← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 14 OF 158

Sashe 14

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A banza zaki kashe kanki Halima mu zaki yiwa asara tun da dai gashi ƙiri ƙiri ya nuna miki baya yi idan kina da hankali ya kamata ki cire shi daga ranki. Dama yau nake niyyar in tambaye ki in gayawa Mama yanda akayi saboda kar su cigaba da shirin biki a banza ko kuwa dai in kama kaina kar in shiga abin da babu ruwana?"

Se na kalleta a birkice nace
"Me zaki gaya mata kuma Anty?"
"In gaya mata na tambaye shi zancen gida tun da ya tafi be sake dawowa ba mana ita ai me hankali ce idan taji haka zata fahimci in da zancen ya dosa, dama dai na gaya mata ta dakata da duk wani shiri dangin Abbanki ne dai suke ta shirin su dan ma dai dama bikin ba na ki ke kaɗai bace abin haushin baze musu yawa ba" ta bani amsa. Se kawai na fashe da kuka, ta saki baki tana kallona can tace

"Dukan ki nayi ko zagin ki Halima da zaki saka mun kuka?"

"Ya yake so nayi Anty? Me zanyi Bilal ya gane irin son da nake masa?" Na faɗa cikin matsanan cin kukan dake fitowa tun daga ƙasan raina. Na yarda son Bilal jarabawa tace babu kuma wanda ze fahimci yanda nake ji har shi kansa kuwa. Kamar zata share ni ta wuce se kuma ta zagayo ya zauna gefe na tare da jana jikin ta nan kuwa na sake samun sararin yin kuka yanda nake so. Cikin tausasawa ta shiga yi mun magana tana cewa

"Halima har se ya buɗe baki yace baze aure ki ba kafin ki fahimci kurman baƙin da yake miki? Halima ko a littafin hausa kin taɓa jin labarin neman aure irin naki? Aure fa za a yi na yar mutum ba wai yar tsana ba amma ace ƙasa da wata ɗaya ba ango ba dangin sa ba babu wani ɓangare da suka nuna murna ko zumuɗin su akan abin da ze faru a ina kika taɓa ganin an yi haka?
Ki ture duk wasu al'adu ace ba dole bane basu yi ba amma Halima muhalli yana cikin sharuɗan da se sun samu kafin aure ya ƙullu, a ina ze ajiye ki? Ko kuwa dama lasisi yake nema a gidan ku zaki ci gaba da zama bayan an ɗaura muku auren ko yaya? Yau idan haya ze kama biki ƙasa da sati uku yaci ace ya samu har ya nuna guri an san me za a saka miki. Kwana nawa ina miki magana akan ki tuntuɓe shi? Yanzu da na masa magana da kaina gashi ya nuna miki zahirin da kika kasa ganewa ko kuma da be fito miki a mutum ba ba auren ki yaron nan ze yi ba ki godewa Allah da be samu galabar lalata miki rayuwa ba ki haƙura ki barwa Allah zaɓi Halima".

"Bilal yana so na kuma aure na zeyi Anty. Ta yaya za ayi ya turo iyayen sa a saka mana rana har idan ba aure zeyi ba? Kuma zancen gida na gaya miki gini yake be ƙarasa ba ni muna magana ya kuma tabbatar mun kafin ranar biki ze gama komai gajen haƙuri kawai kika yi kika masa magana gashi yanzu kin saka ransa ya ɓaci, yaƙi ya zo a waya ma sau ɗaya yake kira na kuma bata ko bari muyi doguwar magana ze kashe idan ma har ya ce ya fasa ɗin ai ke ce kika jawo ba wai a karan kansa yayi ra'ayi ba" na faɗa cikin kuka. Yanda tayi shiru tana kallo na ta tabbatar neman hanya mafi sauƙi da zata huce takaici ma takeyi ta rasa, se na miƙe ina cewa
"Ni gidan mu kawai zan tafi, dama ai so kike yi ya fasa aure na shiyasa idan ba haka ba ai ina ji har Mama se da tace ki rabu damu ai ni ce zan aure shi tun da naji na gani kowa nasa ido ne" na wuce ɗakin da nake ina ci gaba da kuka haɗi da zazzaga mata rashin kunya. Kaya na na shiga haɗa wa a akwati waya ta dake jikin caji tayi ƙara jin ringing ɗin Bilal yasa na saki kayan hannu na na wuce gurin wayar da sauri na ɗaga.

Kamar ko da yaushe a kwanakin nan muryarsa cikin sanyi ya amsa gaisuwar da nayi masa kafin yace
"Amm kina wani abu ne Halima?"
"Ba abinda nake yi, wani abu kake buƙata nayi maka? Ko abinci kake so?" Na faɗa cikin zaƙuwa. Ina jin sa ya sauke ajiyar zuciya kafin yace
"Ina so na ganki ne, akwai maganar da nake so mu tattauna me muhimmanci idan babu damuwa"
"Wace irin damuwa kuma? Yanzu zaka zo ko se da daddare?" Na amsa shi, se yayi ɗan jimm kafin yace
"Ke zaki zo ki same ni idan zaki iya amma". Shiru nayi na kusan minti ɗaya ina juya maganar a raina, abin da Anty Labiba ta faɗa mun yanzu akan na godewa Allah da be lalata mun rayuwa ba ya faɗo mun a rai se nayi saurin korar maganar daga raina ina bawa kaina tabbacin Bilal ba ze taɓa yaudara ta ba ba kuma wannan niyyar ta kawo shi guri na ba.

