← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 109 OF 145

Sashe 109

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Zaro ido Mom tai tana cewa "subahanallahi kina qauye acan aka haifeki kika girma baki ta'ba zuwa ko'ina ba amma kice wai tuwon ne baki iya ba?.

Shiru Nafisa tai tana 'kar-'kar da ido ta kasa magana Mom taci gaba "ai shikenan ba matsala idan kin ta'ba ganin yadda maman ki tayi ki tsaya zanyi sai kina nuna min yadda zansa komai yayi daidai yadda nakeson yayi tauri kin gane".

Kaita d'aga cike da kunya tana sauke ajiyar zuciya a hankali dan kada Mom ta jita tanan taji d'anji dama-dama tana tsaye tserere Mom ce ke komai abun data nuna matan ma kad'an ne saida ta gama ta sauke sannan tace ta koma parlor abinta bari tayi miyar ma kawai dama 'yar aikinta tayi tafiya ne shiyasa don ta fahimci kamar Nafisan bata iya komai ba amma tayi mamaki yaran qauye da suke tashi da 'kwazo da aiki wannan kuma yadai🤔 kodan ai mahaifan a qauyen ma iri dabam dabam ne wasu na koyawa wasu kuma babu ruwansu.

Saida ta gama bayan sallar magriba tace Nafisa taje part Mimih tayi sallah a tsorace ta shiga bedroom d'in duk da tasan bata nan amma gani take kamar zata shigo yanxu ta sameta wuta-wuta tayi sallah afujajan ta antayo waje ta dawo parlor ta zauna shiru shiru Mom bata fito ba har akai kiran sallar isha nanma fiii ta tashi dagudu taje tayo ta fito daidai Mom ta fito itama daga nata part d'in ganin yadda Nafisa take waige-waige yasa tace.

"Lafiya ko wani abune ya tsorata ki"?.

Da sauri Nafisa ta girgiza kai tana cewa "a'a ba komai".

Zama Mom tai akan kujera tana cewa "ok kije kitchen ki sako abinci yau babu mai mun aiki tayi tafiya''.

Nan ma kai Nafisa ta sake girgizawa cike da kunya ta kasa sannan ta gama taci duk tasan idan bataci anan ba ta koma su Mimih bazasu barta taci ba saidai idan Nurain ya dawo gidan‽ Tuna hakan dayai yasa batasan lokacin data mi'ke tayi hanyar kitchen ba ta d'ebo tazo babu kara ta zauna taci son ranta tasha ruwan roba yaudai ta d'ana🍶.

Sai kusan karfe goma na dare Nurain yazo da kansa suka tafi tare taji dad'i sosai da yake dashi ne su Mimih harda dur'kusawa har kasa suna gaida ita a fake suna mata nuni shikuwa dad'i neyake kamashi suna manyansu suke girmama masa mata domin ba wacce bata shekaru ba haka suka wuce abinsu Meelat na rakasu da harara dad'in abunma iya sune Zainab tana part d'inta a parlor tana aiki a laptop indai ba yanzu ta shiga bedroom ba.

Washe gari da yake asabar ce babu aiki haka Nurain ya d'auketa a mota tun safe bayan sunyi breakfast yace yau kuma gari zai nuna mata haka taci wanka tayi 'kwam a gaban mota tana hura hanci shikuwa mai amarsu sai murmusawa yake yana fad'a Mata duk sunan anguwar da suka zo parking yana kallon ta yace.

"Bari nazo".

Kafin tayi magana harya bud'e murfin motar ya fice ganin ya tafi gurin wani mai kayan miya gasunan jawur yagar yau gwanin kyau ya tsaya ya bashi kud'i zai zuba masa tana d'aga cikin motar ta zaro ido waje lokaci guda tace.

"Na shiga uku ni Nafisa wa nake gani acan kamar Amatu? Dama nan suka dawo da zama suma suna birni kenan innalillahi anya kuwa Amatuce ba Mai kamarta bace duk da taga itama wannan da hula a hannunta tana d'inkawa"? Tanan ta kara susucewa shiru tai cikin nazari domin wannan taga ta kara girma da tsayi gashi wannan kamar tafi Amatu fari dakyau domin ta sake tabbatarwa kanta yasa ta d'ago tana sau'ke glass daidai Nurain ya kar'bo kayan miyan a babbar leda gari yai zafi ya juyo taga fuskar malam Habu tar da idonta wani irin bugawa zuciyarta tayi da sauri ta bud'e kofar itama ta fita cikin alamun tambaya Nurain yace.

"Yadai ina zuwa haka naga kamar ba lafiya ba".

Kai Nafisa ta d'aga masa duk ta gigice tace da'kyar tace "eh lafiya ina zuwa bari nazo yanzu zan dawo mu tafi" tana fad'in haka kafin yayi magana ta zurbala tayi gaba bai bita ba kawai ya bud'e mota ya shiga ya zauna yana kallonta cike da mamaki yaga me zatai.

Tana karasawa ganin sune da gaske ba masu kama dasu bane gasu sunyi kyau da ki'ba sun haska da dukkan alamu yanzu suna jin dad'i anan ta'be baki tai tana cewa.

