← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 158

Sashe 22

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Dake su Imam da Amirah harda Inayah d Amir ɗin Anty Labiba sun zo tare muka wuni muna ta sabgogi se la'asar Mu'azzam ya zo ya ɗauke su, na basu kilishin da na taho dashi jiya daga gida su kaiwa Anty Labiba tun da nasan tana so kuma Mu'azzam yace su ze fara saukewa a gida bayan sun tafi na hau gyaran gida kafin wani lokaci na gama komi nayi wanka, ina da miya dan haka couscous zan dafawa Bilal idan sun dawo.
Dab da sallar isha'i ya shigo gida, se da na haɗa masa ruwan wanka na fitar masa da duk abin da ze yi amfani dashi kafin na barshi a ɗaki na koma kitchen na ƙarasa haɗa abinci. Har da fruit salad nayi dan nasan shi daga zarar an ci abincin dare ze fara mitar bakin sa na masa motsi yana so yaci wani abu kuma ya gaji da cin kayan gara. Mun cin abincin yana mun hirar yanda ɗaurin aure ya kasance, ashe mota ce ta lalace musu a hanya shiyasa ma sukayi dare. Bayan mun gama na kwashe koma na kai kitchen sannan na dawo na zauna akan cinyarsa ina jan gashin gemun sa, ya ɗora kan sa a kan ciki na yana cewa
"Har yanzu baki fara jin komai a nan bane?" Dariya nayi na ture shi ina cewa
"Haba sarkin kazallaha, 2 weeks fa yau me zan fara ji?"
"Ki dai zauna wasa yarinya ni nasan na daɗe da yin aika aika". Haka muka ringa hira cikin nishaɗi haɗi da wasannin soyayya. Ƙarfe goma yace mun na kawo masa wani abun ya ɗan taɓa bakin sa na masa motsi, se na ɗakko fruit salad ɗin da na sakawa madarar gari da condensed gashi yayi sanyi gwanin daɗi na haɗo da ruwa.

Se da ya fara shan fruit salad ɗin kafin ya ce na kawo masa kilishi.
"Ai ko ɗazu na bawa su Inayah su kaiwa Anty Labiba na san ta da son kilishi" na bashi amsa, se naga ya dakata da abin da yakeyi ya wani kalle ni fuskar sa kamar da fushi yace
"Kilishin kika bayar? Da izinin wa? Wato ita gata sarkin son cin kilishi ni kuma da bansan daɗi ba shiyasa zaki ɗauke mun abu ki bayar na tare da nayi miki izini ba".

Mamaki maganganun sa suka bani, kilishin da a gidan mu aka bani dan nayi kyautar sa shine ze fara tada jijiyar wuya yana faɗar maganganu akai? Kai tsaye nace masa
"Yanzu saboda na bawa ƙanwar Mamana abu shine kake wannan faɗan? Kuma fa kilishin nan naga daga gidan mu na taho dashi, nawa ne meye laifi idan nayi kyaitar sa ga wanda naso?"
"Ni kike faɗawa haka Halima? Ni kike yiwa gori akan kilishi?" Ya faɗa yana miƙewa tsaye.
Tsayen na miƙe nima ina cewa
"Karka canza mun magana ni ba gori na maka ba kawai na tunatar da kai ne kuma ba da wata manufa nayi magana ta ba".

Ikon Allah, ƙaramar magana ta zama babba. Daga dai zancen kilishi kamar dai dama Bilal yana neman hanyar da ze tijara ni ne se gashi ya samu nan ya ringa fisaji yana rashin mutunchi da faɗar maganganu tamkar ba Bilal ɗina ba. Har yana cewa wai dama tun da muka yi aure ya lura na ke masa wani gani gani, duk abin da zan bashi se in bashi kaɗan, ko kuma idan ya ɗakko da kansa in ringa kallon sa wato taƙama ta daga gidan mu aka kawo shiyasa to daga yau baze sake cin komai daga abinda ya fito daga gidan mu ba balle na goranta masa, maganganu dai marasa daɗi marasa ma'ana ya zubar mun da fruit salad ɗin akan carpet yayi wucewar sa ɗaki yana ci gaba da tijara.

Kuka na zauna ina yi, ni banga abin laifi duk a cikin wannan abun ba, idan ma beji daɗin abin da nayi ba a zato na ai ba ta haka ya kamata ya nuna mun ba se muyi magana cikin lumana amma ya za'ayi ya fara faɗa har yana cewa baze sake cin abinda aka kawo daga gidan mu ba. Na zata daya shiga ɗakin ze fito ya lallashe ni tun da ya barni ina kuka amma har agogo ya buga ƙarfe sha biyu ina zaune ban sani ba, na share fuska ta na tashi a raina ina tuna nasihohin da Mama tayi mun akwai in da take cewa
"Karki kuskura kiyi kyauta da abun mijin ki ko da ƙwayar zarra ba tare da izinin sa ba, sata ce, har kuma be yafe miki ba Allah se ya kama ki" 'Amma kuma wannan ai ni aka bawa' na raya a zuciyata, 'ko da yake tunda an kawo gidan ina ganin ya zamu namu kenan ni dashi' wata zuciyar ta tunasar dani.

