← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 145

Sashe 62

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya Mami da Sultana Fatima sukai dan kuwa Mami ta tabbata Asad bazai kar'bi sarauta ba domin ya ta'ba fad'a mata a shekarun baya tun lokacin daya had'u da Amatu malam Habu zai kaita makaranta ya shiga part d'in ta take tsokanarsa tana cewa "Asad tunda kaine ka fara ganin matar aurenka ai kaine zaka gaji Abbanku ko" kaiya girgiza mata da sauri yace "a'a ba son mulki Mami bazan iya ba babu ni a cikin saidai ko Ajeeb ko Annur da Ameer amma nidai na yafe aikina nasa a gaba" dawowa daga tunani tai tana kallon mai martaba da suke zance da Sultana Fatima sai kawai tai murmushi zaman su yana matukar burgeta Sultana Fatima bata da wata matsala tunda suke tare bata ta'ba yi mata wani abu dataji haushin ta ko ta munana mata ba shiyasa take sonta da Sultana Hadizah ce tasan da yanzu sai daya ko ita ko kuma ita domin bazata d'au raini ba "Hauwa'u tunanin me kike"? Ta sake jin mai martaba ya mata tambaya kai ta girgiza har lokacin da murmushi a fuskarta tace "babu komai u're highness" daga haka bata sake cewa komai ba ta bud'e wayarta tana shiga chat saboda tasan maybe Asad ya mata magana.

🏕️'KAUYE🏕️
Asabe ce zaune sai kiran wayyo Allah wayyo na shiga uku take bayan mai gara tazo ta duba mata targad'en kafarta wanda Dalah tai mata shegen duka Balarabe yana zaune a gefenta da mafici a hannunsa kamar zaiyi kuka sai cewa yake.

"Sannu Asabe sannu kinji Allah ya sauwake Allah ya baki lafiya sannu bi a hankali wai taya ma kikaji targad'en ne ko fad'uwa kikai naga fuskarki ta kumbura kuma gefen bakin ki a fashe"?.

Wata uwar harara Asabe ta sakar masa jin abinda yake cewa wato fad'uwa tai amma zatai irin wannan raunikan a 'kule tace.

"Wanne irin munafirci ne zakace maye ya kumbura min fuska wato ka nuna bakasan komai ba saboda matarka ce tai min duka ko"🤣?.

Zaro ido Balarabe yai cike da mamaki yace "wacce matar tawa amma dai ba Dalah ba itace tai miki haka kuma kika zauna garin yaya"?

"Garin ban sani ba aikin banza aikin wofi kawai na rantse da Allah bazan yarda ba ko kadau mataki kona huce haushi na a kanka dan ba'a ta'ba Asabe a 'kare lafiya ni zafin wuta ce nafi maciji dafi"

Kallon ta Balarabe yai "to yanzu me kike so ayi"?.

"Oh tambaya ma kake kwarai Balarabe ni yaushe nema nayi sake harka samu baki da damar fad'i in fad'a dani ina cewa kayi zaka kana maida min? Eh lallai Dalah ta sake sabon shiri amma ba damuwa bari nima na warke zanci uban ubanta ne ni roba ina daidai da 'kugun kowanne shege".

Saroro Balarabe yai yana kallon ta ya kasa cewa komai cikin tsawa Asabe tace "kallona kake nace kallona ka tsaya yi Balarabe bazaka dau matakin ba kenan"?.

A susuce Balarabe daya zabura murya na rawar tsoro yace "dan Allah kiyi hakuri fad'a min me kike so bansan me zanyi ba umarninki nake bi"?.

Asabe bata kulashi ba saida ta d'ono ruwan zafi a tsumma ta danna a gefen fuskarta tana yamutsewa da'kyar saboda azaba tace "so nake ka saki Dalah yanzu ta tattara yanata-yanata tabar gidan nan".

Kallon ta Balarabe yai "idan na miki haka shikenan kin huce"?.

