← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 24 OF 158

Sashe 24

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Sun ƙare ai, saboda ina da markaɗe a ajiye shiyasa ma ban gaya maka" na bashi amsa. Bece mun komai ba muka koma muka ƙarasa cin abincin kafin ya shirya yace mun ze ɗan fita amma ba jimawa zeyi ba.
"Dan Allah na shirya mu tafi tare" na shiga yi masa magiya amma kamar kullum ya ce Aa. Tun waccen ranar da muka je gidan su da namu ko ƙofar gida ban sake fita ba ba kalar magiya da nacin da ban masa ba amma yaƙi. Kafin muyi aure idan aka ce mun Bilal Bilal zeyi kulle zan ƙaryata se gashi a take takensa na ga hakan. Da nayi masa ƙorafin duk sauran yan uwana da akayi mana aure tare sun je sun gaida iyayen mu ce mun yayi al'ada ce ba addini ba ni ba zani ba, abin da yasa na haƙura da na yiwa Mama mita tace na haƙura ai dama yayi wuri wata ɗaya ace na fara yawo. Ni yanzu gidan Anty Labiba na damu da naje, tun ranar da aka kawo gara bata dawo ba, a waya ma sau biyu ta kira ni akan wani saƙo da tace za'a kawo mun se bayan an kawo ɗin ta sake kira tayi mun bayanin yanda zanyi dashi. Ko a chat idan ba ni nayi mata magana ba bata kulani, nasan fushi takeyi dani shi yasa kuma nake so naje gida na bata haƙuri mu sasanta dan bazan iya jure fushin nata ba.

Ba yanda na iya tun da yace Aa haka na koma ciki na zauna rai na duk babu daɗi se dai kamar yanda yace be jima ba ya dawo da cefane harda irish potatoe da doya tun da yaga su ma saura kaɗan. Se da na aje komai in da ya dace kafin na koma gurin sa. Washe gari kamar kullum da wuri na gama haɗa abin karyawa na soya dankali da ƙwai se ruwan tea, har na gama komai Bilal na ɗaki be fito ba, ganinya kusa makara yasa na haɗa masa shayi dan ya huce kafin yazo sha na wuce ɗaki gurin sa. Seda na taimaka masa ya ƙarasa shiryawa kafin muka fito tare ina masa daru akan yayi kyau da yawa ina tsoron kar yammata su yi ta kallar mun shi a waje. Fusarsa washe da fara'a da alamu yana jin daɗin yanda nake kambama shi a ko da yaushe ina zuzuta kwalliyar sa. Se da na ja masa kujera ya zauna kafin 1na buɗe bowl ɗin dana zuba dankalin na janyo plate zan zuba masa,
"Meye wannan Halima?" Ya faɗa da ƙarfi har se da na razana. Jiki na ya ɗauki rawa na saki fork ɗin hannuna tare da dafe ƙirji na dake harbawa ina ambaton innalillahi wa'inna ilahi raji'un a fili tare da baza ido ko zan ga abin da ya saka shi wannan razanar haka amma iya hange na banga komai akan dining ɗin ko kewayen in da muke ba.

"Banga komai ba Bilal" na faɗa cikin rawar murya dan dagaske na tsorata. Cikin ɓacin ran daya nuna har kan fuskar sa ya nuna bowl ɗin dankalin yana cewa
"Wannan uban dankalin da kika soya waye ze cinye shi? Almubazzaranci zaki fara ko Halima saboda baki san zafin kuɗi ba baki san yanda ake neman su ba? Yanzu cikin mu mu biyu ne zaki soya wannan abun? Ko da yake baki da asara shi yasa, se ki zauna kici" daga haka ya miƙe ya saɓa jakarsa ya nufi ƙofa yana ci gaba da banbami. Ƙarar da ƙofa tayi bayan daya bugota ya dawo dani daga suman wucin gadin da mamakin Bilal ya sakani yi. Na sauke ajiyar zuciya me ƙarfi tare da jan kujera na zauna saboda ji nayi ƙafafu na sun yi sanyi kamar ba zasu iya cigaba da ɗauka ta ba. Se na rasa ma tunanin me zanyi, akan dankali dai Bilal yake kirana almubazza?

Buhu ɗayan da muka cinye a sati biyar be saka ya danganta ni da almubazzaranci ba se yanzu saboda na soya daga cikin kwano ɗayan daya siyo da kuɗin sa? Dankalin da yake cewa baya gajiya da cin sa, se muci da safe mu ci da rana da dare ma mu ci, Allah ke da kullum duk safiya har idan ya rigani shiga kitchen dankali ze feraye ko nayi marmarin doya idan ba shi yaga dama yaci ba se yace sedai kowa yaci abin da yake so amma shine yake mun tijara akan sa yau?