"Karki takura kanki idan ba zaki iya ba babu damuwa dama magana ce akan abinda ya shafe mu mu biyu da nake ganin ya kamata mu tattauna amma zamu iya barin ta kawai idan baki da lokaci" ya katse mun shirun da nayi. Ban san sanda harshe na ya furta
"A ina zan zo na same ka toh?"
"Ina shagon Sani" ya bani amsa. Se na sauke ajiyar zuciya jin ba wani guri daban ya ce na same shi ba har na tsinewa shaiɗan ɗin daya fara kawo mun wasi wasi akan Bilal ɗin. Aje wayar nayi na shiga toilet da sauri na canza pad ɗin jiki na tare da wanke fuskata na fito na canza kaya. Dogon Hijab na saka da niƙab saboda munafukan unguwan mu. Dana fito ban tarar da Anty Labiba a falo ba se Amir ne ya tare ni yana tambayata me ya samu Momy ya shiga ɗakin ta ya tarar da ita tana kuka nace masa ban sani ba sauri nakeyi kuma ana jira na ne yaje ya bata haƙuri.

A bayan gidan mu Chemist ɗin Abokin sa Sani yake, haka na ringa gyara niƙab ɗin fuskata harda canza tafiya dan kar a gane ni ce, na tarar da shi da Bilal zaune suna hira. Kallo ɗaya na masa na hango ramar da yayi idanunsa sun sake fitowa haka dogon hancin sa ya ƙara tsayi hatta da lips ɗin sa se naga sun bushe sun ƙara jaa alamar yana cikin damuwa ko bashi da lafiya. A taƙaice muka gaisa da Sani kafin ya fita ya bamu guri. Na sauke kaina ƙasa saboda yanda Bilal ya kafe ni da nasa idon da nake jin sun ƙara kaifi yau, sama da minti biyar muna zaune kafin a hankali ya fara magana yace

"Kiyi haƙuri Halims be kamata ace na ɗauki fushi akan abin da ya faru ba. Bayan na dawo gida na nutsu na gane kun fini gaskiya se dai ina cikin wani yanayi da ni kaɗai na san wane hali nake ciki duk kuma wanda zan yiwa bayani be zama lallai ya fuskan ce ni ba". Kallon sa nayi jin yayi shiru se yayi murmushi ya ci gaba da cewa
"Tun farko shiyasa ban so aka saka bikin nan wata shida ba kuma kema na gaya miki, dalilin da ya saka bana ɓoye miki komai da nake ciki kenan Halims saboya tunani na duk abin da ya taso za kiyi mun uzuri" se na ɗaga kai na kalle shi yayi saurin cewa
"Ban ce baki mun ba, wlh na sani kin yi ƙoƙari. Kin mun abin da ba kowacce mace ba kuma na yaba and i will for ever be grateful for that Halima. Ke ɗin kin nunawa duniya true love still exist, se dai har yanzu ban kai ba Halima. Nayi tunanin a wata shidan nan zan iya yin ƙoƙarin ganin ban baki kunya ba amma se yanzu na fahimci wautar da nayi gashi kuma lokaci ya ƙure mun balle na juya da baya".

Gaba na ya yanke ya faɗi baki ja har yana rawa na kalle shi nace
"Ban gane ba, what are you trying to tell me Bilal what do you mean by lokaci ya ƙure balle ka juya baya?"

"Relax Halima ba wani abu nake nufi ba" ya faɗa yana kama hannu na, se na fizge ina kallon sa se dai na kasa ci gaba da magana saboda yanda zuciya ta take wani irin bugu kamar zata huda ƙirjina ta fito. Wayar sa ya ciro daga aljihun sa yayi danne danne kafin ya miƙa mun, hannuna na rawa na karɓa na kalli screen ɗin. Video gidan daya kai ni a matsayin nasa wanda zamu zauna a ciki ne yake playing, seda na kalla daga farko har ƙarshe kafin na kalle shi muka haɗa ido dan shima ni yake kallo se ya karɓi wayar ya mayar da ita aljihunsa kafin ya haɗe hannu biyu ya dafe haɓarsa ya furzar da iska daga bakin sa kafin yace

"Bayan da aka saka ranar auren mu munyi magana da Baba Liman ya kuma kira gidan su yaron da ze auri Fadila akan suyi haƙuri a ƙara ranar auren su zuwa wata goma amma suka ƙi yarda akan in dai ba wata shidan da suka yanke ba se dai a mayar musu da kuɗin su kawai ya haƙura ya fasa auren ta. Na gaya miki Halima ni zan yi mata komai na aure, babu abin da baki sani ba a kaina tun da mahaifin mu ya rasu duk wata ragama ta yan ɗakin mu ta dawo kaina. Yayyenmu tun da muka samu saɓani dasu lokacin rabon gado shike nan suka zare hannun su daga komai daya shafe mu ko sanda nace babu damuwa a bar zancen auren mu a wata shidan na ɗauka su Yaya Alhaji ze yiwa Fadila kayan ɗaki ne se da kuma biki ya taho da Hajja tayi musu magana suka ce ai an raba gado an bawa kowa nasa dan haka ba abin da zasu mana.."
Chapter 14 · 0% Book details