← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 145

Sashe 25

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon ta Baffah keyi cikin tausayawa da rashin jin dad'in ganin yadda take kuka kamar ranta zai fita ya shiga jin wani irin d'aci na masa yawo a makoshi kirjinsa na zafi a fusace ya mi'ke yana zuwa kofar d'akin Ramatu yace "ke Ramatu kina ina? Caraf Ramatu ta bankado labule tana cewa "ga yar mutum biyu jikar mutum hud'u me ya faru ake nema na"? Ran Baffah a 'bace yace "kinsan Allah Ramatu ranki zaiyi mugun 'baci akan yarinyar nan sam babu d'igon imani a tare dake saikin kashe ta da 'kuncinki da kike sanya ta ciki to bari kiji yau kam kin kaini bango kibi a sannu zan iya yin komai".

Shewa Ramatu tai "ahayye nanaye yau ake yinta tofa ran maza ya 'baci lallai malam wato nan din me kake son nunawa zakasa nayi abinda banyi niyyar yiba Lami ce nace na sallama ta yadda ta za'bi tabi bare to yanzu ma haka ta dauka baren ya fini ta koma gunsu nace babu ni babu ita har raina haka abin yake babu kuma wani abu da zai canza".

"Haka kikace ko Ramatu"?.

Tana kad'a kai kamar zata hau bori tace "eh nace hakan malam, meye ko kana tunanin zanji tsoron kane? Nasan karshen abun bazai wuce kace zaka sake niba kuma ni yanzu dama haka nake so na samu 'yanci na nayi yawo a gari naci uban kowa na taka na murshe na wanke biyar na tsoma goma na fantama duk inda raina yake so" shiru Baffah yai na d'an wani lokaci kafin ya juya yana kallon Lami da har lokacin take kuka yace.

"Ramatu idan har baki yafewa Lami ba nima bazan ta'ba yafe miki abinda kikai min ba a rayuwa zaki ga karshen ki shiyasa nake miki kashedi tun wuri ki tuba ki canza kafin lokaci ya'kure miki".

Yana juyawa Ramatu taja tsaki tana cewa "wa'azi da zaka gane da ka dena dan wallahi babu abinda zaka fad'a min yai tasiri a raina ko yasa na sauko daga halina har abada muje zuwa koni ko kai".

Baffah babu yadda ya iya haka yayi ta lallahin Lami da fad'a mata magana me dad'i har yayi sa'a ta daina kukan ta saki ranta suka fara d'an zance yana matukar jin kaunar yarinyar da tausayin ta a ransa yana ganin bai kyauta mata ba daya auri Ramatu ta kasance uwa gare ta duk saiya tattara laifin ya dorawa kansa.

Satin d'aya da dawowar Lami aka daura auren Tanko tayi kuka ta kara harta gode Allah domin a dandali a gaban mutane yaci mata mutunci yace tabi son zuciya da kwadayi ta za'bi zaman wudil a kansa yanzu ya cireta a shafinsa lokacin da Ramatu taji harda dariya haka ta tusa Baffah a gaba da baka'ken maganganu wai ga abinda ya jawo nan batai karatun arziki ba ga wanda take so yayi aure yanzu a saiya ji'ka ta yasha.

Wudil zaune Naja'atu take tare da wani saurayi suna hira da murmushi a fuskarsa yace "wai nikam ba kuyi magana da Lami ba sai yaushe zata dawo nifa ina kewarta sosai duk na shiga damuwa" itama murmushin tayi tana cewa "hum Alpha kenan kaifa ina jin Lami bazata dawo ba domin dam bada amincewar mahaifiyar ta tazo ba inaga ta koma garin su da zama".

"Da gaske kike Najat"?

"Wallahi da gaske nake Alpha zanyi maka wasa da tunani ne".

"To amma wayar dana bata fa idan na kira bata shiga kullum a rufe me yasa"? "Oh ai dama bata tafi da ita ba tana gidan mu sai bayan tafiyar ta ina gyaran d'aki na ganta" dafe kansa yayi yana cewa " to yanzu idan zan ganta ya zanyi garin zaki raka ni ko kuwa? Gaskiya ina son ta da aure ba yaudara ba shin zaki iya taimaka min"?.

Murmushin jin dad'i naja'at tayi tana cewa "me zai hana ni kaina alpha ina son zaman Lami a kusa dani mun riga mun saba bana jin dad'i yanzu da bata nan".

"Ok shikenan karki damu zanyi magana da abbanku duk abinda yake akwai zaki ji" "to nagode sosai alpha" mi'kewa yayi yana mata sallama itama ta mi'ke suka fita tare kowa ya wuce gida.

MRS AL'AMEEN AHMAD CE 😘

Sai mun sake had'uwa a gaba masoya na masu yabo gareni godiya 💖💕💚 sosai sosai godiya.

Think before you do 🤨.

#Vote
#comments
#share
#fallow.

[email protected] MAMAN LITTLE ZARAN AUNTY 💃👌👍.

YUSRAHMS ABUBAKAR.

21~AL-BASIT
The extender
22~AL-KHAFID
The abaser

11~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin sayyidil Sajidinah.
🌹🥀🌹🥀🌹🥀🌹

🌄DISCONTENT🌄
Episode 21 nd 22
Wata daya tsakani Musbahu da baban alpha suka zo nemawa masa auren Lami Baffah yayi farin ciki yayi godiya ga Allah ya kara yayi addu'a da fatan alkairi da sanyawar albarkarsa da samun zuriya ta gari sannan ya ro'ki Baffah akan zai tafi da Lami su Naja'atu sun damu ta koma tunda hutu ya rage saura sati daya a koma Baffah kuwa dad'i yaji a take yace ta dauko kayan ta su tafi itama Lamin taji dad'i sosai da sauri kuwa ta had'a komai bata ta shirya ta bisu suka tafi.

