← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 33 OF 145

Sashe 33

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Amma gaskiya Baffah baisan halacci ba duk irin son da Adamu ya nunawa Lami bai gani ba shine yasa 'ya'yansa su dake shi bayan hakan ma bai ishe Shiba harda d'ebo masa 'yan sanda" Delu ta fad'a tana yin hanyar kofar lungun matar Tanko dan ta sanar mata haka Balah ya zauna shi kadai sai masifa yake duk wanda zai wuce yana jinsa.

Bayan sun koma gida Baffah da fad'a ya kama Habu "haba Habubakar meyasa kayi haka tsakani da kunya ka d'ebo masa 'yan sanda da ka kyale kawai ni zan iya hakura Allah ya saka mata".

Kafin Habu yai magana Sabi'u yace "wallahi Baffah habu yayi daidai gara daya d'ebo musu dan koda ace abinda muke dashi zai 'kare matukar za'a hukunta shi to zanyi komai".

Gyara zama Habu yai yana cewa "to ai Baffah idan ba hakan akayi musu ba zasu sake marmarin yiwa wata yarinyar anan gaba ba sun san tsakani da kunyar su suka aikata mata rashin d'a'a bayan haka taya munsan shine zamu kyale shi aida bamu yafewa kaimu ba abinda muke bukata Baffah ka taya mu da addu'a Allah ya bamu sa'a idan mun shiga kotu".

Babu yadda Baffah ya iya haka ya bisu da addu'a kamar yadda suka ce yana musu fatan alkairi duk inda ka shiga a garin kuwa gulmar ake cewa ashe Tanko ne yaiwa Lami fayd'e shiyasa Habu ya d'ebo masa'yan sanda sai tsine masa ake saboda kowa yasan zai aikata halinsa ne.

Abun da ya baiwa su Habu mamaki a kotu 'kememe Tanko ya'ki kar'ban laifin da ake zargin sa yace baisan zancen ba sharri sukai masa iya 'kulewa ya 'kular da Habu ji yake badan a gaban alkali suke ba babu abinda zai hana sha'ke wuyan Tanko harsai yaga ya daina motsi ya mutu daya rabu dashi".

Anyi gwagwarmaya ansha matukar wahala saida akai da gaske sannan Tanko ya amshi laifin sa azaba tasa yai bayani aka sake tambayarsa da jiddadawa shine ya mata fayd'e shine ya mata fayd'e ya zamo silar mutuwarta ya kuwa amsa eh shine da taimakon abokinsa Mudi dan haka aka yanke masa hukuncin zaman gidan yari shekara ashirin da biyar Mudi shekara biyar tab a take Balah ya yanke jiki ya fad'i a sume saboda d'imuwa da tashin hankalin abinda yaji Tankon ya fad'a mugayen halaye marasa kyau wanda bai sani ba a gurin ya suma hawan jinin sa ya tashi sai asibiti aka kaishi haka su Habu suka dawo gida ransu fari tas ko yanzu sun cika burin su tunda an yanke masa hukunci mafi tsauri.

Satin Balah uku a asibiti ya rasu Tanko bai sani ba domin yana can kuma gurin da yake mafi tsananin horo ba'a zuwa koda a shekara sau d'aya ne balle yasa rai zaiga 'yan gida haka kullum yake fama da aikin wahala da horo me tsanani.

Lokacin da suka koma gida a kofar d'akin Ramatu sukaga Ilyah zaune ya karkace sai yanka loma yake kamar wanda yai shekara baici ba zama sukai Baffah na cewa "kai Ilyasu idan ka gama ina son magana dakai" bai d'ago balle yasan mutum ke masa magana duk da yasan irin kokarin da su Habu sukai akan case din Lami amma yai banza daya gama ma yana wanke hannu yai hanyar kofar gida da nufin ficewa tab kamar wanda ya watsawa Habu ruwan wuta haka ya mi'ke zunbur yana shan gaban ransa a had'e yace.

"Wai meye haka kakeyi Baffah nefa ke maka magana".