A fusace Asabe tace "ban sani ba d'an sakalai😬😧 maza kaci gaba da tambaya ta Allah yasa karkayi abinda nace wallahi yau zaka sha mamaki".

Jin abinda take fad'a yasa Balarabe jiki na'bari ya mi'ke yana zunduma kira "DALAH KE DALAH gidan uban wa kika shiga zonan yanzu munafika mara mutunci zaki fito ko saina zo na fito dake a tsiyace"?.

Jin abinda yake fad'a yasa Dalah tashi daga kwancen da take ta fito waje domin ita dama wannan gurin take so azo inda zata bar masa gida yaje ya 'karata zai gane idan tana da amfani a gurin sa durkusawa tai a gaban sa cikin ladabi tace "gani".

A masife Balarabe yace "au gaki? gaki? Shine abinda zaki ce saboda ke ba mutuniyar arziki bace? To yanzu ki tashi ki had'a tsummokan kayanki ki barmin gidana na sakeki Dalah tunda kin zama muguwar mace mai ba'kin hali idan naci gaba da zama dake wata rana nan gaba bansan bala'in da zaki kwaso min ba".

Mikewa Dalah tai tana cewa "alhamdulillah dama nima kullum wannan ranar nake jira kuma ina so kasani nangaba sai kayi nadamar abubuwan da kake aikatawa a yanzu sannan bazan tafi ba saika bani shedar sakina a hannu na".

"Au saurin me kike yanzu ma kuwa zaki kar'ba d'aki ya shige yana masifa Dalah data kalli yadda Asabe take d'und'uma jiki tun d'azu tayi dariya tana cewa "ashe duk cika bakinki na 'karya ne gashi zarrata tai miki aiki? Ai banyi tunanin idan kika sha duka tsoro zaisa kice a sake niba na dauka zakii warke mu d'ora akan inda muka tsaya ne"?.

Wata uwar harara Asabe ta sakar mata tana cewa"ke dallacan gafara ban guri uban waye ya fad'a miki tsoro yasa na nace ya sake ki nayi haka dan na ba'kanta miki ne".

Murmushi Dalah tai "au haba wai dan gaske kike? Ta fad'a tana kallon Asabe ganin tayi shiru yasa tai dariya tana cewa "humm Asabe kenan nifa hasken rana ce baki isa ki kare niba kuma abinda nake bukata ne kullum yau na samu kina tsoro ne kawai domin kin ganki yanzu a zaune kada malam ya fita na take 'kafar ciwon na dawo miki da sabuwar karaya shiyasa kike so nabar gidan kwantar da hankalin ki badai gida bane gashi nan na bar miki saiki dafa ki cinye maiya kawai".

Daidai Balarabe ya fito a d'aki yace "uban waye maiyar kinga Dalah ki kiyaye ni uwar me kika tsaya jira kizo kibar min gida nace" ya karasa maganar yana cillo mata farar takarda wacce yai rubutu da ajami d'auka Dalah tai tana shiga d'aki ta sako hijab ta fito zata fice dakatar da ita Balarabe yai "ina zakije baki d'ebe kayayyakin kiba"? Juyowa Dalah tai tana kallon sa tace "saurin me kake jira ka gani yanzu ma kuwa zan d'ebe an gaya maka ina sha'awar sake zama a gidanka ne"? Mstttthhh taja tsaki tana 'kwalla kiran "Indo ke Indo fito mu tafi" zunbur Balarabe ya mi'ke yana cewa "tazo ku tafi ina? Inace 'yata ce bada ita kikazo min gida ba to wallahi babu inda zata biki kinji na rantse ko fita min a gida" Dalah bata sake ce masa komai ba ta fice yayin da Balarabe ya juya kan Indo data fito daga d'aki da hijab a hannunta tana shirin sakawa jin kiran da Dalah tai mata wani kallo Balarabe ya bita dashi tare da d'aukar sanda dake gefen Asabe yana cewa.

