← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 129 OF 158

Sashe 129

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

BILAL
Sai bayan Azahar ya farka dalilin surutai da ya ringa ji a tsakiyar kansa. Ya tashi zaune yana matse fuska, zazzaɓin daya kwanta dashi ya sauka amma kuma jikinsa sam babu ƙarfi ga hayaniyar data cika gidan daya rasa ta mecece, tashi yayi a hankali ya fita falo, yayi turus a tsaye ganin mata sun bararraje kamar a ɗakunansu suna cin abinci suna hayaniya sai kace masu cin kasuwa.

Wacce take saitin ƙofa ce ta ankara da tsayuwarsa tayiwa sauran alama duk suka juya suna kallon sa, kallon sa kafin waɗanda daɗin hira ya saka suka cire kallabinsu suka shiga ɗauka suna yafawa. Shi dai tsaye yayi yama rasa abinda zaiyi, yanzu ace duk girman falonta da ɗakuna biyu ga tsakar gida bai ishe su suyi didimarsu ba sai sun dangana da ɗakinsa? Tukunna ma mai suka zo yi?

"Baby ka tashi ashe" Zulaiha data shigo falon da ƙaramar kula a hannunta ta faɗa tana masa murmushi. Kallo ɗaya ya mata ya juya ciki haɗi da rufo ƙofa sai ta ajiye kular hannunta ta bi bayansa ɗaya daga cikin ƙawayenta ta ce
"Amma Zully baki da M, dama yana ciki shine kika kawo mu nan gashi mun saki baki muna ta zuba har Billy tana cewa zata shiga tayi kashi ashe Allah ya rufa mata asiri"

Dakatawa tayi tana ware ido ta ce
"Hirar me kukayi?"
"Ke labarin duniya ne kawai ba wani abu ba" wata mai kama da yan sholisho ta faɗa. Sai ta sauke numfashi ba tareda ta sake cewa komai ba ta shiga ɗakin.

Ƙarar ruwan da taji yasa ta zauna tana jira ya fito, ya mata kallo ɗaya ya wuce gaban mirror bayan daya fito daga ɗakin baƙin ciki goma da ashirin, shigen atamar jiya ce a jikinta, ashe ba leda bace kawai munin da atamfar tayi a idonsa ne ya sa ya ganta kamar ledar. Tashi tayi ta matsa kusa dashi ta rungume shi ta baya tana cewa

"Wai me ya faru ne kake ta ɓacin rai Baby?"
Ya tureta, bata haƙura ba ta ƙanƙameshi tana shinshinar jikinsa kamar wata mayya tana cewa
"Baby haba mana, kasan dai babu gurbin fushi a fuskar sabon ango"

Janyeta ta sakeyi bayan daya juya ya fuskanceta, so yake ya tuhumeta akan daren jiya. Ya zura mata ido, tabbas shi shaida ne Zulaihar dake gabansa a yanzu ba Zulaihar daya sani a baya bace akwai sauye-sauye da yawa a tattare da ita amma bai taɓa zaton bayan sababbin ɗabi'u da halaye da ya fuskanta a tareda ita ba harda na mutunchi da tarbiyyar da ya santa da su tun usuli. Gefe ya ɗauke kansa kafin ya buɗe baki ya fara magana sai dai a maimakon kalaman da suke kan harshensa sai yaji wani sautin daban, ya ɓige da cewa

"Wane irin raini da wulaƙanci ne ya sa zaki kawo mun wasu banzaye ɗaki Zulaiha?"

Ta haɗe fuska ta ce
"Ba banzaye bane ƙawaye na ne, kuma walima suka zo mun can falo na ya cika kuma su ɗin ko cikin ƙawayena na daban ne shiyasa na kawo su nan" ta bashi amsa tana kallon idonsa babu shakka balle tsoro.

