← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 158

Sashe 19

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kafin tayi magana nayi saurin kama hannun ta ina kuka nace
"Dama na san saboda ni ne, dan Allah Mama kiyi haƙuri, ki yi mun addu'a ki kuma sakawa al'amari na da Bilal albarka nasan ubangiji baze kunyata ku ba. Addu'ar ku zata kasance hasken da ze kore mana kowanne duhu. Kuma ki dena damuwa Mama yanzun nan Bilal ya kira ni ya gaya mun wani abokin Baban sa ya bashi kuɗi yace ya ƙarasa gini, babu abin da ba ze yi ba da yardar Allah Mama ki kwantar da hankalin ki babu wanda zeyi mana dariya kamar yanda suke sauraro".

Hannu biyu Mama ta ɗaga tace
"Allah na bar amanar Halima a hannun ka. Kada ka bari wauta da makauniyar soyayya su jagoranci al'amuran ta a gidan auren ta"
"Amin, yanzu ki kayi magana Amina. In sha Allahu se mun ce gara da aka yi" Abba ya sake faɗa.
A sanyaye na tura shayin dana haɗo zuciya ta duk babu daɗi. Ban zaci rashin son da Mama take yi wa aure na da Bilal ze saka har ta zubda hawaye ba. Se na ringa jin kamar banyi daidai ba da tun farko naƙi bin ta tata amma kuma ban hango laifi na akan bin son raina da nayi ba. A cikin labarin ta na samu tawa ƙarfin guiwar. A kullum ta kan karanta mana irin rayuwar da sukayi da Abba, wuyar da suka ci tare har zuwa yanzu da daɗi yazo shima suke shan sa tare.
Tun ina ƙarama na tashi da sha'awar irin rayuwar da iyaye na suke gudanar wa ta tsantsar soyayya da tattalin juna har zuwa kanmu yaran da suka haifa.

Mahaifiya ta Amina Sa'id haifaffiyar unguwar Yakasai ce yayin da Abba yake haifaffen Galadanci. Tamkar banbancin dare da rana haka suka sha banban gurin asali, Mahaifin Mama attajiri ne kuma basarake wanda a zamanin sa sunansa yayi amsa kuwwa a ƙwaryar birnin kano da kewaye. Allah ya bashi tarin dukiya wadda ya ƙare rayuwar sa yana hidimtawa iyalansa da al'ummar dake zagaye dashi. Mamana ita ce ya ta huɗu cikin jerin yaran sa bakwai daya haifa da matar sa ta aure guda ɗaya Hajiya Saude. Namiji ne babban su Alhaji Lawan se me bi masa Hajiya Rumana sannan Mama Fauziyya se Amina mamana kenan, Baba Faisal ya rasu shekaru biyar baya, Baba Mudassir se Anty Labiba data kasance autar su.

Abbana ya fito daga babban gida me yawan ahali domin matan mahaifin su huɗu, a jerin yaya shine na goma sha uku a gidan gaba ɗaya a ɗakinsu kuma shine na huɗu kuma namiji tilo. Gidan su gida ne irin na bani babu, Mahaifin su Malam Ibrahim talaka ne domin har ya mutu be bar musu komai ba ban da gidan gandu. Duk da bashi dashi kuɗi amma yayi ƙoƙari sosai akan tarbiyyar yaransa. Ya saka su makarantar addini duk kuma wanda kaga yayi karatun boko a gidan to shi ya saka kansa ba Malam Ibrahim ba. Abbana shine namiji na farko daya fara karatun boko a gidan domin sauran da sun tasa sukayi sauka a makaranta shikenan se su shiga kasuwa, da dama ta fara zuwa se aure su fara tara Iyali wannan yasa jikokin gidan muke da bala'in yawa wasu idan ka kalli shekarun su dana iyayen su se kaga kamar basu suka haife su ire ire na mun shiga layin sa'annin yayan jikoki ne saboda iyayen mu da basu yi aure da wuri ba.

A BUK Abba ya haɗu da Mama, lokacin yana level 2 Business administration ita kuma tana level 1. Daga mutunchi kasancewar sa me ƙoƙarin gaske ya kan koya musu karatukan da suka shige musu duhu a hankali mutunchin nasu ya rikiɗe zuwa soyayya wanda ita Maman ce ta fara nuna sha'awar hakan. Daƙyar Abba ya amince, badan ba tayi masa ba ko kuma baya son ta se dan ganin tazarar dake tsakanin sa da ita. Ya kan ce mata
"Akwai banbanci me girma tsakani na dake Amina. Ni ba sa'an auren ki bane, ƙima ta bata kai ta ko da direban da yake kawo ki makaranta ba ki rufa mun asiri ki barni na kammala karatuna lafiya domin shine madogara ta idan wani abu ya faru na rasa wannan damar ban san ina zan kama ba". Bata sare ba taci gaba da bibiyar sa da kuma ubangiji ya ƙadarta akwai rabon aure a tsakanin su se gashi sun yi har an haife mu a kullum bakin Abba baya gajiyawa da nanata halin karamcin da ahalin Mama suka gwada masa.

