← Book details Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 147 OF 158

Sashe 147

Kura A Rumbu Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Duk su biyun sunji ƙarar marin daya kifa mata da ihun data fasa kafin ƙofar ta ƙarasa rufuwa, da yake window duk a rufe suke kuma basu ji cigaban abinda yake faruwa ba, Anty Habiba taci burki tana cewa
"Amina kinji abinda naji? Kamar fa marin ta yayi?"

"Sai ki koma ki rama mata tunda dama dake aka haɗu aka tura motar" Aminan ta bata amsa tana nufar get, Habiba tabi bayanta tana cewa

"Na shiga uku, wlh mutumin nan shigo-shigo ba zurfi yayi mana daga ganin Fadila tana cikin tashin hankali wlh kuma a haka zamu tafi mu barta?"

"Ni dai kin san bakuyi shawara dani ba sanda zata aureshi, hasalima sai ranar ɗaurin aure naji sunansa na kuma fara ganinsa dan haka yanzu kada wanda ya tsomoni a cikin shawarar yanda za'ayi dan ban zan hawa ba ba za'a nemi gangara dani ba" ta faɗa tana buɗe motarta. Har suka isa gida kuwa da kunne take sauraron Habiba dake ta amma bata tanka mata ba, sai da suka je ƙofar gidan Hajja kafin tace mata

"Kinga idan kika gayawa Hajja na ɗaya zaki tayar mata da hankali ƙarshe hawan jininta ya tashi sa'annan ita kanta Fadilan ki ƙara jefata a wani taskun dan dai ganin idonki kinga alamar baya buƙatar kowa yaje masa gida itama kuma ta yarda da hakan domin da tsarin bai mata ba ai tana da ƙafafu ba kuma kulleta yakeyi ba zata nemi hanyar gida da kanta, ke ko kulleta yakeyi har idan taga zaman bai mata ba zata nemi mafita dan haka ki kama bakinki kawai.

Hajja ta washe baki jin sun samu Fadilan kuma sun ce lafiyarta ƙalau kafin tace
"Ja'ira wato ita miji daɗi, toh ya na ganku hannu na dukan cinya? Bata bayar da komai a kawo mun bane ko kuwa a mota kuka manta?"

"Tace zasu zo a cikin satin nan ai" Anty Amina tayi saurin bata amsa ganin Habiba ta buɗe baki, sai ta taɓe baki tace
"Ai shikenan Allah ya kawo su lafiya". Ta ɗaga pillow ta zaro takardu ta miƙawa Amina tana cewa

"Kuna fita waccen yarinyar matar Bilal tazo, to dai itama tace tun ranar Juma'a tana gidan kai amarya ya kirata yace daga can ta wuce gidansu wai tafiyar gaggawa ta kamashi idan ya dawo zaije ya ɗakko ta, toh mayyar bata tafi ba ta zauna. Ni nafi zaton Abuja ya tafi gurin waccen ɗaya shaiɗaniyar Bilal dai ba zai daina sakani magana ba".

Su kuma takaddun na menene?" Anty Amina ta tambaya tana juya takardun hannunta, Hajja ta watsa hannu tace
"Na iya karatu ne ni balle ki tambayeni? Shiyasa ai na ajiye su ina jiran Abubakar ya shigo tunda kun rigashi sai ki buɗe ki gani ƙila sakinza tayi".

Anty Amina da Habiba suka kashe da dariyar maganarta, wai ƙila sakinsa tayi, Hajja kenan ko a ina mace take sakin namiji sai Allah.
Dariyar Anty Amina ta katse ta ɗora da salati tana duba takardar Hajja da Habiba suka zuba mata ido da son jin ƙarin bayani dai dai lokacin kuma Abubakar yayi sallama tareda Abdullahi babban ɗan Anty Aminar duk suka shiga sahun masu tambayar mai ya faru?

Abubakar ta bawa takardar, ya gama karantawa ya ninke yana cewa
"Allah ya rufa asiri amma dama na san sai anyi haka?"