Duk sai ya zama confused, ba abinda yake so ya tambayeta ba kenan bai kuna san sanda ya canza shawarar yin hakan ba amma kuma amsar data bashi a yanzun ta sake kashe shi da mamakinta har ya rasa abinda zai sake ce mata. Daƙyar ya iya cewa

"Su fita, ba su kaɗai ba ki sallami duk wata mace da kika tara mun a cikin gida kar na fito na tarar da ko mutum ɗaya idan ba haka ba" ya mata kallon data fahimci tsaf yana nufin zai yi rashin mutunchi ne.

Guri ta samu gefen gado ta zauna tayi ƙasa da kai kamar dagaske ta shiga cewa

"Tun daka shigo jiya kake ɓacin rai tamkar wanda zai shiga kabari, bama jiya ba, tun bayan da aka ɗaura mana aure ka canza. Gaba ɗaya ka zama wani abu daban da yanda na sanka, duk tarin alƙawarurrukan da ka yi mun na farinciki da kulawa idan na zama taka babu ɗaya daga ciki da naga yiwuwar faruwarsa sai wulaƙanci da ƙasƙanci da kake nuna mun.

A daren farkonmu Bilal haka ka tsallakeni kayi tafiyarka falo ka kwanta baka damu da wane hali nake ciki ba tunda ka rigada ka samu biyan buƙatar ka shikenan duk kuma nayi haƙuri na jure duk hakan bai yi maka ba yanzu so kake yi ka tozarta ni a gaban ƙawaye na ka ƙarasa nuna musu cewar bani da mutunchi ko daraja a gurinka ko?

Ni ba zan koresu ba amma kai ban hanaka ka fita ka koresu ba sai dai kafin nan ka fara sallamata dan ba zan iya wannan rayuwar ba" ta ƙarasa tana fashewa da kukan da ya jishi har tsakiyar ransa. Bai san sanda ya durƙusa gabanta ba dukda ya kasa ce mata komai ita kuwa kamar wacce ya saka bulala yana duka haka ta ringa kuka irin me shassheƙar nan tana nanata sai ya saketa tunda dama ya aureta ne dan ya wulaƙantata ba sonta yakeyi ba.

"Mai yasa kika ɓoye mun kin rasa budurcinki a waje?" Ya tattaro duka ƙarfin guiwarsa ya amayar da abinda yake cikinsa. Lokaci ɗaya kukanta ya tsaya ta ɗaga kai da sauri ta kalle shi da firgicin da ta kasa ɓoyewa kafin kuma ta sauke kai kamar munafuka ta sake fashewa da kukan daya fi na farko tausayi da narka zuciya. Cikin kukan muryarta na rarrabewa ta ce

"Ban sani ba"
"Kamar ya baki sani ba?" Ya faɗa cikin fushi sai dai kuma sautin muryarsa a ƙasa. Ta kife kai jikin gado tana cigaba da kukan da wanda bai san dawar garin ba dole ya tausaya mata kafin ta ce

"Ina shekaru bakwai a duniya wata rana Ummanmu ta aike ni da daddare siyo maganin sauro ruwa ya sakko na fake a wata rumfa, ban san wanene ba ban kuma san mai ya faru da ni ba amma Umma ta ce sai da akayi nemana na kwana uku kafin aka sameni a Asibiti kuma ma'aikatan Asibitin sun ce wata mata ce ta kaini tace musu tsintata tayi suka ce ba zasu karɓe ni ba sai ta zo da yan sanda shine ta ajiyeni tace zataje ta dawo daga nan basu sake ganinta ba kuma basu san daga wace unguwa ta kawoni ba balle a bayar da cigiya. A dalilin haka har lalurar yoyon fitsari na gamu da ita daƙyar da taimakon Allah na samu lafiya" ta sake rushewa da kuka.