"Oh munafika wato da yake kinji kiran uwarki shine harda fitowa da sauri ko da Asabe ce sai tana kumfan baki kice baki jita ba saboda ke matsiyaciya ce kin gado ba'kin hali irin na dangin Dalah uban ki zakici ai yanzu bata gidan".

Ran Indo a 'bace ta tsaya tana kallon Balarabe sai kace ba ubanta ba zai ri'ka yi mata irin wannan tsinuwar ganin shi ta tsaya kallo yasa ya wurga mata sandan hannunsa yana cewa.

"Dan ubanki me kike kallo maiya ko cinye ni zaki d'anye🤔"? Da gudu Indo ta fad'a d'aki sandan daya wurgo mata saura kad'an ya sameta a baya tana shigewa ya daki kofa d'akin ji kake kararau ya fad'o kasa huci Balarabe keyi yana nuna kofar d'akin da hannu.

"Zakici uban kine shegiya la'ananniya mai ba'kin jini babu wanda ya ta'ba zuwa yace yana sonki duk garin nan nidai wallahi ba jinina kika biyo ba saidai dangin Dalah dangin tsiya aikin banza nayi danasanin aurenta har abun ya min ciwo ya zama tabo tsinannu kai duk kunbi kun burkita min 'kwa'kwalwata da halinku bari nabi bayan shegiyar uwar taki tazo ta d'ebe daud'ar ta da bolarta a gidana" ya fad'a yana yin hanyar fita sai sambatu yake yayin da yabar Asabe yau ba bakin magana sai d'und'uma jiki take tana ya'kewa saboda azaba.

🏙️KANO🏙️
Nurain na zaune a parlor bayan ya gama waya da Nafisa sai kallon secreen din yake yana murmushi fitowar Zainab kenan daga part d'inta cikin shiri zata tafi office tana ri'ke da hannun Auta dake sanye da uniform Amnah tana binsu a baya ganinsa a zaune yasa cikin mamakin meya tsaya yi har yanzu bai tafi gurin aiki ba ta karaso zatai magana abinda yake kallo a cikin wayar ta kalla wani irin 'kara ta saki tana jifa da handbag👜 d'in dake hannunta muryarta na rawa tace "My choice me zan gani haka photon wata budurwar ka zubawa ido kana gani wacece ita a ina take meye ala'kar ku"? Ta fad'a hawaye na zubo mata tana kallonsa zuciyarta na girgiza da tsoron karfa ace budurwar sace data shiga uku yadda bata son kishiya.

Shiru Nurain yai bai bata amsa ba a rud'e ta zauna a gefensa zata kar'bi wayar ya zame hannunsa kuka ta saki da karfi tana cewa "dan Allah ka fad'a min gaskiyar wacece ita a gurin ka kafin kasa zuciyata ta buga wallhi bazan iya jurewa ba ina da matukar rauni ta wannan bangaren bazan iya jurar kishi ba my choice ka fad'a min ka hutar dani 'kunci" ta fad'a tana kifa kanta a kafad'ar sa fitowar mai aikinsu Falmata ganin abinda yake faruwa yasa da sauri taso juyawa Nurain ya dakatar da ita.

"Fatima zoki raka su Amnah school kada lokaci ya'kure".

Jiki a sanyaye Falmata ta juyo kanta a sunkuye tace "to mai gida muje Amnah" wucewa sukai Amnah tana sake waigowa ta kalli yadda Zainab d'in take kuka suna fita Nurain ya sake jawota jikinsa yana rungumeta sosai cikin lallahi yace.

"Kiyi shiru mana haba baby zaki tada min da hankali na".

'Ko'karin fisgewa Zainab take tana ture shi da dukkan 'karfin ta tace "ka sakeni bana so ba wani baby ka rabu dani".

"zan rabu dake but fad'a min abinda ya 'bata miki rai"?.

"Ai kana jin tambayar danai maka ka shareni kasan irin kishin da nake maka amma wanne irin sake nayi har na bari kake kallon photon wata jakar".

Zaro ido Nurain yai "jaka dai?.
Chapter 62 · 0% Book details