"Sai anyi haka dame? Wai mai aka rubuta dan ubanka ka wani ninketa ba kai mana bayani ba?" Hajja ta zaburo masa, ya zauna yana cewa

"Sammaci ne daga kotu, gidan da wannan budurwar tasa ta siya ya siyarwa da wani mutum ba tareda ta sani ba, yanzu kuma ita ta siyarwa wani dan haka wanda ya siyarwa ya makashi a kotu bisa zargin damfara. Ɗayar takardar kuma ita budurwarce ta yi ƙararsa itama akan zargin sata, da kuma yaudara da zamba cikin aminci".

"Amma Allah ya tsinewa wannan yarinyar Jalilah, dama ashe ta shigo rayuwarmu ne dan ta jefa mu a masifa ta lalata mun ɗa shine yanzu zata masa sharri ta haɗashi da hukuma saboda bai aureta na ko me?"

"Wlh na sharri ta masa ba duk abinda ake zarginsa ya aikata da bakinsa duk ya faɗa mun, yanzu dai ku nemo shi kawai dan wannan sammacin ma na biyu ne kuma da gargaɗi kotu zata iya ɗaukar kowanne mataki idan bai bayyana gabanta nan da kwana biyu ba" Abubakar ya sake faɗa yana duba takardar. Hajja ta fashe da kuka tana salallami duk sai jikin Anty Amina yayi sanyi tace

"Ba kuka zakiyi ba Hajja addu'a ya kamata kiyi"

"Yana zaman-zamansa yana lallaɓa rayuwarsa da yar matarsa haka kawai ya rakitowa kansa masifa, ina amfanin tarayya da wannan shaiɗaniyar yarinyar gashi yanzu tana nema ta tozarta mu ta jefa shi a masifa? Ni wlh tun ganina da ita dama hankali na bai kwanta ba, kawai dan shi ɗin yace ba komai ne amma dama matan Habuja tun duniya na kwance ma makiraine, mutanen da suke kashe mazajensu dan suci dukiya balle kuma yanzu da duniya ta tashi tsaye makirci ai sai wanda aka gani ni dai Allah ya isa tsakanina da ita wlh" Hajja ta sake faɗa cikin kuka.

"Daga baya kenan, yanzu dai ki gwada duka layukansa da kike dasu ki faɗa masa ya dawo ayi komai a mutunche idan kuma ya zaɓi asirinsa ya tonu kowa ya san halin da ake ciki shikenan" Abubakar ya faɗa yana ficewa.

Anty Amina ce ta shiga kiran wayar Bilal amma layukansa biyu da take da duk aka ce a kashe suke, ta kalli Hajja dake sharɓar kuka kamar yar yarinya tace
"Hajja baki da wani layin nasa ni na kira wanda nake dasu duka a kashe"

"Guda biyu ne MTN da Airtel nima su ɗin ne" ta bata amsa tana fyace majina. Anty Habiba ce tace

"Toh kin tambayi ita matar tasa ko ta san inda ya tafi?"

"Tace dai bata sani ba amma ban sani ba ko ƙarya takeyi" Hajja ta bata amsa dai-dai nan Abubakar ya dawo falon ya zauna yana cewa

"Kun same shi?"
"Aa duka layukansa a kashe suke" Anty Amina ta bashi amsa a sanyaye, ya ce

"Ku kira Anty Halima ko zaku samu wata number".

Su ukun suka haɗa baki gurin cewa
"Halima?"
"Eh, akwai wani layi da ya ɗan yi amfani dashi can da daɗewa, na duba shi naga banyi saving ba amma ƙila a samu a gurinta ita" ya sake faɗa.

"Ga matarsa wacce Halima za'a samu number sa a gurinta?" Anty Habiba ta faɗa, ya kalleta ya ce

"Kada kiyi mamakin ta san inda yake yanzu haka"

"Sai ta yuwu dan zata rufa masa asiri ko mutum ya kashe" Hajja ta faɗa a sanyaye, ya miƙe yana cewa

"Kuma da Kinsan da haka kika goya masa baya ya rabu da ita, matar da duniya ma ta shaida abokiyar rufin asirice. Ai dai wlh ya tafka asara, gashi nan ya ƙare da yan balaja'u a gida da waje".