Kallon kallo suka fara kafin Ilyah ya kuma gegewa zai wuce fisgoshi Habu yai yana hankad'a shi sai gashi guruf ya kifa a gaban Baffah a fusace Ilyah ya juyo yana kallon Habu dake tsaye bayansa yace.

"Ni ka hankad'a haka? Habu aiko wallahi sai kayi Dana sani".

Wata uwar harara me zafi Habu yasakar masa yana cewa "wannan shine fad'arka sau ba adadi na saba jin haka a bakinka amma banga ranar da zata zo nayi nadama ba a rayuwa ta domin sani zan gama da duniya lafiya bani da bakin iyaye a jikina".

Cikin 'kunan rai Ilyah yace "kuma waye me bakin iyayen".

"Ina wani bayan kai, ko nayi karya"?.

Kafin Ilyah yai magana Baffah ya katse su "ku dakata magana nace zamuyi ba fad'a ba wannan shashancin bai kamata ba zauna habu" zama yai suna aikawa juna harara Baffah ya soma magana.

"Iliyasu nasan kasani cewa ga abinda yan uwanka suke na fafutikar gano wanda yai silar Lami har Allah ya basu sa'a asirin su ya tonu amma baka ta'ba zuwa ka tambaye mu me muke ciki ba gashi kaji an yanke musu hukunci duk da haka bakai hankalin da zaka tare ni da wata magana ba meyasa"?.

Tashi Ilyah yai yana karkad'e jikinsa yace "to Baffah ina ruwana me kuwa zance muku dama ni na sasu wannan matsalar suce gani sukai zasu iya Lami dai ta riga ta mutu ba dawowa zatai ba gashi kunzo kunata bata zaman ku da 'yan gari nikam babu abinda yai min zafi kada ku sake sani cikin safgarku".

Yana kaiwa nan yai waje shiru Baffah yai Sabi'u daya dafe kai yace "kayi hakuri Baffah dan Allah ka daina sa damuwar Ilyah a zuciyarka kada wata rana ya d'ora maka hawan jini".

"Umh to mezance Sabi'u Ilyasu ya fita daban a cikin 'ya'yana saidai Allah ya shirye shi" Amin Sabi'u yace Habu kam ba'kin ciki da takaici sun hana shi magana kawai mi'kewa yai ya shige d'aki ya kwanta barsu a waje suna ci gaba da tattaunawa.

Tun Baffah yana 'boye musu jinyar dake damunshi har tazo ta bayyana hankalinsu yayi matukar tashi cikin gangarawa suka daukeshi zuwa asibiti kamar bazai rai suna isa aka tura su emergency saboda ganin halin da yake ciki.

Haka suka wuni likitoci na kansa abun har tsoro ya basu sai bayan sallar magriba babban likita ya kira su zuwa office din sa bayan sun zauna ya fara yi musu bayani.

"Nayi mamaki lokacin da nake duba mahaifin ku yana da zaratan samari kamar taya kuka bari har jinya taci 'karfinsa baku kawo shi asibiti ba yanzu dai mun samu an ceto rayuwar sa insha Allahu zai samu lafiya amma dan Allah nan gaba ko ya kuka ga wata 'yar matsala ku taho asibiti".

Sauke ajiyar zuciya sukai cikin jin dad'i sukaiwa likita godiya anan suka kwana iya Salamatu ce ta biyosu ta kawo musu abinci amma banda Ramatu da Ilyah sai dare sosai ta tafi washe gari ma da wuri tayo abun karyawa tazo kasa hakuri Habu yace.

"Waini dan Allah su Ilyah basu san Baffah baida lafiya ko wulakancin nasu ne dan su nuna basu maida shi komai ba".

Cikin yanayin damuwa Salamatu tace "sun sani bansan me yasa basu zoba".

"Ai gaskiya mutanen nan lamarin su da gyara saidai Allah ya ganar dasu".

