← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 158

Sashe 37

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon kaina nayi sama da ƙasa ko zan ga abinda yayi kama da shirin tafiya ƙauye a jiki na amma ban gani ba dan haka na mayar da kallona kan sa nace
"Ban gane ba, me shigar tawa tayi?"
Ba amsa ni ba ya wuce gaban wardrobe ɗina ya buɗe ya shiga birkito kayan ciki yana cewa
"Malama ki cire wannan kin san in da zamuje da zakiyi wannan shigar salon ki zubar mun da mutunchi?
Hannu na harɗe kawai a ƙirji ina kallon ikon Allah. Lace ɗin da nayi kwalliyar kamun bikin mu ya janyo daga ƙasan kaya ya ware shi kafin ya watsa kan gado ya buɗe in da mayafai na suke yana cewa
"Wannan zaki saka". Se ma ya bani dariya, na matsa gefen gado ina cewa
"Wai ina zamuje Bilal?"
"Siyar da ke zanyi, malama ki yi abin da nace kawai kar ki ɓata rai da lokaci" ya faɗa yana aje mayafin daya ɗakko kan kayan. Se na ɗaga rigar nace
"Kasan dai yanzu wannan kayan baze shige ni ba, ka faɗa mun in da zamu je se na duba wanda zasu dace da fitar na saka"
"Walima zamu je" ya bani amsa a daƙile". Har na buɗe baki zan sake tambayar sa tame? Koma waye ya gayyace mu se dai yanda ya haɗe girar sama data ƙasa yasa na kama kaina na shiga lalubo wasu kayan tunda ya kushe atamar dana saka.

A motar Nasir daya karɓo muka fita, se da muka fara tsayawa a kantin Baby dream. A mota ya bar ni ya shiga bayan wasu mintuna ya fito hannu biyu riƙe da ledoji shaƙe da kayan jarirai ya ajiye su a back sit. Mamaki fal rai na baki na cike da magana amma babu fuska dole na haɗiye na zubawa sarautar Allah ido. Can cikin nasarawa gra ya kaimu wani gida. Daga get ɗin farko ma zuwa cikin gidan tafiya ce ta misali, yanda ya gaisa da masu gadin get ɗin na gane akwai sanayya a tsakanin su amma dukda haka a tsorace na ringa kalle kalle har muka isa in da ake ajiye motoci.

Kamar mara gaskiya na ringa bin bayan sa har muka isa entrance ɗin gidan ya dannan door bell, mun kusa minti bakwai a tsaye kafin aka zo aka buɗe, yanda kasan gidan su haka Bilal ya ringa jefa ƙafa ni kuma ina bin sa a baya, se da muka zauna kan wasu kujeru masu azabar kyau da laushi kafin na fahimci gidan Abokin sa Hafiz muka dalilin hoton su shida matar sa dake kafe jikin bango. A raina na raya ashe dai ba ƙarya Bilal yake ba idan yana santin irin arziƙin da Hafiz ɗin suke dashi, na ayyana yana da kuɗi haka ko me ya kaishi aikin gomnati kuma bama wani shahararre ba irin su CBN ko Oil ko porth authority naga can aka fi samun yayan manyan ƙasar a ciki.

Tun zuwan da suka mana ni na manta ma da babin su har idan ba shi ya ɗakko zancen su ba, matar ma da mukayi exchanging number sau ɗaya ta taɓa kirana tace sisters ɗin ta sun ji ƙamshin turaren wutar dana bata suna so na haɗa ta da me siyarwar (08033950747, kina neman turaren wuta me asalin ƙamshi da kama guri wanda duk wanda ya shaƙa seya tambayi in da kika samo shi? Ki tuntuɓe ta) shikenan bamu sake magana ba. Da ina ɗan ganin ta a whatsapp daga baya kuma na dena ganin ta ma na zata yanda ta sake dani sanda suka zo zamu yi doguwar mu'amala kamar yanda Bilal yake fata toh kuma hakan bata kasance ba.

Se da mukayi jiran kusan wasu minti goman har seda Bilal ya kira maigidan a waya kafin suka fito yana saɓe da baby tana bin sa a baya. Na ringa hasaso sanda suka je mana ni dai bangan ta da ciki ba ko kuma lura ne banyi ba oho dai gashi nan ta haihu. Farat farat kamar karon farko muka gaisa, tace mun
"Baki da kirki Halima, na rasa number ki ke kuma ko sau ɗaya baki ce kinji ni shiru bari ki taɓo ni kiji ya nake ba ko dai zumunchin ne bakya so muyi?"
Kafin na bata amsa Bilal yayi caraf yace
"Ai itama wayar ta ta lalace ne, tuntuni kuma tace na karɓo mata number gurin yallaɓai se in manta" Hafiz yace
"Kai dai kace zaka kare ta kawai amma zuwan ka nawa gidan nan kuna haɗuwa ai ko ka manta ya kamata ace idan ka ganta ko sau ɗaya ka tuna saƙon da aka baka". Ni dai sakin baki da hanci kawai nayi ina kallon Bilal jin wannan gingimemiyar ƙarya daya shirga an kuma kama shi. Na sha mamakin jin wai yana zuwa gidan ashe, lallai se a bar Bilal. Ashe shi yasa ba'a ko tambaye mu daga ina ba aka bar mu muka shigo, ko me yake zuwa yi se Allah.

