← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 145

Sashe 98

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Saidai abinda ya bashi mamaki daya gama fad'a masa sai yaji yayi shiru bai tanka ba haryai tunanin ko ransa ne ya 'baci amma daya d'ago sai yaci karo da murmushi akan fuskarsa yana kallon malam Habun da mamaki tsantsa ya'ki 'boyuwa a tare dashi yace.

"Haka ne malam Abubakar naji jawabinka kuma na gamsu sannan nad'au 'kaddara Allah ya mayar min da dubunta karka damu ba kaine mutum na farko wanda aka kar'be adedeta na a hannunsa ba inada yara masu min hayar Napep zasukai su arba'in amma maganar da nake maka an 'kwace min Napep yafi qarfin a kirga tun ina lissafawa harna gaji na daina tunda bashi da amfani lissafin dama haka ne dole wata rana in kana da kaya jarrabawa ta shigo ciki sai kaga abinda zai sameka ya samu kayanka babu damuwa malam Habu zuwa nan da karfe goma idan na shirya zuwa office zanyi maka magana muje store ka sake d'aukar wata Allah ya kiyaye gaba su kuma masu kwacen Allah ya shiryesu".

Malam Habu yaji matukar dad'i sosai kuma ya yaba dakyan zuciyar Alhaji Musa baiji kwanciyar hankali da sanyi aransa ba tun jiya sai yanxu da yazo sukai magana ko abinci bai samu jiya yaji ba da dare yadda aka kawo masa shi yana nan a rufe a d'akinsa humm da harya fara tunanin da yadda zai biyashi kud'in adedeta😥 .

Komawa gida yai ya fad'a musu suma sai lokacin suka samu kwanciyar hankali daga nan aka fara gyara gyaran gida mai girki ta d'ora abun kari yan makaranta kowa tai shiri bayan sun karya suka tafi domin yanxu Hajiya tace su ri'ka bari idan su dawo a school sai suzo gurin aikin tunda itama da safen bata nan tayi office saidai ranar weekend ne suke zuwa tun safe sukai daidai lokacin zuwa islamiyyah saisu mata sallama su tafi.

TANKO/MUDI🏕️
Zaune suke gaban boka wanda idonsa ke rufe sai surutai yake suna sauraronsa saidaya gama kafin ya bud'e ido yace.

"Ina jinku da me kuka zo yau"?.

Kallon juna sukai suna jinjina kai Tanko dayai gyara murya yace "ran boka Hambuwa ya dad'e dama matsala ce ta sake kawo mu yauma kamar kullum duka dai akan wannan mutumin wancan siddabarun dakai masa ya sameshi mu kanmu shaida ne mun gani da idanuwanmu a tsiyace ya dawo gida bai shigo dako naira biyar ba hatta abokinsa wanda suka tafi tare saida abun ya shafeshi to yanzu kuma ana cikin haka rana tsaka ya tashi yabar gari shida iyalansa bamusan inda ya tafi ba boka tsoron mu kada muje mu saki baki kwatsam mu ganshi ya dawo qauyen sannan ya zama mai arziki shiyasa muka zo gurin ka zamu baka komai da kake so amma kada ka barshi ya ri'ke koda naira biyar tasa balle ya tara wani abu wanda zaiyi alfahari dashi muna so kasa duk abinda ya ta'ba koba nasa bane abun ya narke ya zama dai komai yayi masa zafi bamaso yaji dad'i har karshen rayuwar sa".

Kai boka ya jinjina yana cewa "kun taki sa'a kunzo a daidai lokacin daya dace domin maganar da nake muku a halin yanzu ma yana cikin kwanciyar hankali dajin dad'i a inda yake babu abinda ya nema ya rasa komi a wadace yake".

Zaro ido sukai cike da firgici Mudi dake girgiza kai yace "inaa boka hakan bazai ta'ba faruwa ba jin dad'in nasa nadan lokaci ne bama so ya sake koda d'igon murmushi ne a rayuwarsa a sanya masa ba'kin ciki da rashin sukuni har abada sannan ka tura masa aljani shed'ani ya d'ora masa masifu iri iri kada ya barshi ya huta kuma hatta wadannan 'ya'yan nasa kada a barsu suyi aure boka haka muke so".

Ihu boka yai yana cewa "an gama za'ai komai yau kamar yadda kuka bu'kata zai shiga damuwa da 'kunci har abada sannan za'a dad'a masa rariyar hannu komai zai ta'ba saiya narke baza'a barshi ya sake ba".

Kai Tanko ya d'aga "yauwa boka Hambuwa hakan nake son ji ko hankalina zai kwanta amma taya za'a ce malam Habu zai yi arziki ina raye tabd'i humm wallahi bazan bari ba so nake komai ya sa hannu akai ya zama kamar ansa wuta ya 'kare abunda ya tara a zuwansa boka ka tura aljanu su 'koneshi sannan me zamu kawo maka abun ladan aikin"?..

Dariya boka yai yana cewa "babbakakken bunsuru shi zaku kawo kullum tsawon wata d'aya shine ladan aikin".

