato bane Babannasu". Baba Mudan yaja numfashi ya ce

"Gaskiya dai wannan ƙanin uban nasu ba za'a kwashe da daɗi dashi ba mutum ba lafazi ba magana mai daɗi wai mu muka sani idan ma sama zamu kai su shi dai a kwashe masa yara daga gida ya dena ganinsu ni wlh sai naga ma kamar ba cikakkun hausawa ba ƙirar jikinsu tafi kama data gwarawa". Haka suka cigaba da tattaunawa har suka ɓullo layin su Anty Labiba, a ƙofar gidan suka ci karo da Mama suna shirin shiga mota Anty Labiba na jikin get ta rako su. Maman ta gane shi tsaf saboda shi ya ringa zarya lokacin auren Halima da Bilal, suna haɗa ido kamar mara gaskiya yayi saurin ɗauke kai gefe kamar bai ganeta ba harda ƙara sauri suka wuce.

Anty Labiba da taga ta bisu da kallo ta tambayeta ko ta sanshi ne ta ce
"Surukin Halima ne ƙanin Babansu Bilal shi yayi masa walicci ma", Anty Labiba ta saki wani murmushi haɗi da girgiza kai tace
"Allah sarki, ƙila bai ganeki bane" Maman ta bata amsa da cewa
"Da alama" sannan ta buɗe mota ta shiga, Anty Labiba ta zura kai ta window tace mata

"Wai ya kuwa zo Bilal ɗin ko har yanzu?"
"Ina fa yazo Labiba?" Mama ta bata amsa sai ta taɓe baki tace
"Toh Allah ya rufa asiri bari na koma kar su ce na barsu su kaɗai" daga haka ta koma cikin gida Mu'azzam ya tayar da mota suka wuce.

Sanda suka dawo har na sauke jollop ɗin shinkafar da nayiz naji daɗi sosai yanda Mama ta nuna jin daɗin girkin da nayi, a daren har hira mukayi na gaya mata zuwan Suhaila, ina so in mata zancen Hafiz da yake cigiyar Bilal kuma naji tsoro kar na ɓata ɗan shirin da muka fara sai kawai nayi shiru.

A ɓangaren Bilal kuwa wunin Juma'ar cur kashe wayarsa yayi yana kuma gida sallar Juma'a kawai ya fita ana idarwa kuma ya dawo ya sake kulle ƙofa, sanda Suhaila taje ma yana ji har ta gama bugu ta haƙura ta tafi ya ɗauka matan unguwar ne masu zuwa gulma da sunan tambayar ko Halima ta dawo shiyasa ko za'a fasa ƙofar saboda bugu yana ciki ba zai taɓa amsawa ba balle ya buɗe. Shi yanzu ko mazan layin ma ba duka yake gaisawa dasu ba, sai kace akansa aka fara samun saɓani da mace har tayi yaji kowa da dogon bakinsa sai ya tare shi yace zai masa faɗa wai bai kyauta ba ganin suna nema su raina masa wayau ya saka ya dena tsayawa idan zai fita a mota glass ɗin sa a sama haka idan ya dawo in kuwa tafiyar ƙafa ce ko zuwa masallaci nan ma zai haɗe fuska ta yanda ko ka masa magana zaiyi kamar bai ji ba ya share.

Yau ɗin ma sai da akayi magriba kafin yayi wanka ya shirya cikin wata sabuwar shadda yayi kyau sosai kuwa ya hau mota ya fito. Jin sa yake kamar wani sabon mutum musamman daya kunna wayar sa saƙon Kawu Sani ya shigo yana sanar masa an ɗaura aure idan ya kunna wayarsa kuma ya kira shi ko kuma yaje gida ya same shi, itama Zulaihan ta yiwo masa text mai nuna zallar farin cikin ganin wannan rana a rayuwarta da kuma ƙorafin rashin halartarsa gurin ɗaurin auren.

Gidan Kawu Sanin ya fara zuwa, a waje suka haɗu zai tafi sallar isha'i dan haka suka wuce masallacin tare sai bayan da aka idar kafin suka keɓe Kawu Sani na kallon sa yace
"Munje an ɗauro aure amma fa wannan Kawun nata yaso ya mana hauka wai sai mu jira mu taho da ita su ba za'a bar musu ya a gida ba bayan an ɗaura mata aure".

Ido ya buɗe da mamaki kafin ya ce
"Sai kuka ce masa me Kawu?"
"Mai zamu ce masa kuwa? Muma buɗe masa ido mukayi tunda munga abinda yafi ganewa kenan dan waliyyin ɗaya yaron ma cewa yayi sai a warware auren tunda abun nasa ya zama da iya shege a ciki idan yaso in an shirya gaba ɗaya sai a dawo ayi". Bilal ya shafa kai yana murmushi Kawu Sani ya cigaba da cewa
Chapter 91 · 0% Book details