← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 158

Sashe 49

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Me yasa Mama?"
"Saboda haka yaga dama". Ta bani amsa, take hawaye ya ɓalle mun dan dama ba nisa sukayi ba, na karanci akwai tausayi na akan fusakar ta amma ta dake tace
"Tun farko abinda na gudar miki kenan Halima amma kika kasa ganewa. Se kije kiyi ta haƙuri, ita dama rayuwa haka take kowa da kalar nasa ƙalubalen" daga haka ta fita ta barni na haɗa kai da guiwa na shiga kuka kamar wadda aka doka. Tuntuni dama dashi da iyayen sa kullum cikin yi mun shaguɓen na tafi gida na haihu sukeyi yanzu kuma se ace na koma bayan ko da na haihun ma basu zo ba alamar basu damu da ƙaruwar da muka samu ba kenan.

Kukan dana ringayi be hana Mama Fauziyya da Anty Labiba mayar dani gidan Bilal ba. A hanya suna ta hira abun su ni ko na haɗa kai da window ina share hawaye. Gaskiya ba'a kyauta mun ba, an ma nuna neman kai kawai akeyi dani shi yasa za'a tattarani kwana biyu da haihuwa ace za'a mayar dani gidan miji. Da muƙulli na sukayi amfani suka buɗe gidan. Compound ɗin kamar ya shekara babu mutum a ciki ƙura da ganyayyekin bishiya kasancewar sanyi ya fara kankama. Yanayin dana ga gidan yasa na fara shakkar anya kuwa Bilal na gari? Domin Bilal ɗin dana sani in dai ba sharafa yakeyi ba babu yanda za'a yi ya bar muhallin da yake zaune ciki a haka.

Yanayin falon ya tabbatar mun da zargina na Bilal baya nan, hatta da fasassun tangaran da taliyar daya zubar tun shekaran jiyan suna nan ba'a kwashe ba. Ɗaki Mu'azzam ya shigar mana da kayayyakin baby wanda duk a gidan mu aka siya tunda ko abun susar kunne banje dashi ba. Anty Labiba da Mama Fauziyya suka gyara gidan tas, kafin a kira Magriba har tsakar gidan an nemo almajirai sun share sun wanke. Har bayan sallar isha'i kafin sukayi mun sallama zasu tafi, na fashe da kuka ina cewa

"Yanzu tafiya zakuyi ku barni ni kaɗai?"
"To zama kike so muyi Halima? Da can dawa kike zaune ba ke da mijinki bane?" Mama Fauziyya ta faɗa. Na girgiza kai ina cigaba da kukan nace
"To ai yanzu baya nan Mama, kuma ko yana nan da da yanzu ai ba ɗaya ba ni ban ma san yanda zan kula da yaron nan ba kuka yakeyi cikin dare Anty Labiba ce take goya shi kuma idan safiya tayi ya zan masa wanka nima ya zanyi?" Na ƙarasa cikin kuka me tafe da shassheƙa. Shiru suka yi da alamu kukan nawa ya taɓa su. Mama Fauziyya ta zauna kusa dani ta jani jikin ta cikin rarrashi tace

"Mijinki bashi da kirki Halima. Ta yaya za'ayi ace ki haihu har kwana biyu amma be zo ba wani nasa be zo ba a gari ɗaya ba wai can nisan duniya ba? Kin fi kowa sanin sauƙin kai irin na mahaifin ki amma tunda har yayi fushin da yace ki dawo gidan ki tabbatas abun ya ɓata masa rai. Da kansa ya kira Bilal ba wai wani ya saka ya kira shi ba amma be amsa wayar sa ba har yanzun nan kuma be biyo sahun kiran ba, dama ai ga akan yanda kuka rabu har kika tafi gida ko? Kiyi haƙuri ki jira shi ya dawo duk yanda kuka yi ki kira waya domin mahaifin ki yace ba zaki koma ki zauna masa a gida ba har se da dalili, wato idan sakin ki yayi".

Da sauri na kalle ta jin abunda ta faɗa daga ƙarshe, wai Bilal ya sake ni. Baki na har rawa yakeyi nace
"Mama y sake ni kuma?"
"Yanzu bayan wannan kora da halin daya miki har kina tunanin cigaba da zama dashi ne Halima?" Mama Fauziyya ta faɗa kusan da mamaki, se na shiga girgiza mata kai nace
"Bafa faɗa mukayi ba Mama, kuma ni jiki na ma yana bani ba lafiya Bilal yake ba ai dai kunga gidan nan beyi kama da wanda mutum yake zaune a cikin sa ba tun da har can ɗakin sa kun duba duk babu alamar yana kwana a gidan nan. Ni tsoro nakeyi koma wani mugun abu ne ya same shi" na ƙarashe cikin sabon kuka.

Yanda Mama Fauziyya ta buɗe baki ze baka tabbacin ta rasa abin faɗa ne, a fusace Anty Labiba tace
"Dan ubanki ai se ki bazama ki binciko in da ya shiga. Ki tashi mu tafi idan kuma baki gaji da kwasar takaicin bane se ki zauna ki taya ta kwana ni dai nayi nan" daga haka ta nufi ƙofa itama Mama Fauziyyar ta miƙe ta bita ganin haka yasa na rufa musu baya ina fashewa da sabon kuka nace
"Ni wlh bazan iya zama ni kaɗai ba gida zan tafi"
"Ai kin san hanta maza tafi amma karki kuskura naga ƙafar ki kusa da motar mu ki jira idan muka tafi se ki biyo bayan mu" cewar Mama Fauziyya. A bakin ƙofa na durƙusa bayan fitar su na ringa rusa kuka baji ba gani, se da baby na ya fara kuka kafin na tashi daga gurin na ɗauke shi daga kan kujerar da yake kwance na zura masa ido ina kallon sa hawayen dake saukar mun suna ɗisa akan fuskar sa. Rungume shi nayi ina cigaba da kukan. Ban ma san me ya kamata nayi ba, an shiga an fita tsakanina da Abba na kawai dan ba abinda za'a gaya mun na yarda wai shi yace a dawo dani gidan nan.

