← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 156 OF 158

Sashe 156

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sai kace wanda ake korarku Halima gashi ko ruwan ma baki sha ba balle ki barsu suma su sha sai kace wanda suka zo baƙon guri ko baki gaya musu nan ɗin tushensu bane? Mu jininsu ne basu da sama damu?" Hajja ta faɗa. Kamar inyi shiru sai kuma nayi murmushi na kalleta nace

"Ina fa zasu manta tushensu Hajja? Ai idan ita Sharifa bata sanku ba shi Al'amin daya bar gidan da wayonsa ai ba zai mantaku ba. Ita ɗin ma da ace tana ganinku ba zata muku ƙiwa ba in da zataga Abubakar yanzu zaki san da gaske ta san jininta" ina rufe baki Abubakar ɗin yayi sallama tun kafin kuma na san su biyu ne ƙamshin turaren Dr Salman ya isarmun da saƙon.

Da gudu kuwa Al'amin ɗin ya nufi Kawunsa itama Sharifan ta zame tana kiran "Uncle" ya ɗaga su duka su biyun yana juyi dasu suna dariya. Sai na rasa jikin wanda ya fi wani yin sanyi tsakanin Bilal da Hajja musamman da Dr Salman ya ƙaraso ya zauna gefena. Suna gama gaisawa na miƙe ina nuna mata ledojin da muka shiga dasu shi kuma ya ajiye musu rafar 1k guda biyu na fita yana biye dani a baya dan Abubakar ya fita da yaran.

Amarya na tsakar gida ta shimfiɗa sallaya a inda rana bata tarar ba tana shan rake, na ce mata "Sannu" ta amsa mun da "Ina wuni" muga gaisa daga tsayen na mata jajen abinda ya samu Mijinta kafin nayi waje.

A soro Bilal ya tsayar dani, kamar wani mai jin tsoron kada a jishi kai a ƙasa ya ce
"Na san abubuwa da yawa sun faru a baya da ban samu damar wanke kaina ba Halima. Dawo da maganar bashida amfani amma ina so ki sani na gane kuskure na kuma yarda cewar na zalunceki a zamantakewatarmu. Dagaske nake miki wannan maganar tun daga ƙasan zuciyata ina mai neman gafararki Halima kiyi haƙuri ki yafe mun duk wani abu dana miki daga ranar da kika fara sanina har zuwa yanzu da muke tsaye. Ko ba'a faɗa mun ba na san abubuwa da suke faruwa harda haƙƙinki Halima. Na sakaki kuka sau babu adadi a sanda kike taredani tun bayan rabuwata dake nayi kuka sau babu adadi nim. A hankali abubuwa da yawa suna ta faruwa da suke ankarar dani girman laifukan dana ringa aikata miki wanda nake kallo a matsayin ba komai ba a wancan lokacin dan Allah kiyi haƙuri ki yafe mun" ya ƙarasa kamar zai durƙusa mun.

Murmushi nayi na ce
"Na daɗe da yafe maka Bilal, sau da yawa mu kanyi baƙin ciki idan wani al'amari ya samemu wanda kuma daga baya hakan sai kaga ya zame mana alkhairi amma bama fahimtar hakan da sauri har sai munyi haƙuri tukunna. Tsakanina da kai idan akwai mai laifi nice dana cusa maka kaina ta ƙarfi dukda ka yi iya ƙoƙarin ka gurin nuna mun baka muradin hakan. Kayi haƙuri ka zauna dani tsayin lokaci. A yanzu na fahimci ba'a yiwa so dole, sannan Soyayyar da kake so ake sonka ita ce soyayya"

Na nuna masa Salman dake zaune cikin mota nace
"Da baka barni ba da ban haɗu dashi ba hakan yana nufin da nayi asarar ingantacciya kuma nagartacciyar soyayya wacce babu algus a cikinta. Saurayine bai taɓa aure ba amma ya zaɓeni mai yaya biyu akan tarin yammatan da suke karakaina akansa, wannan kaɗai nasarace na kuma godewa Allah" daga haka na sa kai na fice na barshi tsaye yana bi na da kallo.