"Ni dai ba zan kirata ba wlh" Anty Amina tayi saurin faɗa ganin Hajja na kallonta, sai ta ɗauki wayarta tana cewa
"Buɗo mun lambar ni na kira".

HALIMA
Ajiye cokalin hannuna nayi ina ɓata fuska nace
"Ni dai ka daina kallona idan ba so kakeyi na ƙware ba"

Ɓata fuska yayi ya ce
"Na gaya miki ba zan iya daina kallonki ba Leemah". Sai da na lumshe ido kafin na buɗe su akansa ina cewa
"Toh na ƙoshi" yayi saurin tashi daga kan kujerar sa ya nufo ni yana cewa

"Ai kuwa baki isa ba, harfa kakarin amai kikeyi saboda yunwa kuma ko spoons biyar bakiyi ba kice kin ƙoshi? Ashe zan yi miki ɗura kuwa" ya ƙarasa yana naɗe sleeve ɗin farar rigar jikinsa. Ji nayi kamar in tashi na taka rawa amma na kanne na ɓata fuska nace

"Allah Uncle Salman na ƙoshi, ka fa bani tea ko ka manta?"
Ƙarar da wayata dake aje kan table tayi ya saka duk muka kalli gurin, sunan Hajja na gani yana yawo, na ɗago wayar ina buɗe ido dan na tabbatar da ita ɗin ce ko kuma idanuwane suke gizo? Ganin kiran na neman katsewa ba tareda na amsa ba Dr Salman dake tsaye kaina ya zare wayar daga hannuna ya amsa tareda sakata a speaker.

Muryar Hajja ta cika kunnuwanmu ta rafka sallama kafin tace
"Hello Halima kina ji na?"
"Ina jin ki Hajja ina wuni?*" Na faɗa bayan dana amsa mata sallamar, ta amsa da
"Lafiya lau, ya su Aminu da Sharifa? Duk suna lafiya ko?"

Sai naji wani banbarakwai, ashe sun san da yayansu a hannuna? Shiru nayi ban amsa mata ba ta cigaba da cewa
"Dama lambar Bilal nake so ki tura mun, banda Mtn ɗin sa da Airtel idan kina da wata daban su duk ba'a samunsa a su"

"Ai ni banida kowacce number sa ma yanzu Hajja" na bata amsa a dake, tayi shiru kafin tace
"Abubakar yace ba zaki rasa ba, ki taimaka wata matsala ce ta taso kuma ana ta nemansa a waya ba'a samunsa idan kuma kin san inda yake kawai ki faɗa mana aje a same shi"

Na saci kallon Dr Salman daya koma kujerarsa ya kafeni da ƙananun idanuwansa kamar farin shigar maita kafin nayi ƙasa da kai nace
"Sai dai ki kira Yaya Nasir ba zai rasa sanin inda yake ba ko ya baku number" sai tayi jumm kafin tace

"Shikenan, kya gaida Mamarku sai anjima" daga haka ta katse wayar.

"Tashi mu tafi toh" Dr Salman ya faɗa yana miƙewa tsaye. Na kalleshi, fuskarsa ta canza, yar fara'ar da yakeyi tunda na shiga office ɗin duk ta gudu ya dawo boss ɗin sa ga ƙananun idanuwan sun sake ƙanƙancewa. Ganin banida niyyar tashi ya saka ya wuce yana cewa

"Ki sameni a mota" ya fita ya barni.

Kada wadda ta tambayeni mai yake faruwa ko yaushe aka fara? Nima ban sani ba kuma daga nan zamu tashi 😂😂😂😂
[6/5, 9:14 AM] Hauwa Galadima: *KURA A RUMBU*

*LABARI/RUBUTAWA MARYAM FAROUK (UMMU-MAHEER)*
*Whatsapp 07061838488* *Arewabooks @Maryamfarouk01*
*Wattpad @MaryamahMrsAm*
*TikTok @Maryamfarouk_Ummu-mahir Novels*
Chapter 147 · 0% Book details