← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 93 OF 145

Sashe 93

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Amma me bayan sati kamar yadda suka cewa malam Habu haka suka zo ya basu gida ya fito da komai nashi waje malam Habu bai fad'awa kowa aje a fad'owa Rakiya ba dan saboda yaga take taken su ba mutanen arziki bane amma a cikin bai tura mata d'inba sai gashi taxo tana cewa dan Allah su daina rushe masa gida su kar'bi gonarta a madadin gidan babu wanda ya kalleta haka sukai plat da gurin ya zama sai tarin tudun 'kasa kamar daga sama saiga Ilyah yazo ya jasu gefe suka dad'e suna magana daga baya ya wuce tacan yana hararar malam Habu su kuma suka dawo gurin suna cewa shikenan wancan mutumin da ya tafi yanzu ya ninka musu kud'in filin da gonar da suka kar'ba yanzu ya saye ya zama nasa basu da matsala kafin suka kad'a kai suka bar qauyen tunda sunyi abinda ya kawosu Malam Habu suna tsaye cirko cirko cike da tsananin mamakin Ilyah wato dan ya tozarta shi ya bari saida aka rushe gidan yazo ya saya Dan kada ya saya a gurinsa ya roki alfarmar ya barshi yaci gaba da zama da iyalansa hum babu komai rayuwa ce Rakiya hawaye tai cikin takaicin ganin abinda Ilyah yaiwa Malam Habu tana kallon sa tace.

"Dan Allah Habubakar kayi hakuri kar kasa damuwa a ranka insha Allahu wata rana sai labari muje gida ku d'ebo kayanku".

Murmushin dole malam Habu yai yana kukan zuci yasa su Asma'u suka fara d'iban kayan aka suna kaiwa gidan inda Rakiya take har suka gama d'auke komai gari kuwa yayi shiru kamar wanda akai mutuwa wasu jiki yayi sanyi saboda tausayin malam Habu wasu suna dariya harda qyaqyace irinsu Tanko da Bara'atu😣.

MARSHALL ISLANDS🌃
Asad yana zaune yana aiki Clarah tazo tana zama kujerar dake facing dinsa da yake ba'a gidansa bane yazo barrack ne kallon sa cike da burgewa kullum gayen nan gani take yana kara yi masa wani irin kyau kwarjininsa yana bayyana huuuuuhsh ta sauke ajiyar zuciya jin yace.

"Meke tafe dake"?.

Sake kallon sa tai da murmushi akan fuskarta tace "Asad dama Ina so zan maka tambaya ne akan tsakani na dakai idan baza ka damu ba please"?.

"Ina jinki".

Ya bata amsa batare daya d'ago ko yabar abinda yake ba d'an yatsina fuska tai murya a shagwa'be kamar zata fashe da kuka tace.

"Please Asad a haka bazaka fahimce niba saika daina aikin nan ka bani hankalinka duka".

Kai ya jinjina yana d'agowa ya kalleta a fisge kafin yace "shikenan zamuyi maganar amma baki bukaceta yanxu ba baki damu ki fad'a min ba indai saina aje aikina ne zaki dad'e bamuyi magana mai muhimmanci ba".

Jin abinda yace yasa da sauri ta daidai kanta tana cewa "amma meyasa kace haka Asad kamar ya idan saika daina aiki zamuyi magana zan dad'e ba muyi ba"?.

Kai tsaye yace "idan kina son samun lokaci na ki bari sai nayi ritaya sannan nake free kin gane zaki iya tafiya".

Da mamaki Clarah ta kalleshi tana zaro ido tace "ritaya kuma Asad? Ritaya dai wacce na sani ta aje aiki mutum yai samu hutu"?.

"Eh ita".

Ya fad'a yana danna link d'in ranar ko Allah zaisa yau yaga wani abu Clarah data shagala wajen kallonsa tana ta le'ka laptop d'in tana danna waya idan taga kamar zai d'ago ya kamata saitai sauri ta rufe wayar daya koma kan aiki zata sake bud'ewa taci gaba.