Mi'kewa Habu yai yana cewa "bari naje gidan" da sauri yasa takalmansa yana ficewa daga asibitin ya tari mashin har kofar gida cewa yai jiransa yanzu zai fito su koma.

Yana shiga yaga Ilyah gaban murhu yana babbakar kan rago wato dai shi wannan rai da rai yana cikin cin nama kamar jikan sarkin mayu karasawa yai yana cewa.

"Ilyah ka kyauta kenan"?.

Da sauri Ilyah ya juyo ganin Habu tsaye yasa batare dayai magana ba ya maida hankalin sa kan aikinsa dan yasan kwanan zance bazai wuce akan jinyar Baffah bane indai haka ne kuwa ko a jikinsa.

Ganin yai banza dashi yaci gaba "dakai fa nake Ilyah yanzu tsakani da Allah kayi daidai kenan Baffah mahaifin kane amma baida lafiya kana gani muka tafi bakace zaka bimu ba gashi da gari ya waye kaga bamu dawo ba mezai hana ka kaje kaga halin da yake ciki ko baza ka zauna ba sai kayi burus".

Idan dutsi ko bishiya na magana to Ilyah ma yayi kamar ba mutum haka ya dauke kai yaci gaba da aikinsa mamaki ne ya kama Habu kawai ya sake baki ya tsaya kallon iya gudun ruwan ilyah, harya gama ya 'bare kan babu wanda ya sake magana saida ya mi'ke zaije ya wanke yace.

"Kai fa Habubakar babu inda zanje garama kabar 'batawa kanka lokaci kaje ka tafi dan babu inda zanje kuma banga wanda ya isa yasa nayi abinda banyi niyya ba dama Baffan wani abu yake ban dazan damu da jinyarsa yaje can ya 'karata🙆😱😨".

Wucewa yai yana zuba ruwa ya fara wankewa a fusace Habu yaje yai bol da kwanan da Ilyah yake wanke kan ganin hakan ma bai huce ba dauka yai yana tumurmusa shi a kasa karshe ya jefa shi a cikin kwata kafin ya juyo yana cewa.

"badai akan wannan tsinannan kan bane gashi na jefa a kwata sai naga ta tsiya".

Da gudu Ilyah yazo ya kama Habu da kokawa nan fad'a ya kaure jin hayaniya yasa Ramatu fitowa tana cewa.

"Meye hakan Ilyasu ina kan ragon yake"?.

Ran Ilyah daya gama 'baci bai kalli Ramatu ba yace "gashi can wannan mitsiyacin ya jefa a kwata".

Zaro ido Ramatu tai tana kallon gurin tace "kwata? Aikam ganin yadda yai dumu dumu yasa Ramatu fasa 'karar takaici tana cewa "wayyo Allah na amma wallahi Habubakar anyi mugun mutum wato saboda ba'kin ciki shine ka jefa mana nama a cikin kwata aiko saika biya".

Kallonta Habu yai batare daya amsa mata wancan fad'an da take ba yace "yanzu tsakani da Allah babah Ramatu kin kyauta kenan kunsan Baffah baida lafiya keda Ilyah tun jiya mu tafi asibiti amma babu wanda ya bimu a cikin ku".

Jin abinda yace yasa Ramatu cewa "gwafar ubancan lallai ma Habu me kake nufi kenan yanzu zuwa kai kasa muje dole ko me kake nufi? Fad'a min naji wallahi Habu ka ishe ni ka fita ido na in rufe".

Tsaki Ilyah yaja yana cewa "to dan Baffah baida lafiya meye a ciki zai warke kazo ka wani damu mutune dole ne sai munje asibitin bayan ku kuna can wa za'a bari jiran gidan"?.

Wani kallon baka da hankali Habu yai masa wato sudai wadannan baza su ta'ba yin hankali ba a rayuwar su ace uban daya haifeka kake nuna halin ko in kula akansa lallai kam wannan ta'bewa tai yawa yana musu fatan su gane da wuri kafin lokaci ya'kure musu..........
Chapter 33 · 0% Book details