A hankali na tura ƙofar ɗakin da ya shiga, akan gado na hango shi yayi ɗai ɗai yana bacci abun sa, wani abu ya tsaya mun a rai. Wato ko a jikin sa bacci ma kwanta yana yi. Sabbin hawaye ne suka ɓalle mun, hakan nan na canza kaya na kwanta kusa dashi ina cigaba da ɗauke hawayen daya ƙi tsaya mun dan banyi zaton Bilal ze fara mun haka ba. Da asuba be tashe ni ba kamar yanda muka saba yayi ficewar sa masallaci daya dawo kuma ɗayan ɗakin ya shiga ya kwanta. Ban farka ba se kusan bakwai na safe saboda rashin kwantawa da wuri ga kuma ciwon kan da kuka da damuwar dana kwana dasu suka saka mun. Nayi mamakin ganin rana tarwai kuma babu Bilal a gefe na, haka dai na watsa ruwa nayi sallah bayan na gama addu'oi na na fita ganin baya falo se nayi tunanin to ko fita yayi?

Yan ayyukan da zanyi na fara na sake gyara falo na saka turare kafin na wuce kitchen na shiga fere doya. Har na gama haɗa abin karyawa be shigo ba, ɗaki na koma na ɗakko wayata na shiga kiran sa ga mamaki na se na jiyo ƙarar wayar daga ɗayan ɗaki na. Katsewa nayi na nufi ɗakin, na murɗa handle ɗin ƙofa naji shi a rufe da key, mamaki ya sake cika ni, a hankali na shiga ƙwanƙwasawa, nafi minti biyar a tsaye ina buga ƙofar amma ko motsi ban ji ba balle na saka ran ze buɗe mun.
[12/30/2024, 6:48 AM] Hauwa Galadima: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*PAGE 10*
Ɗaki na koma dan bazan iya karyawa ni kaɗai ba na fara sabawa tun da mukayi aure da Bilal bamu taɓa raba kwano ba, yanzu bama na jin cin abincin raina duk babu daɗi. Tun ina sauraron jin ya buɗe ƙofa ya fito har bacci ya kwashe ni a kishingiɗen da nake. Ban farka ba se da naji ana ƙwala kiran sallar azahar, nasha mamakin irin baccin da nayi. Se da sake watsa ruwa saboda jiki na da naji duk ya ɗaure sannan nayi alwala na fito ina jina fayau ciki na a rarake. Sallar na farayi sannan na gyara fuskata na saka kaya dukda yanda nake jin yunwa dan Anty Labiba ta hora ni da kasancewa tsaf tsaf ko da yaushe. Daga yanayin falon na gane ya fito yayi abinda ze yi. Dana duba kan dining kwano kaɗai na tarar an cinye doya dana soya tas ga kuma cups biyu da aka sha tea, kwashe kwanukan na farayi na kai kitchen sannan na dafa indomie naci ina mamakin me yayi zafi haka ne da Bilal yake wannan abun?

Ranar haka na wuni ni kaɗai a gida, se da yamma ne ma maƙwafta na mutum huɗu suka shigo mun, biyu gidan su ɗaya matar wa da ƙani ne Hafsa Maman Salim da Amina ita amarya ce tsiran mu sati biyu kamar yanda suka ce gidansu shine a farkon layi se Zubaida Maman Yusuf da gidan ta ke kallon nawa da kuma Bintu ita ce muke katanga ɗaya. Har gab da kiran magriba muna ta hira kafin suka yi mun sallama suka tafi na rakasu na dawo na gyara gurin da muka ɓata. Zuwan su ya rage mun kewa ya kuma ɗauke mun hakankali daga damuwar in da Bilal ya tafi yini guda na kuma kira wayar sa sedai tayi ta ƙara baze amsa ba daga ƙarshe ma ya kashe ta gaba ɗaya.

Har nayi sallar isha'i babu shi babu dalilin sa, zuwa sannan hankali na ya tashi na fara tunanin ba lafiya ba. Ƙarfe tara na kira Mama ina kuka na gaya mata tun safe Bilal ya fita ina ta kiran sa kuma baya amsawa daga ƙarshe ma wayar a kashe take.
Chapter 22 · 0% Book details