"Clarah kibar nan wajen nan yanzu kafin ranki ya 'baci idan kinsan baki da abinda zaki fad'a min get of my sight".

Jiki a sanyaye ta mi'ke xata bar gurin sai kuma ta dakata tana juyowa tace "shikenan muyi maganar yanzu ka amince"?.

"Ok".
Kawai shine abinda yace mata numfashi mai d'umi ta fitar saboda tunanin a yadda zaidau maganar kafin tace.

"Wai Asad ya batun auren mune har yanzu shiru nifa na damu naga na zama matar ka ina fatan ganin wannan ranar".

Baiyi niyyar kallonta ba amma maganar data fad'a yasa ya d'ago yana dubanta sau d'aya tare da jinjina kai kafin ya mayar da hankalin sa kan aikin da yake yana cewa.

"Zaki iya jirana sai nayi ritaya idan ma zanyin kenan"?.

Zaro ido Clarah tai cike da firgici tace "wai da gaske kake saikayi ritaya Asad"? Tayi maganar tana kallon yanayin sa jin yayi banza da ita taci gaba.

"Gaskiya nikam Asad bazan iya jira sai kayi ritaya ba ina so muyi aure a kwana kusa bayan duk shekarun da muka d'iba a baya sannan gaba ma haka a'a Asad please wannan huluncin daka yanke yamin tsauri da yawa Asad ina son ka sosai zuciyata gaf take da bugawa idan ban bud'e ido na ganni matsayin matarka ba dan Allah ka janye wannan maganar kar kasa hawan jini ya kamani".

Kai Asad ya girgiza "no Clarah I can't bazan yi abinda zai takura niba kin gane? kawai idan zaki jira ki jirani idan bazaki jira ba babu wani damuwa zaki iya yin aurenki ina miki fatan alkhairi jeki".

Da sauri itama ta girgiza masa kai hankali tashe tace "a'a Asad kada muyi haka dakai shikenan naji na amince zan jiraka koda nanda shekara hamsin ne zan iya kayi hakuri".

"Ok zaki iya tafiya".

Sauke ajiyar zuciya Clarah tai tana sake kallon shi kafin ta juya tana fita zuciyarta duk ba dad'i ga abinda Asad yace mata ita kuma data samu pass taje gida harta fad'awa mahaifa kwanan nan xata kawo musu mijin da zata aura yanxu ya zatai kenan ta tabbata ko mutuwa zatai Asad tunda yace haka a yanxu bazaije gidansu ba dole tayi kiran Dad da Mom ta basu ha'kuri tayi musu qaryar wani uzirin daya hanashi zuwa yadda bazasu fahimci komai ba balle akwai wani cousin d'inta dake sonta sunansa Ifeany yayi bi yayi naci tace masa akwai wanda take so dan haka dole ta jira Asad kodan kar yayi mata dariya ganin ta 'kishi kuma wanda take so ya'ki aurenta.

MRS AL'AMEEN AHMAD CE😘
Sai Allah ya kaimu gobe da nisan kwana.

Yusrah Musa Abubakar YUSEEN AL-AMEEN🏖️ sister Najaat Saleem Fateey Aishat Abubakar.

THANKS FOR UR SUPPORT
🌹🥀🌹🥀🌹🥀🌹🥀🌹🥀🌹

TYPING 📲 Thur, 29/24 10:11AM YUSRAH MUSA ABUBAKAR💋.

👑MË KÄMÄR SÄRKÏ👑

STORY WRITTEN ND EDITING
🗣️✍️✊Mrs Al'ameen Ahmad ce.

DEDICATED TO
MR HÂUSÅ ËBÔÔKS📚📙📘📕
SHURAIHU USMAN CEO FAUNDER OF TASKAR NOVELS.

💫ÀÑÑÙRÌ WRITER'S ASS💫
🏘Home ️of 🤟hospitality and 🌹harmony.
ÀÑÑÙRÌ haske daga Allah 🎇🎆✨.

🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈🎈
SALEEM MUSA ABUBAKAR🤝 I know everything about you is so so good but one thing is wrong that u're not mind🎉.

WHATSAPP NO:234 8160983083.
YUSRAH MUSA ABUBAKAR.