"Sun ƙauna ce ni a sanda bani da komai, sun aminta dani suka bani guda daga mafi soyuwar ahalin su idan har ban saka musu ta hanyar faranta ran Amina har bakin raina ba da wanne ido zan tsaya gaban Allah na maida amar da mahaifin ta ya bani?" Abin da yake yawan faɗa kenan. Mama ta manta asalinta da rayuwar jin daɗin da ta taso a ciki ta rungumu mijin ta da sabuwar rayuwar da ta zaɓawa kanta. Sun kwana basu ci ba, wata rana su ci sau ɗaya ko sau biyu an tashe su daga gidajen haya ba adadi amma duk ta jure bata sare ba haka nan dai dai da rana ɗaya bata taɓa tilasta masa karɓan tayin taimakon da yan uwanta suke masa ba kamar yanda yace mata zai nemi halal ya ciyar da ita alfarma ɗaya kawai yake nema a gare ta shine karta raina yana ji jikin sa wata rana ze mayar da ita inuwar data saba da ita gashi kuwa Allah ya amsa bayan wani lokaci.

A sanda Mama take da ciki na Anty Labiba ta dawo gidan mu da zama, tun tana zuwa ta kama mata ayyuka ta tafi har ya zama ta dawo gidan gaba ɗaya bayan an haife ni saboda yanda take so na. Da ita aka sha gwagwarmaya ba kuma ta bar gidan mu har se da lokacin auren ta yayi shi yasa Abba ya kan ce Labiba ce babbar yar sa ba ni ba domin tun tana da shekaru goma a duniya take hannun sa har ya aurar da ita itama kuma kallon uba take masa b wai mijin yayarta ba.

Na gyara kwanciya ta ina sake nutsawa cikin tunanin dana tafi, irin wannan rayuwar nake so na gina, mu sha wahala tare da miji na ta yanda a duk sanda Allah yayi mana arziƙi baze manta halacci na ba. Ban yarda da irin auren da mutanen yanzu suke rububin yi ba na ready made, baki san yanda namiji yasha wahalar sa ya tara abinda yake dashi ba kin ganshi a me wadata kin aura daga ƙarshe ya ringa goranta miki cewa arziƙin sa kika hanga idan kuma me mata ne nan ma se ya fifita matar sa da suka sha wahala tare har a ringa kiran ki da yar tayin cin arziƙi shine abin da ban yarda dashi ba. Matar da aka sha wahala da ita tafi mutunchi tafi ƙima a gurin miki har ma da duk waɗanda suke zagaye dashi, haka ko da ya auro wata daga baya itan ce dai zata zama a sama haka nan yayanta se sun banbanta da wanda uwarsu ta zo rana tsaka.
A mahangar Haliman Bilal ba cewa ta ba.

Daga yana yin da naga gidan mu washe gari na gamsu dagaske an fara shirin biki. Masu aikin kayan zaƙi na gara ne suka fara baje kolin su haka nan yan uwa da ƙawayen Mama sun fara zuwa suna tsara yanda biki ze kasance hatta Goggo Habi da taga babu sarki se Allah ta saki musamman da aka aiko da yamma cewa ranar asabar da zata kama saura sati ɗaya ɗaurin aure za'a kawo lefe na wannan ya wanke mata zuciya tun da dama tace abin da idan ta tuna yake baƙanta mata rai yanda za'a ɗauki santaleliyar budurwa kamata a bayar sadaka ashe da iskanci ne yasa yaƙi yin abin da ya kamata yanzu da yaga ana nema a ƙwace masa goruba daga hannu ai ya motsa a tunanin ta kamar yanda Abba ya gaya mata sun kira waliyyan sa ne sun ce musu sun fasa shine suka bayar da haƙuri akan wani al'amari ne ya janye shirun da sukayi amma yanzu komai ya yaye.

A cikin sati ɗaya aka gama aikin gidan Bilal, gida ya fito yayi kyau masha Allah tamkar na wani hamshaƙin me kuɗi. Ranar alhamis su Anty Labiba suka je suka ga gidan a lokacin ana fenti kowa ya dawo yana santin gida amma saboda rashin tsoron Allah irin nata da dai ba zata taɓa son Bilal ba se cewa tayi ita bata yarda gidan sa bane, idan kuma har yana da halin yin gini irin wannan to kuwa ba ƙaramin rainawa Halima hankali yayi ba. Ni kaina da naga video gidan se da nayi mamakin yanda finishing ya sake fito da ainihin kyau da tsarin gurin, har ƙofofi naga an canza a sanda muka je na ƙarfe ne har so nayi na masa magana akan me ze haka a saka dai na zamani amma na kasa ze gashi an canza saman ma da da yace ceiling ze yi bashi da sararin yin pop yanzu se gashi anyi ga tiles me kama da marbles an malale ko ina haka kitchen yasha cabinet irin yanda nake mafarki.
Chapter 19 · 0% Book details