A hanya Dr ya kalleni ya ce
"Amma kika ce kinfi jin daɗi da Abbansu baya zuwa dubasu". Ba tareda na kalleshi ba nace
"Eh mana nafi son hakan"
"Ba gaskiya bane, idan kinfi son haka mai yasa kika nuna jin zafin rashin kulawar tasa kuma ɗazu a gabansa?"

"Ni kuma nayi me?" Na faɗa ina buɗe masa ido, shima buɗe idon yayi kafin ya ce
"Wai sai yaushe zaki daina sonsa kwata-kwata? Dame ya fini Halima? Ina zaune a mota ina kallonki kina ta washe masa baki har kina nunoni Allah kaɗai ya san mai kike gaya masa a kaina ƙila cewa kike ni maye ne na nace miki ko?"

"Ni dama na san kana kallonmu" na faɗa da sigar zolaya. Ya haɗe fuska kamar gaske yana cewa
"Wlh na raina ajinki ma dana ganshi sam ashe ma baki ga taste. Kalleshi ba sai kace wani sahorami fuska kamar mace. Dama ta yaya wancan zai san darajar mace kamarki? Da kike ta wahalar dani kike garani kamar wani ball na ɗauka zanga wani namijin gaske wanda ya fini banda girman idanuwa da tsinin hanci baya ga haka na kereshi a komai har ma abinda baki rigada kin sani ba duk na san zan fishi wlh dan daga ganinsa ba wani ƙoƙari zai yi na azo a gani ba".

Baya na fara kallo naga hankalin yaran gaba ɗaya yana kan Tab ɗin da suke kallo ko da ma ƙasa ƙasa yayi maganar na toshe kunnuwana biyu da hannu ina cewa
"Kai dai kaji tsoron Allah kuma ni a yaushe nace maka har yanzu ina sonsa?"

"Idan bakya sonsa akan me tunda aka ce an kamashi hankalinki yaƙi kwanciya? Kin ganshi a kotu amma dukda haka baki haƙura ba kika wani fake da yara saboda kizo ki ganshi yanzu dai hankalinki ya kwanta ko?" Yayi maganar yana kallona. Shagwaɓe fuska nayi ina kallonsa nace

"Amma dai ka san asirin da kayi mun ya ci dan bana iya cikakkiyar awa ɗaya ba tareda nayi tunanin ka ba" ya saki murmushinsa mai kyau kafin yace
"Ni dai kika asirce ina nan kuma ina addu'a Allah ya ɗorani a kanki kada ki mayar dani bita zai-zai dan tunda har Hajiya tace ta lura ina sonki dagaske na tabbata gaskiya duk inda kika kai sunana ba'a ci miki kuɗi a banza ba".

Tare mukayi dariya nace
"Haka fa yan office suke cewa wai daga zuwa na asirceka duk ga mata nan da suka kwashe shekaru a gurin babu wacce kake yiwa kallo biyu sai ni gani ɗaya zaka fara so na?"

"Sai ki ce musu dama ke nake jira shiyasa bana iya yiwa kowacce mace kallo biyu sai a kanki na fara". Ji nayi kaina ya fasu, yanda yayi maganar haɗi da mun wani kallo yana lumshe ido da yake tabbatar da gaskiyar abinda ya faɗa ya saka naji kamar in fasa ihun murna. Gidan Mama muka koma ina tsaye muna sallama Abba ya fito dan haka na shige gida na barsu suna gaisawa dariya ta kamani ganin Salman kamar zai kwanta a ƙasa ana gaida suruki.