Jin yaƙi yin shiru yasa na miƙe na shiga ƙoƙarin goya shi, motsi naji kamar ana murzawa ƙofa muƙulli kafin kuma aka shiga bugawa, sakko da yaron nayi da sauri na ƙanƙame shi kamar wadda aka zo ƙwace shi, a hankali na nufi ƙofar, ta jikin yar ɓular leƙe na hangi waɗanda ke tsaye, Abubakar ne da Nasir sun ruƙo wani da banga fuskar sa sosai ba saboda kansa yana jingine ne jikin kafaɗar Abubakar ɗin. Ganin waɗanda na sani ne yasa naji hankali na ya kwanta dan haka na buɗe musu ƙofar. Gabana ya yanke ya faɗi ganin wanda suka ruƙo ɗin, Bilal ne. A yanayin da yake yafi kama da wanda yasha daƙyar a hannun yan fashi ko ɓarayin daji. Da sauri na matsa na basu guri suka shigo se lokacin na lura ashe har da Hajja da Anty Amina Yayar sa.

Jikina har rawa yake ina kallon su, Hajja ta fashe da kuka tana cewa
"Wannan masifa da bala'i har ina?"
"Dan Allah Hajja kiyi shiru, kin dai ji abinda likita yace yana buƙatar hutu sosai kar a dame shi da hayaniya ko wasu tambayoyi shiyasa ma nace ku wuce gida kawai amma kuka biyo mu kin zo kuma zaki cika masa kunne da hayaniya" Abubakar da suka kwantar da Bilal ɗin akan kujera ya faɗa, se kuma ya kalli in da nake tsaye kamar me jiran a bani umarni na fice a guje yace
"Anty Halima ƙaraso mana".

"Halima? Au dama tana gidan nan?" Hajja ta faɗa tana waige na. Kamar mara laka na matsa cikin falon, Hajja ta sake fashewa da kuka tace
"Ba shakka, yanzu kina gidan nan kwana har biyu sama ko ƙasa ba'a san inda mijinki yake ba amma baki biyo kadi ba Halima? Ko da yake baki da asara idan ma mutuwa yayi hankalin ki kwance tunda kin aje iri se dai kiyi jiran lissafi kawai"

"Wai dan Allah wane irin abu kikeyi haka Hajja?" Anty Amina ta sake katseta cikin fushi, se ta miƙe ta isko ni tare da karɓan yaron hannuna tana cewa
"Zauna Halima, sannu kinji".
Zaman nayi ina zare ido dan gaba ɗaya kaina ya kulle da abinda yake faruwa. Daga kwancen da Bilal yake ya miƙo mun hannu, na kalli fuskar sa da tayi luhu luhu kusan kamannin sa ma sun canza ban san sanda na isa kusa dashi ba na durƙusa lokaci ɗaya na fashe da kuka.

Sha biyu ta gota sanda Hajja na Nasir suka bar gidan Abubakar da Anty Amina suka zauna zasu kwana tare damu. Abubakar ɗin ne ya taimakawa Bilal yayi wanka bayan ya ɗan warware daga magagin da yake tayi kamar wanda baya cikin hayyacin sa. Shayi kaɗai ya iya sha, a nan falo suka kwana ni kuma muka kwanta a ɗaki da Anty Amina. Kwata kwata na gagara runtsawa, ga tunanin abinda ya samu Bilal dan har sannan babu wanda yace mun komai ga babyn dake ta tsula kuka har ya zarce na kwanaki biyun da mukayi a asibiti, haka muka kwana Anty Amina na jele dashi tsakanin ɗaki da falo idan ta gaji Abubakar ya karɓa Bilal dai yasha bacci saboda magungunan daya sha dan se guraren takwas na safe ma kafin ya farka yayi sallah.

**********
A hanyar komawa Mama Fauziyya take cewa Anty Labiba
"Halima ta bani tausayi Labiba, be kamata ace a yanzu ne Yaya Aminu ze nuna fushin sa ba. A gani na da haƙuri yayi a zauna a gida ko sati biyu ne tayi, idan har aka ja wannan lokacin be zo ba ina ganin komawar ma bata da amfani kawai a kira shi ya bata takardar ta shikenan dama ƙila rabon wannan ɗan ne kuma gashi an haifa".

"Anty Fauziyyah kenan, ni dai bazan tofa komai akan sabgar Halima ba amma lokaci ze yi alƙalanci" Anty Labiba ta bata amsa. Da suka isa gidan ma seda Mama Fauziyyar ta sake yiwa Mama magana akan ta taushi Abba Halima ta dawo gida.
"Duk ma wanda za'a tura ta zauna da ita ba kamar tana nan gabanki ba. Sanda ya kamata ku nuna mata kuskurenta bakuyi ba ba se yanzu da hakan ze iya cutar da ita ko ya cutar da abinda ta haifa ba. Kuskure ai an rigada anyi shi tun farko da aka biyewa son zuciya aka yi auren haƙuri kawai zakuyi ku tayata karɓar ƙaddarar ta" cewar Mama Fauziyyar.
Chapter 49 · 0% Book details