← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 145

Sashe 27

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari Musbahu na zaune a irin gurin me sayar da shayi yaji ana labarin yaji wani na cewa "kai jama'a ban taba ganin mace fitinanniya irin wannan matar ta jiya ba ta zage sai zagin mutane take" dariya d'ayan yayi yana cewa "humm kai dai bari kawai nifa nafi zaton mahaukaciya ce" me shayi dake tafaman shekawa yana mikawa yace "tab ba wani hauka daya sameta wallahi in kaga irin haka dama hali ne a jikin rai wazai yi fatan ace wannan uwarsa ce Allah ya kiyaye" Wanda yazo yanzu ya zauna ne ya tari zancen da cewa "ai abokai babu abinda zai baka dariya kamar da tace wai tazo gurin wani d'an mafiya ne mai sace yara da sunan zai sa su a makaranta idan kwana biyu yaji anyi shiru saiya sayar maka da d'an ka" dariya suka sa Musbahu dake zaune jin abinda suke cewa yasa ya shiga tunani kodai Ramatu ce ta biyoshi yasan zata iya ba karamin aikin ta bane kar abu yai nisa ma ta jawo masa masifa magana taje gurin hukuma bari yaje ya gano da mamaki fal a ransa ya kasa magana mi'kewa yayi yabar gurin dan yaje ya tabbatar abinda yaji suna fad'a gaskiya ne.

Gida ya koma ya samu mama a waje tana d'an ayyukan safe ganin sa haka yasa tace "lafiya naga kamar akwai wani abu da ke damunka"? Zama Musbahu yayi yana cewa "eh ba lafiya ba yanzu dana baro gurin baban Khairat me shayi naji wani zance wai jiya wata mata tazo tana neman gidan Musbahu d'an mafiya yana sato yaran mutane yazo ya sasu a makaranta bayan kwana biyu idan yaga iyayen yaran sun dauke kansu saiya sayar dasu shine tsoro ya kama ni kar naje ko Ramatu ce kinsan zata iya zuwa".

Zaro ido mama tai cike da mamaki tace "tofa gaskiya ne ma itace tunda kaji tace Musbahu kuma yana sato 'ya'yan mutane ai kasan itace yanzu tana ina" sauke ajiyar zuciya yai yana cewa "tana gidan me anguwa naji suna cewa" "to mezai hana kaje ka gani idan ita dince nifa bana son gayyar fitina sai a bata yarta mu samu salama tunda abun haka ne" kai Musbahu ya girgiza cike da damuwa yace "ina son yarinyar nan ta zauna a guna tayi karatu bana son ta koma wannan 'kauyen" "to ya zamuyi bamu muka haifa mata 'yaba dole mu ha'kura mu taba kayarta inda rabo tunda ga Alpha zai aureta kaga dai zata dawo kusa damu" mi'kewa Musbahu yayi "to shikenan bari naje na gani Allah yasa ba ita bace" "Amin mama tace daidai ya fita su Najat sun fito a d'aki suka ce "wace abban mu ke cewa Allah yasa ba ita bace"? Juyawa mama tai tana kallon su tace "ba kowa kuzo kuyi mana kayan karyawa" karasowa sukai Naja'atu ta dauki wu'ka ta soma firar dankali Lami kuma ta tafi kitchen zata dora tunkuyar shayi" Yusuf dake tsaye kusa da mama yace "to ni kuma me zanyi" kallonsa mama tayi "me zakai kuwa kana namiji aikin mata ne amma zauna ka taya ni d'aurayar kwanuka" kujara yaja ta roba yana zama suka fara.

A kofar gida cikin zaure ya samu me anguwa da tsirarun mutane sunzo gaida shi zama yayi bayan sun gaisa yace "dama naji wata magana ne a bakin mutane shine nake so na tabbatar wai jiya an kawo wata mata gidanka ta kwana"? Kai me anguwa ya d'aga "eh shakka babu zahiri jiya nikam ina barci ma aka tashe ni nayi mamaki dana ganta harda rauni a goshi wai ana ihun barawo aka rad'e ta ba'a sani anyi tunanin barawon ne shine aka kawo ta nan ta kwana kafin yau ayi bincike a kanta dan ni tsoro ma ta bani da fari, baka ji zagi iri iri ba a bakinta da diban albarka sai loya ashar take kamar ba musulma ba".

Shiru Musbahu yayi na d'an lokaci kafin yace "zan iya ganinta"? "Eh ba matsala zaka iya Bismillah muje tana kewayen bangaren gidana domin ban bari ta kwana cikin gidan ba domin yanzu rayuwa ba tabbas mutane ba abinda yarda bane kar naje da dare ta tashe tayi mana wani abu ta gudu shiyasa nasa aka kulle ta amma muje ka ganta" mi'kewa sukai suna zagayawa Musbahu na binsa yana mamaki a ransa saida yaje ya tabbatar kamar a mafarki ya ganta zaune akan tabarma tana karyawa ga bandeji a goshinta kai ya jinjina yana cewa "Ramatu dama nasan haka zata faru zargina ya tabbata" d'agowa Ramatu tai tana kallon sa tace "dama kasan haka zata faru meh? annamimi shiyasa ka dauko min 'yata gashi nan a garin biyoka na dauke ta wani d'an Allah tsinen ya buga min sanda jiya wallahi ka sani bazan ta'ba yafe maka ba Allah ya isa ce zata rabamu" da mamaki mai anguwa dake gefe a tsaye yace "amma dai tana da ta'bin kwakwalwa ko idan ba zararre ba babu wanda zai ri'ka magana kamar haka" tun Musbahu baiyi magana ba Ramatu tace "tsohuwar kace me ta'bin kai ba niba dama wa ya sako dakai harka dauka in banda yawon gulma wanda ya cuce ni nake wa magana ba kai d'an gayyar sod'i ba bai shafe ka ba dan haka kaja bakin ka kayi shiru idan kuma ka matsa zakaga tashin hankali in kuma akan wannan d'an iskan tuwon da kokon da kuka kawo min ne saika fad'a na biyaka donni ba matsiyaciya bace irinka😲" tofa wai ikon Allah sai kallo fad'an daya fi karfin ka akace ka mayar dashi wasa me anguwa mamaki ne ya rufe shi harya kasa magana sai ido da yake binta dashi lallai matar nan ba 'yar arziki bace da yasan abinda zata saka masa dashi kenan wallahi da bazai karbeta jiya ba saidai ta kwana a layi ko tasan inda dare yai mata.