"Kin je hankalinki ya kwanta dai ko?" Anty Labiba ta faɗa ina shiga, Mama Fauziyya ta tare mun tana cewa
"Menene laifi a ciki Labiba? Zuri'a fa ta rigada ta shiga tsakani babu yanda za'ayi a raba. Tunda kunce ba zamuje ba ba'a mata kara ba ai sai taje da kanta"

"Tunda wani yace yaja ya damfari mutane ina ruwanmu da zuwar masa jaje? Dama ai ita take da jiɓi dashi idan ma zuwan ne ita ya kama kuma taje" Mama ta goyawa Anty Labiba baya. Zama nayi tunda Mama Fauziyya na nan na san ba zata bari su mun rubdugu ba.

"Ina Dr ko ba tare kuka je ba?" Anty Labiba ta sake soko wata maganar, na ɓata fuska Mama tace
"A haka dai shima kamar Namijin gaske amma ya zauna yarinya ƙarama tana juyashi. Tsabar sakarci wai har zaman kotu ya rakata ashe, dama zan gayawa Mudassir idan ba dagaske yakeyi ba ya kama gabansa in kuma auren zaiyi ya fito ayi a wuce gurin tun bata mayar dashi shashasha irinta ba. Ni na rasa wannan azababbiyar soyayya da kike yiwa Bilal sai kace wacce ya wanke ya bawa ta sha" Mama ta sake faɗa cikin fushi.

Miƙewa nayi na wuce ɗakin Amirah ina jin Mama Fauziyya tana cewa
"Sai a hankali, irin su Halima suna da yawa fa kawai dan ita muka fara gani shiyasa abun ya zo mana a sabo. Idan suka so abu kafin su barshi gaba ɗaya sai sun samu madadinsa. Wuyarta ɗaya ta samu wanda zai ringa mata irin soyayyar da take ƙulafuci a gurinsa shikenan zai zama tarihi kuma idan ba'a yi wasa ba idan ta tsane shi sai a ringa roƙonta data sassauta ƙiyayyar. Kawai dai yanda kika ce idan auren zai yi ya fito ayi a wuce gurin".

Haka sukayi ta juya maganar ni dai na shige ɗaki na kwanta bacci na fara fizgata wayata dana ajiye a saman pillow da nake kwance ta shiga ƙara ba shiri na tashi zaune ina tura baki kamar wani ya ajiye mun. Salman ne, sai da ta kusa katsewa kafin na amsa da sallama ya amsa ya ce

"Abba ya ce in turo ko kina so ko bakya so ya bani ke, zaɓi biyu ki zuba ruwa a ƙasa kisha idan kina farinciki ko ki bari idan aka kaiki ɗakina ki haɗe zuciya amma karki mutu dan nima binki zanyi".

A gurguje
BILAL
Ganin da yayiwa Halima sai ya sake dawo masa da komai saboda, mutumin daya ganta tareda shi kuma ya tabbatar masa da cewar tayi masa nisa. "Dama da irin sa ta dace ba kai ba" zuciyarsa ta ringa ƙara masa zafi. Duk juyin da zaiyi sai ya tunata, idan kuma ya tuna ya da yaransa suka nuna basu sanshi ba sai yaji dagaske dai ya tasarma rasa komai a rayuwarsa. Ya rasa duk abinda ya mallaka, ya rasa Halimarsa sannan yana shirin rasa yaransa amma ba zai bari hakan ta kasance ba.

Haka ya cigaba da jinya tsayin wata guda baya zuwa ko ina hatta masallaci sai da Hajja tayi dagaske kafin ya fara fita tace zamansa a gida ba zai canza komai ba sai dai tunani da damuwa su ƙarasa kassarasu kawai. Ita yanzu kacokam damuwarta tana kan Fadila da kowa yake cewa wai ta haƙura ta ɗauke kai tunda dai Fadilar taji ta gani zata zauna a cikin uƙubar da take ita na menene zata ringa ɗora danuwarta ranta kullum jininta yayi ta hawa sama?
Chapter 156 · 0% Book details