Bayan tafiyar su Ramatu ta dawo batasan me ake ba hakkinta na uwa itama dole ya fad'a mata tasan abinda ke faruwa bazai biye halinta ba zata wuce yace.

"RAMATU" da sauri ta waigo ganin kaya turus a gaban Baffah yasa ta washe baki tana cewa "na'am malam gani nazo ne"? "Eh magana zamuyi" kamar an jefota yaga taxo ta zauna tana le'ken babbar ledar dake gaban sa yace "to malam gani nazo in kaji kira an samu amma banda kiran dan sanda".

Shiru Baffah yai yana kallon ta ganin baice komai ba tace "malam ka kira ni kuma kayi shiru"?.

Sauke ajiyar zuciya yai yana cewa "ina fata yanzu kam zaki fahimce ni duk da nasa ke baud'addiyar mace ce wacce ba'a gane inda al'kibilar ki take amma ya zama dole na fad'a miki yau dazu bayan fitar ki Musbahu yazo tare da wani mutum wanda d'ansa yake son Lami sunzo nema masa aurenta kuma na basu duk da banyi shawara dake ba amma ya kika ce kema mahaifiyar tace kina da hakki a kanta ga dai kayan da suka kawo nan da kud'i".

Zaro ido Ramatu tai gani kud'i daure a kyaure dami guda baki washe tayi tana cewa "ayya malam ai bakai laifi ba meye a ciki basai kai shawara dani ba ai kaida kaya mallakar wuya ne" ta karasa maganar tana dauko 'kwallelan goro daga cikin ledar ta soma garza tana cewa "yaushe zasu sake dawowa ne nifa ban gane cewa mutumin nan yana son Lami ba saiyau kace gara daya dauke ta suka tafi gashi harda abin arziki ta samo saurayi d'an birni" kai Baffah ya jinjina lallai kam wato idan akace mutum nada son zuciya sai a hankali yayi mamakin ganin yadda Ramatu ta amince Shi dai farin cikin sa daya Lami zata bar kauyen nan taje ta zurfafa karatun ta tayi ilimi ta cika burinta.

"Malam me kake tunani"? Ramatu ta fad'a tana sake cewa "malam aban nawa kason zan rabawa dangi" .

Cikin mamaki Baffah yace "kason me"? Kud'in dake gefe ta nuna tana cewa "garin su Mariya zanje in an jima nasan kayan lambu sunyi na saro Lami ta fara min talle" "telle kuma"? Baffah ya fad'a yana kallon ta "eh talle saita tara kud'in da za'a saya mata yan kayan d'aki da kayan katako" "a'a indai dan wannan ne ki barshi ni zanyi mata komai".

Daina cin goron Ramatu tayi bakinta daya sauya kala zuwa ja ta bud'e shi tana cewa "amma dai malam zilama ce tasa kace haka"? Wani kallo Baffah ya mata tare da maimaita kalmar "zilama"? Ba kunya Ramatu tace "eh zilama nace kake dashi malam bada zilan zilan irin taka ba da had'ama taya zakace kaine zakai mata kayan d'aki dan karka bani ko sisi shine kace wani kaine zakai mata to wallahi bazan yarda ba domin nice nayi na'kuda na haifeta na fika iko da ita wato dan ka je ka sayi ru'babbun Kaya shine kace a barmaka ragamar komai a hannun ka".

"Ramatu meyasa ko kadan baki da tunani? Ni kike cewa haka? Bansan ranar da zaki hankali ba shiyasa kullum nake godewa Allah da bai sa Lami tayo halinki ba" mi'kewa Ramatu tai "malam me kake nufi kenan karya nayi"?.

Ransa a had'e yace "ban sani ba ban guri" wucewa Ramatu tayi tana cewa "wallahi kome zai faru bazan yarda malam ehe idan kuma ba haka ba saidai a fasa auren" Baffah bai sake kulata ba ya tattare kayan da kud'in ya shiga d'aki.

Nan labari ya kardad'e gari ko'ina sai gulma ake wai Lami tayi saurayi d'an birni zata koma can tabar rayuwar kauye lokacin da labari ya iske Tanko hankalin sa ya tashi haka nan yaji yaji bayaso ta auri wani nan ya fara shiga da fita ya rasa inda zaisa kansa yaji dad'i dan haka ya yanke shawarar zai samu iyayen sa suje nema masa auren Lami ba haku yai ba.

Abokin Tanko Mudi wanda ba'a ganin tsakanin su shi Tanko ya samu yana fad'awa matsalar sa yace kuma ya bashi shawara Mudi yace masa kawai suje su samu Lami idan suka hure mata kunne tuni zasu rusa ala'kar ta da d'an binnin saiya aureta Tanko ya yarda haka zaiyi idan ya samu ya shawo kanta saiya lalla'ba ya saki Karime tunda d'akin sa daya ne.

Lokacin da Tanko ya samu iyayen sa da wannan maganar sunyi mamaki kuma ransu ya 'baci cikin fad'a Delu tace "a lallai Tanko ka raina mana hankali wa ma naji kana zaka aura Lami ko? To wallahi ko Ramatu ce baka isa ba aidai itace ta haifi Lamin ko? gaskiya Tanko ka cika mara tunani Lamin data za'bi birni ta share ka ta manta dakai shine yanzu saboda baka da zuciya kai kuma kake kokarin rufa mata asiri bayan ta tona maka kai kuma sakarai kawai".
Chapter 25 · 0% Book details