Ina nan zaune kusan awa guda gaba ɗaya kaina ya kulle har na rasa kalar tunanin da zanyi. Bugun get da kuma wayata da ta ɗauki ƙara yasa na tattara hankali na guri ɗaya ganin Hansa'u ke kiran yasa na miƙe dan nasan itan ce take buga ƙofa tun da mun yi magana tun jiya ta gaya mun yau zata zo ta kawo mun atamfa da kace ɗin ankon bikin ta da aka saka nan da sati shida. Fara'ar dole na ƙirƙira na ɗorawa fuskata bayan na buɗe musu ƙofa suka shigo tana mun mitar sun daɗe suna bugu kuma dan wulaƙanci tana kira ban amsa ba. Bana yanayin da zan ja magana se kawai nayi murmushi muka shiga falo. Ƙanwar ta Abida ce ta wuce kan dining kai tsaye tana cewa

"Ni wlh yunwa nakeji Anty Halima ban karya ba ta taso ni me kuka rage?" Bata ma jira na bata amsa ba ta dirar wa dankalin Bilal, Hansa'u zata hau ta da faɗa na hanata, ina lura da yanda take kallo na nasan baze wuce ta karanci damuwa tattare dani bane tun da kuma ban ce mata ba itama ba tayi karambanin tambayata komai ba, basu jima ba suka wuce bayan ta bar mun atamfa ɗaya da lace ɗin na zata ma wuni zatayi tace mun Aa yau take so duk wanda zata kaima ankon gida ta gama dasu. Abida bata daddara ba ta sake ɗaukko kwalin exotic a fridge tasha ta tafi da sauran, yana cikin lemon da Bilal yafi so kuma shi kaɗai ya rage kwali ɗayan ina kallon ta amma bazan iya cewa ta ajiye ba domin rowa ba hali na bace ba kuma zan koyeta a gidan aure ba sannan Abida na ɗauke ta ne kamar Amirah ƙanwa ta babu yanda za ayi na hanata wani abu da nake dashi.

Saboda yanda muka rabu da Bilal yasa na cire komai daga raina na yi masa girkin daya fi so kafin ya dawo na sake gyara gida na baza turare nima nayi wanka na cancaɗa kwalliya na kame a falo ina jiransa. Rai a haɗe sallama a ciki ya shigo falon, nayi kamar ban lura da yanayin sa ba na nufe shi ina masa sannu da zuwa. Be tare ni yanda muka saba ba be kuma gwasale ni yanda nayi zato ba se ya miƙo mun jakar hannun sa na karɓa ina murmushi tare da yi masa sannu da zuwa, yanda ya amsa ya sosa mun rai har naji idanuna suna neman su kawo ruwa amma na dake. Kitchen ya wuce na bishi da kallo kafin na wuce ɗaki na aje masa jakar sannan na shiga banɗaki na tara masa ruwan wanka. Ina ciro masa kayan da ze saka ya shigo ɗakin, kamar daga sama naji yace
"Kuma kika cinye dankalin duka". Na saci kallon sa shi ɗin ma ni yake kallo se nayi gefe da kai na nace
"Idan an barshi ai lalacewa zeyi". Ƙwafa naji yayi kafin ya shige banɗakin kamar ze tashi sama, ni se ma ya bani dariya. Abincin ma sama sama yaci ya ture ya shige kitchen, kamar ɗazu da safe ya sake kwazara mun kira saura ƙiris na ƙware da abincin baki na na maida shi cikin plate ɗin na tashi da sauri.

"Dan girman Allah Bilal ka dena mu irin wannan kiran bana so" na faɗa tamkar zan fashe masa da kuka ganin sa a tsaye jikin fridge, ya kalle ni kafin ya buɗe fridge ɗin yana nuna ciki yace
"Ina exotic ɗina?"
"Nayi baƙi sun shanye" na bashi amsa kai tsaye. Yanda ya yi mici mici da ido yana kallona se ka rantse iyayen sa na zaga.
"Shi lemon nawa kike gaya mun kin yi baƙi sun shanye?" Ya faɗa yana nuna kansa, Allah ya sani na fara zuwa bango. Wane irin abu ne daga dankali se kuma lemo se kace ana fatara ko tsiya?
"Baƙi nayi suka zo da yara ni ban ma sani ba muna falo suka shigo suka ɗauka kaga kuma babu yanda za ayi nace su mayar tun da dai abin nan munfi ƙarfin sa ba fatara akeyi ba" na bashi amsa ba tare dana kalle shi ba. Seda ya kwashi sakanni yana kallo na kafin yace
"Yayi kyau" ya fice daga kitchen ɗin ya barni a tsaye.
[12/30/2024, 6:48 AM] Hauwa Galadima: *KURA A RUMBU*
*(Based on true life event, some parts are fictional to spice up the story)*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*WOMEN OF WORDS WRITERS ASSOCIATION (WOW)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*

*Ban yarda wani ko wata ya juya mun labari ta kowacce siga ba tare da izini na ba*
*Kuɗin karatu yana wakiltar mutum ɗaya ne, kiji tsoron Allah karki ɗauki hakkina ta hanyar fitar mun da littafi*
*KURA A RUMBU littafin kuɗi ne, a biya naira 800, biya a asusun*
*1840175439*
*Access bank*
*Maryam Farouk, se a tura shaidar biya a lambar Whatsapp ta sama*
Chapter 24 · 0% Book details