Mita Suhaila taci gaba dayi ni dai na bita da ban haƙuri ina riƙe da kyakykyawan babyn ta me suna Muhammad Sani sunan babanta suna kiran sa Na'im. Duk tarin kayan ciye ciyen da aka cika mu dasu ruwa kaɗai na iya sha a ciki, se da muka shiga ɗakin ta ta dame ni da se na faɗi abin da nake ra'ayi an mun tunda ta lura ba ni kaɗai bace baze yuwu na zo gidan banci komai ba. Dankali nace a soya mun dan na kwana biyu ban ci ba tun azumi. Se bayan sallar Isha'i muka tafi gida shaƙe da kayan arziƙi harda naman suna kusan cikin ƙaramin bokiti a haka ma tace wai ya ƙare ne haihuwar kusan kwana talatin ni dai nace an gaida masu kuɗi ko raguna nawa suka yanka se Allah ko kuma dan basu da yan uwa da yawa a Kano ne tunda mu na gidan su Bilal ma ko hanji ban gani ba cewa akayi mutane sunyi yawa akan naman ya ƙare dama kuma dabbar ƙarama ce batayi auki ba.

"Ki san a Egypt ta haihu se ranar idi suka dawo yace baya so azo ayi ta jagwalgwala masa yaro shiya sa suka yi zaman su se da ya ɗan yi ƙwari. Yan gidan su can a Kaduna sukayi suna na zata ma da suka dawo gida zata wuce wai su basa haka ashe ba'a zuwa wankan gida" Bilal ya faɗa bayan da muka hau titi. Na gyaɗa kai tare da cewa
"Allah sarki, zuwa wankan gida dama ai ra'ayi ne kuma ma yanzu duk an dena ai kowa a gidan ta take zama tayi jegon ta"

"Wanda suka de na dai sun dena mu kuwa a dangin mu kwana sittin ma akeyi ba arba'in ba" ya sake faɗa, se da juya na kalleshi da mamaki nace
"Wato kwana sittin ma? Kai yanzu idan na haihu se ka yarda na tafi gida nayi har kwana sittin bana tare da kai?"

Ido ɗaya ya kashe mun kafin yace
"Nasan dai zan azabtu da missing ɗin ki amma ya zanyi da abin da al'ada ta gindaya. Kwana sittin ɗin ma fa bayan an haihu ne wannan lissafin naga matan su Yaya Suleiman da haihuwar fari da cikin su ya shiga wata tara suke tafiya gida. Kinga kamar Anty Mariya da take ba yar gari ba ina ga se da tayi wata uku ma ita sannan ta dawo ai to ke tun da a kusa kike da kafin haihuwar zuwa bayan haihuwar se kije kiyi arba'in biyu kawai, wai ma wata nawa ne cikin yanzu?" Ya ƙarasa yana ɗora hannun sa akan cikina.

Al'ajabi da mamaki suka sa na kasa cewa komai se bin sa da ido dana ringayi ya kuma yi mirsisi abin sa yaci gaba da tuƙi yana soko mun wata hirar. Mamakin nawa biyu ya kasu, na farko wai ashe ma ya tabbatar ina da ciki amma ko da wasa ban ga wata murna ko zumuɗi a tattare dashi ba sannan kuma yanzu lissafi yake idan na tashi haihuwa gidan mu zan yafi nayi arba'in har biyu wato lallai bani da wani muhimmanci a gurin Bilal. Ji nayi raina ya ɓaci take hawaye ya fara cika mun ido, jin nayi shiru bana amsa hirar da yakeyi yasa ya kamo hannu na yana cewa
"Bacci kika yi ne ina ta magana kinyi shiru?" Aiko kamar ina jira se hawaye shaaa suka ɓalle mun, "subhanallahi Halima me kuma ya faru?" Ya faɗa yana gangarewa gefen titi. Haɗe kai nayi da guiwa na shiga rera kuka kamar wadda aka daka.

A karon farko tun auren mu naga rikicewar gaske tattare da Bilal akan ɓacin raina. Fita yayi ya zagayo ta in da nake na durƙusa kamar zeyi kukan shima yana roƙon na gaya masa mene ne. Se da nayi me isata kafin nace
"Yanzu saboda baka farin ciki da kyautar da Allah yayi mana shi yasa ko a fuska baka nuna mun ka sani ba, ni kaɗai nake shirme na kai ko a jikin ka" na sake fashewa da kuka. Se ya dafa kai kafin ya miƙe yana murmushi ya koma mazaunin sa.
"Na lura so kike kiyi surprising ɗina shiyasa nake acting along kar na ɓata miki shiri amma da na san ranki ze ɓaci akan haka da tun sanda na gane nayi magana. Kuma Allah ba wani daɗewa akayi ba, ranar da kika ce na siyo miki mangwaro ne shine nayi suspecting kuma dama na lura ba kiyi period da azumi ba. Nasan akwai shirin da kike yi da ya sa baki gaya mun ba kar nayi magana kuma na lalata miki" yayi maganar ta sigar da ko ba gaskiya ya faɗa ba dole na yarda da abin da yace. Har kaza ya siya mun ƙatuwa da yoghurt me sanyi, da muka isa gida kuwa a hannu ya ɗauke ni har da yi mun rawa wai dan na yarda yana murna da ƙaruwar da muka samu.
Chapter 37 · 0% Book details