"malam baba Habubakari kwandon sukari🤔😳 dama daga gida da kayo gudun hijirar nan ka dawo? Dariya tai tana kallon Amatu tace "Allah hamsha'kiya meye kike min irin wannan kallon kodai kinyi sha'awata ne kin ganni tare da mijina muna zaga gari a had'add'iyar mota wacce nasan har ki gama rayuwar ki bazaki ta'ba shiga cikin mota mai AC ba".

Kan Malam Habu ta koma wanda ya tsaya cikin mamakin son abun duniya irin na Ilyah wato saida ya aura mata yaron nan kenan katse masa tunani tayi da cewa.

"Baba Habubakar sana'ar kayan miya ka gudo nan kanayi ko domin ka tara kud'i masu yawa kaje kafi babana arziki ko? humm aiko wallahi karya ne nagaba yai gaba na baya gobe saidai ya tara a haka zaka qare rayuwarka cikin talauci a gaban tumatur🍅🌶 hum'um Allah ya sauwa'ke️".

Tana rufe baki Amatu ta d'aga hannu a fusace zata wanka mata mari malam Habu ya dakatar da ita.

"A'a mamana 'kyaleta duniya ce taci karenta ba babbaka dana gaba akanga zurfin ruwa badan yaya Ilyah yana wulakanta ni agabansu yana nuna niba komai bane da suma bazasu wulakanta niba amma ba komai rayuwa ce wata rana sai labari ke kuma Nafisa Allah ya shiryeki abinda zance dake kenan".

Murgud'a baki Nafisa tai tana cewa "Amin inda gaske kake nina wuce aci gaba da cinikin tumatur" ta fad'a tana she'kewa da dariya kafin ta juya tana yau'ki da rangwad'a harda sauya tafiya taku d'aya bayan d'aya taje a yangace ta bud'e mota ta shiga Nurain yaja yayi gaba bai tambaye taba Saida dukai nisa sun kusa gida yace.

''wai dama kin sanshi ne naga kin tsaya kuna magana"?.

Kai Nafisa ta d'aga tana murmushi tace "eh na sanshi wani talakan fa'kiran mabaracin qauye ne da daya zauna a garin mu daga baya yayo gudun hijira ya dawo nan ya 'buge da tallar tumatur a kan tebur waishi ala dole saiyayi kud'i da qarfi" ta fad'a tana dariya.

Da sabon mamaki Nurain yace "ai kuma yayi kuskure zafin nema baya kawo samu, to amma kuma tsaya ai naga wannan budurwar ta kusa dashi dake zaune tana d'inki naga ta mi'ke xata kawo miki mari ta fasa meyasa"?.

"Humm wai dan nace idan domin ya tara kud'i ya baro qauye a haka zai qare shine take shirin marina ya hanata naso ya barta ta d'ora hannunta a jikina yau da taga yadda ake wasan 'kyawwa🐈 da 'bera🐀 wallahi sai tayi kwanan bayan kanta".

Sauke ajiyar zuciya Nurain yayi bai sake cewa komai ba har suka karasa gida da yake ba girkinta d'aya da Zainab ba kowa nata take yasa Nurain ya tsaya a main parlor yace Mimih taje kitchen d'in Zainab ta d'auko abu su raba kayan miyar nan taji haushi ji take kamar ta rufeshi da duka saboda ya aiketa a gaban Nafisa wacce tai kiru-kiru a gabansu cikin tsoron irin kallon da suke aiko mata.

Saida Mimih ta d'auko yasa dole itace ta raba kamar ta fasa masa ihun takaici ta d'auka takai kitchen d'in Zainab tana fitowa ya mi'ke yana cewa.

"Ki kawo mata nata itama kitchen d'in part d'in ta yanxu kiyi mata blending d'in wasu wanda zatai mana amfani dashi yau kada kisa yaji sosai a markad'en domin bata so kodan ta riga ta gaji mun dawo daga xaga gari ki mata jallop rice kisa mata isashshan mai kifi iya ita xaki dafawa banda ni domin baci xanyi ba fruits zansha idan kin gama kimin magana kin gane "? Kai Mimih ta d'aga zuciyarta na turiri ji take inama zata jita free ba Nurain ta kama Nafisa kila yau a gidan nan sai tayi mata qaramin rai wucewa sukai Nafisa da tasan dawar garin jikinta sai rawa yake gashi bakinta yayi nauyi balle tacewa Nurain d'in ya bari zata d'auka harda share d'an sauran hawayen ta na tuna irin ba'kar u'kubar da zasu d'an'dana mata idan ya fita.

Kai Mimah ta d'aga tana cewa "wai me ya Nurain yake nufi kece zakiwa wannan village girl d'in girki taci yau kutumelesi tabd'ijan aiko ya d'ebo Mata ya'ki zataga tijara muje kitchen d'in nata yau zataci uban daya haifeta kafin gobe ya bar gidan muje mu soya mata aya a hannu muje kitchen d'in.

D'aukar basket din kayan miyan Mimih tayi suka shiga part d'in Nafisa basa falo suna bedroom dan haka suka wuce kitchen Meelat dake jinjina kai tace "ku tsaya kuji zamuyi mata girki amma ba wanda zai ciyu ba tunda ya Nurain yana gidan saimu 'bullo da dabara musa hikima cikin al'amarin".

Cikin rashin fahimta Mimih tace "ban gane me kike nufi ba taya zamuyi mata abincin da basai ciyu ba"?.
Chapter 109 · 0% Book details