← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 158

Sashe 41

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

[1/25, 11:31 AM] Hauwa Galadima: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*

*Page 17*
Be ko saurari tayin abincin da na masa ba ya fice daga gidan bayan yayi wanka yana sake jaddada mun Fadila ta bar gidan kafin ya dawo, bayan fitar sa na shiga gyara falon da tayi mun kaca kaca da shi dan tun shigowar Bilal ɗin ta koma ɗaki na in da na sauketa. Na tabbatar taji banbamin da yakeyi tun da ba a hankali yayi maganar da ze fita ba, na ɗauka daya fitan zata tuntuɓe ni da zancen amma shiru se ma dawowa falo da tayi zata sake tarwatsa gurin na dakatar da ita ta hanyar ce mata ba nisa yayi ba yanzu ze dawo. Ina kallon ta ta harare ni harda murguɗa baki ta koma ɗaki.

Ranar raba dare mukayi muna tashin hankali da Bilal tunda ya dawo gurin goma ya tarar Fadila bata tafi ba ya tasa mun masifa tun ina bashi haƙuri da nuna masa rashin dacewar abinda yake son nayi har na kai bango nace ba zan kore ta ba ai ƙanwar sa ce kuma gidan sa ne idan da gaske baya buƙatar zamanta ya kore ta da kansa mana shikenan fa ina wuta ya sakani a ciki ya ringa zazzaga da tijara se naga ashe abinda ya mun akan kifi ma somin taɓi ne. Dana gaji na kwanta na juya masa baya se dai na kasa bacci ga ɗan Fadila da kamar ma sa gayya yake ta canyara uban kuka duk suka haɗu suka cazamun ƙwaƙwalwa.

Daƙyar na iya farkawa nayi sallah bayan dana samu bacci ya ɗauke ni, sosai kaina yake mun ciwo ga zuciya ta da babu daɗi. Ina idar da sallah na sake komawa na kwanta ban farka ba se ƙarfe tara harda wani abu. Se da nayi wanka sannan na fita daga ɗaki, Fadila na harɗe akan kujera da remote tana canza tasha, yanda ta kalle ni se ka ɗauka kishiyar ta ce ta fito ta wani basar ta maida kai abinda takeyi nima kallo ɗayan na mata na maida hankali na kan falon dake nan kamar yayi sati bega gyara ba ga kwanukan abincin a ajiye har sun bushe alamar ba amfanin safiyar nan bane harda cup dana hango sauran shayi a ciki.

Ji nayi zuciyata ta sake harzuƙa, ni ya kamata nayi jidali an kawo mun baƙuwa ba tare da an sanar da ni ba kuma tazo tana nema ta mayar mun da gida wani dandalin yan datti ga wani sabon raini da ban santa da shi ba tana nema ta fara gwada mun. Kitchen na wuce ba tare da na ce mata kanzil ba, ko me tayi tunani kuma se ji nayi tace
"Ina kwana Anty, se yanzu kika tashi kenan?"
Da lafiya na amsa mata na shige kitchen, nan ɗin ma kaca kaca komai yana zaune da ƙafarsa. Se da na gyara gurin tas kafin na buɗe fridge in fito da abincin da Bilal yaƙi ci se in ɗumama mu haɗa da baƙin shayi tunda banga alamar ya siyo abin karyawa ba, banga abincin ba se lokacin nayi realizing ai nama wanke kwanon cikin kayan dattin dana tarar a kitchen ɗin. Tunanin wanda yaci na tafiyi, nasan ba Bilal bane zuciyata ta raya mun Fadila ce.

Ina tsaka da jimamin irin wannan abu ta shigo kitchen ɗin tana haɗa fuska kamar zatayi kuka tace
"Kun san da masu jego a gidan saboda Allah se ku kwanta kuyi ta bacci? Ni wlh yunwa nakeji har jiri nake gani asan yanda za'ayi dani".

Ba yabo ba fallasa nace mata
"Wace abinci kuma kike nema bayan wanda kika ci?" Yanda tayi da ido kamae irin na mata ƙage se kuma ta watsa ido tace
"Wai abincin cikin fridge? Yunwa ce ta hanani bacci tun dare naci wannan na duba ma naga ko da dankali ko doya in soya mana naga babu se wani sauran bread na samu akan dining na haɗa shayi nasha amma ji nakeyi ma kamar ƙara mun yunwar akayi". Tunda ta fara magana nake kallon ta har ta kai aya, mamakin ƙarfin halinta nayi. Ɗan bread ɗin da take cewa fa kaɗan ne babu a guda in da dani da Bilal muka ci har saura se yayi mana shine take cewa wai beje mata ko ina ba.