Kai Tanko ya d'aga "shikenan boka za'a fara kawowa daga gobe wannan ba matsala bace tunda muna da kud'in mu bamu da damuwar komai bamu rasa komai ba mu taka kowa mu murtsuke ba yadda aka iya damu mun zama gagarau nan gani nan bari d'umamen mayya😨 tashi mu tafi Mudi boka saika ganmu gobe da babbakakken bunsurun ka🐏 za'a kawo maka shi tun yana kan zafinsa kamar yadda kaima kake mana aikin mu da d'umi d'umi" Tanko yana gama fad'in haka suka tafi suka bar boka yana surkullen aikin asirin dazai yi musu wanda zai aikashi kan malam Habu😥.

🚶🚶🚶🚶🚶
Tafiya dai tafiya sakewa Malam Habu adedeta baifi wata takwas ba tsautsayi ya sake shigowa ciki wani mai mota ya bugeshi ya fad'i adedetan ta mammokad'e ya d'an samu ciwo kad'an a jikinsa mutumin ya bashi ha'kuri sannan ya kaishi asibiti ya biya kud'in maganin ya sake daukoshi ya dawo dashi gida ganin yadda yake da iyalai yasa mutumin bayan ya koma gida ya kawo masa kayan abinci masu yawa harda taimakon suturu masu tsada duk da kunce ne amma bazaka ta'ba cewa an sasu ba sai tashin kamshin turare suke umm kayan alhazawa malam nan ma dalilin wannan abu malam Habu yayi samuwa a gurin wannan mutumin ya dagoshi Sosai harda jari ya bashi.

Dan haka daya warke yacewa Alhaji Musa kada ya sake bashi adedetar sa domin shi dama sana'a bata kar'beshi ba yana ta'ba kaya ake samun matsala yanzu wacce sana'ar zai kama Alhaji Musa ya bashi shawara kawai ya saro kayan shago zai bashi kwantaina ya zuba ko Allah zaisa ya dace.

Haka malam Habu yai yaje yayo sarin kaya mai yawa ya cika kwantainar fal kuma kamar wanda yai Kiran kasuwa haka jama'a ke rubibin shagon saidai fa ba'a ci nisan zango ba shago yayi hayam babu kaya ba kud'i kamar ansa wuta an 'kone malam Habu ya shiga rud'u sosai ganin bashi da damar yai sana'a ta gari yayi bakin ciki ya kara.

Alhaji Musa ya sake bashi jari a karo na biyu duka dai sai an fara abu ciniki caf caf kamar gaske sai kud'i ya narke daga nan nefa abu yayi yawa komai malam Habu ya ta'ba saiya narke damuwa goma da ashirin ta dameshi dan haka Alhaji Musa yace yasan wani malami ya shirya suje gurin sa su gani ko saka hannu ne farko malam Habu bai amince ba yace ba saka hannu dama ya dad'e idan ya ta'ba abu saiya zama babu kamar mai rariyar hannu daga baya ya yarda suka je yayiwa malamin bayanin komai abinda ke damunsa da rayuwar dayai a bayan domin malamin ya tambayeshi da fari yaya mu'amalarsa da iyayensa sun rabu lafiya yace masa eh dan haka malamin yace to indai ba hakkin iyaye ne ke bibiyarsa ba akwai wani abu a kasa zai masa istahara zuwa nan da jibi su dawo zai fad'a musu komai godiya sukai masa suka dawo gida haka malam Habu yayita zulumin Allah yasa dai lafiya gabadaya ya hana kansa sukuni Allah Allah yake su koma yaji meke faruwa dashi.

Bayan kwana biyu Alhaji Musa ya d'aukeshi a motarsa suka koma kamar yadda malamin yace masu su dawo saida suka gaida dashi suka samu nutsuwa sannan ya fara koro musu bayanin abunda ya shigewa kowa duhu harda shi uban gayyar (malam Habu).

Yace musu tabbas akwai 'boyayyan abu a jikin malam Habu tun shekarun da suka wuce a baya an turo masa muyagun mugayen baka'ken aljanu masu had'ari sun shiga jikinsa duk wata damuwa da tashin hankali su suke sakashi a ciki sihiri akai masa dasu asiri akai masa wanda aka hada da gashin kansa akai shiyasa asirin bazai ta'ba barin jikinsa ba saidai in mutuwa yai amma hanya d'aya za'a iyabi a kawar da komai hanyar itace za'ai kokarin rabashi da aljanun a masa magani asirin yabar jikinsa domin shed'anun zamansu dabam asirin ma zamansa dabam kowanne yayi mugun karfi da tasiri a jikinsa saboda shekarun da aka d'auka abun nacin jikinsa fitar da aljanun yana da wahala saboda kafurai ne kuma masu taurin kai shiyasa za'a fara da karya asirin tukuna idan an dace sai a dawo kansu insha Allahu komai zaizo karshe za'a fara bashi magunguna yana yi kuma kada ya tsallake koda rana daya yabi umarnin maganin zai dace sannan malamin yace shi baya kar'bar abun sadaka sai anyi an warke dan haka sukai masa godiya daga ranar ya fara aikata duk abinda malamin ya bashi ya kuma bashi addu'o'i kala kala safe da yamma yanayi ba tsallake.
Chapter 98 · 0% Book details