61~AL-MUMITU
The Destroyer
62~AL-HAYYU
The Living

30~Allahumma salli wa sallim ala sayyidina muhammadin Madaniyyil Arabiyyil Mukarrami yaumi 'kiyamati.

🌄MIGRATION ND OPTIMISM🌄
Episode 61&62
QAUYE🏕️
________Ganin zama fa bai kama malam Habu ba shi kad'ai yayi tunanin cewa kawai gara yabar qauyen nan gabaki d'aya da iyalansa ya koma wani gurin da zama ya kafa ingantacciyar Sana'a ya faranta musu kuma ya sau'ke nauyinsu dake kanshi dan haka bayan ya gama yanke shawara da dare ya dawo daga masallaci ya tarasu gabadaya yana kallonsu cikin nazari da tunanin abinda zaiyi shine daidai kuma shine mafita a rayuwarsa da iyalansa nasa kafin ya soma magana kamar haka.

"Assalamu alaikum ina so dukkanku ku bani aron hankalinku nan zanyi wata magana duk da bansan a yadda zaku fahimce niba amma ya zama dole na fad'a muku na yanke shawarar barin garin nan gabadaya tare daku idan Allah ya kaimu jibi gobe na baku dama kowa taje tayi sallama da 'yan uwanta sannan wacce taga bazata iya bina ba tayi min magana na sauwa'ke mata".

Gyara zama A'i tai tana cewa "malam ina da tambaya"?.

"To ina jinki".

Cigaba A'i tai "yanzu idan ka d'ebe mu muka bar garin nan gayyarmu guda harmu takwas ina zamuje gurin wa zamuje sana'ar me zamuyi acan ko garin da kukaje kaida Sadi kake fad'a"?.

Kai Malam Habu ya girgiza yana cewa "a'a banan ba inda Allah ya kaini zanje kawai zan fita ne lalume a cikin duhu tunda bansan inda zan samu sa'a ba damuwa ta na samu na faranta muku".

"Nide malam badan karkace na fiya shishshigi ba da nace kayi hakuri da tafiyar nan gashi kuma wai harda mu tunda Allah yasa Rakiya mutuniyar arziki ce bazata gaji damu ba amma yanzu kawai mubar gari muje bamu samo komai ba azo anai mana dariya" A'i tai maganar tana kallon malam Habu da jiran jin amsar dazai bata.

Sauke ajiyar zuciya yai yana cewa "A'i koda za'ai min dariya idan naje na dawo ban samo komai d'inba zan tafi tabbas bazanci gaba da zama a wannan garin ba domin yanzu ya fita min arai koda zan dawo cikin sa za'a d'ebi lokaci mai tsawo kuma insha Allahu hakan da zanyi shine daidai".

"Nidai malam a gani na ka sake nazari wannan ba shawara bace".

"Ai shiyasa nace wacce taga bazata iya bina ba tayi min magana na sauwa'ke mata na bada za'bi kuma kuyi nazari zuwa Nan da jibin ina jiran ku shikenan na gama magana".

Shiru A'i tai bata sake koda tari ba Binta da Saude dama suna gefe sukam basuyi magana ba abinda yace shine zasubi fatan su Allah yasa hakan ne mafi alkhairi.

Washe gari duk bazuwa sukai kowa ya tafi bankwana da dangi haka suka wuni suna yawan sallama da 'yan uwa kowacce sai dare ta dawo suka tarar da Rakiya tasa malam Habu a gaba tana rokonsa kada yaje ko'ina indai gida ne ba matsala suci gaba da zama idan gonace zata bashi aron tata guda d'aya ya ri'ka nomawa amma dan Allah kada yace zaibar gari shi kuma ya nuna Mata yana godiya da karamcin ta gareshi amma tayi ha'kuri ta fahimce bawai ya'ki bane a'a kawai shi zama a garin ne ya fita a ransa shiyasa yake so koda shekara ce yaje yayi rani a wani gun ya dawo daga baya babu yadda Rakiya ta iya haka ta ha'kura badan ranta yaso ba.
Chapter 93 · 0% Book details