Bilal da jikinsa yayi laƙwas yayi shiru yana kallonta tausayinta mai tsanani ya shiga ratsashi. Har ransa yaji ya yarda da abinda ta ce ya faru da ita, ya ɗagota jikinsa yana cewa

"Me ya sa baki taɓa faɗa mun ba?"
"Umma ce tace ba sai na faɗa maka ba, wai abun ya daɗe kuma ina yarinya lokacin"

Ya ɗago ta yana cewa
"Shikenan, amma ya kamata muje asibiti gaskiya a dubaki dan.." sai kuma yayi shiru, ta ce
"Saboda me?"
"Bana tunanin an dubaki da kyau a wancan lokacin ta yuwu kina buƙatar ɗinki" ya ƙarasa a hankali.

Kusan minti goma ya ɓige da rarrashinta dukda har ransa yaji ya gamsu da maganarta amma kuma ƙuncin da yake ji a zuciyarsa bai ragu ba dannewa kawai yakeyi yana rarrashinta. Ganin tana nema ta canza musu akala daga rarrashi ya saka ya tureta yana ɓata fuska. Bata ja ba itama ta kama kanta ta bar masa ɗakin babu kowa a falon dan suna shigewa ɗakin suka tattara suka koma can falonta.

"Kinga abinda na faɗa miki ko? Sai da nace kiyi ɗinki kika ce ba haka ba, anyi ɗinkin ma ya Allah ya cika wanda ma basu taɓa aure na suke ganewa balle shi toh yanzu mai kika ce masa?" Suwaiba ta faɗa taba zare ido bayan da suka shige banɗaki Zulaihan ta faɗa mata yanda sukayi da Bilal.

Sai da ta yarfe gumin da ya tsattsafo mata kafin ta labarta mata ƙaryar data shirya masa, Suby ta buɗe ido da mamaki ta ce
"Kuma ya yarda?"

"Hmmm ya yarda mana, wlh ni kaina nayi mamaki yanda ba jeka ka dawo lokaci ɗaya ya sakko bakiga yanda tausayina ya rufe shi ba" cewar Zulaiha. Suby ta zauna kan WC tana cewa

"Taɓ, kuma ba dai kawai shiru ya miki ba Zully?"

"Ke wlh ya yarda, in sa bai yarda ba na sani ba zaiyi shiru ba sai ya sake cewa wani abun ko kai tsaye ya ce ƙarya nakeyi. Yanzu dai ya ce zamuje Asibiti ayi mun ɗinki shine ma naji tsoro kar na je ko setup zai yi mun su tona mun asiri" Zulaiha ta faɗa muryarta da fuskarta suna nuna damuwa. Suwaiba ta ce

"Sai ta yuwu, amma ai ba zaki bari haka ta faru ba idanma niyyarsa kenan. Yanda kikayi wasa da hankalinsa a farko haka zaki ƙarasa wasan, ke zaki faɗi Asibitin da zakuje ko ma kawai ki kira Nurse Binta tazo gida ta miki baki alaikum idan ya nuna ba haka ba kice masa idan kukaje Asibiti ai zai zama kamar tonon asirinku in ma kuma Asibitin dai za'aje ba za'ayi a gidan ba to kuje in da take aiki asirinki a rufe babu wanda zai ji bare ya gani".

"Shiyasa nake sonki ƙawata haka za'ayi" Zully ta faɗa tana bata hannu suka tafa Suby ta ce

"Toh sai ki kama kanki ki kuma dakata karki sake shafa masa maƙale mata in ba haka ba wlh ya harbo jirginki da wuri"

"Yo ko baki faɗa ba dama ai ba zan sake ba" ta bata amsa.

Kafin la'asar ta sallami jama'ar data tara duk niyya sukayi har dare su sha budurin da basu samu sunyi ba ita da ƙawayenta a gidan dan dama bata gayyacesu yinin da akayi jiya ba tace su bari sai yau ɗin sa zo gidan tayi order abinci mai rai da lafiya kuwa ga snacks da lemuka iri iri suka ci suka sha sunata iya shegensu duk a zatonta Bilal ya fita dukda motarsa tana nan amma jin shiru tun bayan data kai masa kayan kari ya saka ta ɗauka ya bar gidan ne.
Chapter 129 · 0% Book details