Rufe fridge ɗin nayi ba tare da nave mata komai ba na wuce store, banda shinkafa da ƙwarorin taliya da macaroni babu abin da yayi saura a ciki, taliyar na ɗauka na haɗa da papper mix guda ɗaya daya mun saura na dafa mana mukaci ina jinta a wasance tana cewa wai na bata abinci babu kifi babu nama nayi kamar ban ji ba dan raina a ɓace yake bana so kuma na furta wani abu da daga baya ze zama abin magana tunda naga su basa raina abin laifi. Bata tayani da ko cangwal ba na aikin gida se hayaniyarta data ɗan ta data cika mun kunne. Ina gamawa na koma ɗaki na kulle ƙofa ta na bari akan tunda akwai sauran taliyar taci da rana.

Tunda na kwanta bacci ya kwashe ni ban tashi farkawa ba se ƙarfe uku harda mintoci na rana. Sallah na farayi kafin na leƙa naga halin da Fadila suke ciki, falon babu kowa se pillows dake hargitse kamar anyi wasan dambe. Ɗaki na leƙa nan ma bata nan babyn ta ma baya nan balle nayi zaton ko banɗaki ta shiga. Tunani na shigayi ina ta tafi? In da akwatin ta ke ajiye na duba nan ma babu hakan ya tabbatar mun da fitar taje ta dawo tayi ba ƙila gida ta koma amma me yasa zata tafi bata gaya mun ba?

Ji nayi hankali na ya tashi, kar dai Bilal ya dawo ya kore ta, amma kuma da ya dawo gidan dole ze tayar dani ko da yake tunda ba abin ƙwarai zeyi ba be zama lallai ya tashe ni ɗin ba tunda yasan zan hana.
Duk se naji babu daɗi, layin ta na shiga kira wayar tayi ta ringing ba'a amsa ba dana sake kira kuma se na jita a kashe. Har na mayar da akalar kiran kaj Bilal se kuma na katse na bari idan ya dawo zanji dalilin da yasa be haƙura ba ya koreta. Haka na ƙarasa wunin rai babu daɗi, biyar da rabi ya dawo sallama ma ciki yayi be amsa sannu da zuwan da nake masa ba ya wuce ɗaki abin sa se na tashi na bishi. Ganin ya shiga wanka se na koma na haɗa masa abinci, shinkafa da wake da mai da yaji dan bani da ko ƙwayar attaruhu balle nayi miya ko jallof nasan kuma yanda yake fushin nan ba siyowa zeyi ba. Har ya zauna na manta ban aje masa ruwa ba na koma na ɗakko da sauran zoɓo roba ɗaya daya rage Fadila bata shanye ba.

Yana ci ina satar kallon sa yanda kasan me cin guba, na tabba harda yunwa tasa shi ci ba tare da yayi ƙorafi ba. Se da ya kammala ya dawo cikin falon kafin na matsa kusa dashi ina cewa
"Kuma ɗazu daka dawo se baka tashe ni ba"
Kallon rashin fahimta ya mun, ban damu ba naci gaba da cewa
"Yanzu saboda Allah duk yanda nayi maka magana baka haƙura ba se da kace ta tafi? Haba Bilal, a zato na ko can wata bare ce tazo gidan nan cin arziƙi ai beci ka koreta ba balle ƙanwar ka uwa ɗaya uba ɗaya ashe ma duk faɗar da kake tana da matsayi a gurin ka duk surutu ne
gaskiya baka kyauta ba kuma ban ji daɗi ba gashi na kira wayar ta ma bata amsa ba nasan fushi tayi".

Kanzil bece mun ba, abu da me ciki abu kaɗan ke hasala ni u duk hidimomin su shara mopping yayi shirin aiki ya fita. Se da ya tafi na tuna ban tambayeshi zan fita ba, a waya na kira shi nace masa zanje gida na duba Amirah dan tayi zazzaɓi se yace na bari idan ya dawo se muje tare. Na sake gwada kiran Fadila ta buɗe wayar amma haka ta ƙaraci ringing bata amsa ba se na kira Abubakar dan hankali na ya kasa kwanciya ina so na tabbatar da lafiyarta tunda ko babu komai daga gida na ta tafi. Abubakar yace mun ta koma can gidan su taje tana kuka ya tambaye ta meya faru taƙi gaya masa sanin da zeyi baze wuce ita da Bilal bane shi yasa ma be biyo kadin dawowar tata ba kuma yau da safen ta tafi gidan Anty Amina babbar yayar su. Ni dai tunda naji tana lafiya shikenan can su ƙarata da ɗan uwanta shi ya kore ta ba ni ba.
Chapter 41 · 0% Book details