Katse masa tunani Musbahu yayi da cewa "dan Allah me anguwa kayi hakuri ta sanadi nane da duk haka bata faru ba kai da baka santa ba kaine zakaji mamakin abinda datai maka wannan halin nata yana daya daga cikin butulci irin nata.................

Yana rufe baki Ramatu tace "tsohon ka ubanka Saboh shine butulu ba niba" kai me anguwa ya jinjina yana cewa "tabdijan Allah ya sauwake kada Allah ya kara hada ni da irin ki Musbahu ta tashi ku tafi" me anguwa ya fad'a cikin takaici mi'kewa Ramatu tai tana sake kai lomar tuwon tace "basai ka koreni ba wata tsiyar ce a gidan naka badan kana me anguwa anacin na haram ba 'beran masallaci ma bazai fad'a maka babu ba" daukar kofin kokon tayi ta karasa shanyewa kafin ta d'ure wainar a leda tana cewa "ga gidan ka nan na bar ma saika dafa ka cinye dama in banda kaddara me zai kawo ni garin balle nazo gidan ka wannan me ba'kin idon ne ya jawo komai" tari me anguwa bai sake yiba har suka fita suna tafe tana cin waina a layi ga kafarta ba takalmi kuma ko a jikinta gajiya Musbahu yayi ganin sai kallon sa mutane keyi yace "dan Allah kibar cin wainar nan a layi nan fa ba karkara bace ki bari sai munje gida" harararsa tayi "to ubana dama an fad'a maka idan naje gidan naka zama zanyi ba arziki ne ya kawo ni ba" bai bi takan maganar da take fad'a ba yaci gaba "haba Ramatu gaskiya baki kyauta ba tsakani da Allah yanzu Saida kika biyo yarinyar nan da kinyi hakuri ma da anyi musu hutu zan mayar miki ita.....................

Katse shi Ramatu tay "au haba jimin munafiki a gidan uban wa harda zaka mayar min ita to bana so na hutar dakai kuma kasa Allah a ranka ban yafe maka wannan ciwon da aka ji min ta sanadinka ba" ta karasa maganar tana sake kaiwa lomar waina Musbahu ikon Allah kawai yake kallo dan gaskiya fitinar Ramatu tafi karfin gaban kwatance.

"Kana jina kayi shiru ko? Amma bari na gama idan na d'ebo maka yan sanda zakai bayani".

'Dan kallon gefen da take Musbahu yayi yana cewa "ki kwantar da hankalin ki dama Lami ba daukota nayi dan na raba ta dake ba karatu zatai kuma tunda bakya so shikenan muje ki tafi da kayarki gida" washe baki Ramatu tai jin abinda yace tace "uhum d'an gari ba d'an garari ba muje yanzu ta had'a kayanta mu tafi kaima baka fi jin dad'i ba amma abu kamar naka kabi ka kanainaye saboda kwadayi da son zuciya" suna tafe tana masa bala'i mutane sai kallon ta suke suna mamakin a inda Musbahu ya samota.

Suna shiga gidan ta gansu zaune suna karyawa salati ta saki tana cewa "Lami ahh dole ki 'ki zama kauye kiyo birni inda zaki ci abinda kike so tabdijan to maza taso daga yau maganar cin abu mai dad'i ya 'kare zaki koma garin da kika fito kauye inda kika fi wayo".

Duk d'agowa dukai Lami data zaro ido waje cike da tsananin mamaki take kallon Ramatu yayin da mama tace "baiwar Allah wace ke daga ina me kike anan"? Hararar ta Ramatu tai tana cewa "a lallai kam samun gu harda zage zage ai ba dole saikin sanni ba wacce nazo gurinta ita ta sani".

Kallon Lami mama tayi taga ta sunkuyar dakai tana share hawaye wato inta fahimta babarta ce wacce Musbahu yake bata labari mafad'aciyar nan mai jawo fitina kara kallon Ramatu mama tayi tace "kiyi hakuri karaso ki zauna".

"Zama? Zama fa kika ce? Dama shi nazo yi banzo da niyyar ko kallon arziki nayi muku ba dan haka ki zuba min ido kawai shine naki kija bakin ki kiyi shiru" maida hankalin ta kan Lami tayi tana cewa "ke kuma dan ubanki da kika tsaya sauraron mu zaki tashi ki dauko kayan ki mu tafi ko saina fasa miki jiki da duka shashashar yarinya kawai".

Mi'kewa Lami tai cikin damuwa tana shiga d'aki hawaye na zata hado kayanta Naja'atu dake ta bin Ramatu da kallo tace "dan Allah ki 'kyale mana ita anan meyasa zaki raba mu".

Wani kallo Ramatu tayi mata "ke kuma asuwa kare da gudun layya ki bari nayi da tsofin ki dan ko kallo su d'in ma basu ishe niba kin gane".
Chapter 27 · 0% Book details