← Book details Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 61 OF 145

Sashe 61

Me Kamar Sarki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sultana Hadizah data kifa kai cikin Alkebba tana kuka jin abinda yake cewa yasa ta d'ago cikin kuka "wallahi bazan yarda ba dama can Asad da Khimiyyah jininsu bai had'u ba tun suna yara Asad mugu ne ba 'kaunarta yake ba kowa zai sake ya nuna shi d'ane amma banda ita indai yana guri ya riga ya zame mata dodo kullum sai tayi mafarkinsa da ihunta wani lokacin har a fili zakiji tana kuka kamar gaske tana kiran yai hakuri dan Allah harda wu'ka wani lokacin tace tana ganinsa a mafarki yana binta zai kasheta kuma akan haka me za'a cemin bayan ya gama cuta ta.........….......................

"HADIZAH YA ISHE KI HAKA😡" Mai girma Alhussain yai maganar cikin tsawa ko kunya haka Sultana Hadizah ta sake d'ora hannu aka tana fashewa da kuka "na shiga uku na lalace wayyo Allah na wai ana neman kashe min 'ya kuma nayi magana saboda d'an gidan kane shine kake min tsawa..................,........

"HADIZAH BANCE KI RUMIN MIN BAKI BA🤐? ZAN AIKATA ABINDA ZAKI NADAMAR SA"😣.

"Hussain kayi shiru haka ina son zanyi magana ku bani hankulanku nan idan kun gama" mai martaba Alhassan ya fad'a yana kallon su d'aya bayan d'aya ganin shed'an ya shigo musu gida yazo yana son tarwatsa musu farin ciki.

"Kayi hakuri yaya raina ne ya riga da ya gama 'baci wannan matar da kake ganinta bata da kara ko kadan batasan me take ba idan ba rashin ta idon ba a barshi ni 'kanin kane sannan Sultana Shafi'ah abiyarta ce zata iya fad'ar komai a gabanta amma kufa mahaifan Asad ne take irin wannan wulakancin iri iri a gabanku saboda bata gaji arziki ba".

Har lokacin bakin Sultana Hadizah bai mutu ba idonta jajur ta kallo Mami tana cewa "ai ba laifin kowa bane bayan mahaifiyarsa itace ta goya masa baya ba iya ra'ayin sa bane ga ummul-gauwal (uwar munafukai) nan tana jina......................

Nunata mai girma Alhussain yai da yatsa cikin takaici jin abinda take cewa yace "kinga Hadizah kiyaye ni idan wasu ne ma suke zugaki zasu kaiki su barki baki ta'ba ganin fushi ba ko? Ki taka a sannu idan kika kaini bango zaki sha mamakin irin huluncin da zan yanke miki bake ko 'yan gidanku ba hatta danginki bazasu ji dad'i ba idan kina gani kamar wasa nake kici gaba kece zaki ba wani labari ki tsaya iya matsayin ki".

Kasa magana Sultana Hadizah tai sai huci mai zafi da turiri ne yake fitowa daga zuciyarta cike da 'kiyayya ta sake d'agowa tana kallon Mami da ta d'auke hankalinta sam a kansu tamkar bata gurin hakan datai ba kamaramin 'konawa Sultana Hadizah rai yayi ba lallai wallahi bazata ha'kura ta 'kyale ba koda zai zama sanadin mutuwar aurenta zata d'auka indai Asad zai wulakanta Allah yasa ya mutu acan Allah yasa bazai sake dawowa ba yayi karo da masifa 'yan ta'adda suyi masa kisan 'kyama.

😲😳TOFA SUBAHANALLAHI SULTANA HADIZAH YADAI🤔 WANNAN WACCE IRIN 'KIYAYYA CE🤨😏 KIKE NUNAWA ASAD 'DIN MU?🙄🙄.

"Kun gama"? Mai martaba Alhassan ya tambaye ransa a 'bace.

Kai mai girma Alhussain ya girgiza yana cewa "kayi hakuri yaya ni bana d'aukar shashanci ne".

"Ai shiyasa nace kun gama"?.

"Eh yaya kayi hakuri".

"Shikenan ku saurara da kai zan fara Hussaini mene ya had'a ku har wannan maganar ta taso?.

"Yaya magana take akan bazata yarda ba idan Khimiyyah ta mutu wai harda sai taje kotu tsabar da'ki'kanci ni kuma a tunani na koda Asad ne da laifi kuma ya daketa harta mutu bazata bud'i baki tace komai ba saboda laifin d'an uwa daud'ar gora ne".

Kai mai martaba ya jinjina cikin mamaki yana kallon Sultana Hadizah domin ya kira Asad a nutse ya tambaye shi abinda ya had'a su kuma ya fad'a masa bai cewa kowa komai bane so yake sai Khimiyyah ta tashi ayi a gaban kowa dan yanzu kome zaice tunda har anyi haka Sultana Hadizah zataga kamar shima yana kare shine dan d'an sane baison laifinsa.

Maida hankalin sa kan mai girma Alhussain yai yana cewa "ba nace a bari sai Asad ya samu hutu yazo gida ba sannan ita kuma Khimiyyan ta samu lafiya na yarda na amince ayi bincike a sannan duk wanda yake da laifi a cikin zai fuskanci hukunci na bana so na sake jin wata magana indai akan wannan case d'in ne zan zamo uba mai adalci a tsakanin su"?.

"To yaya kayi hakuri in Allah ya yarda za'a kiyaye na tabbata Khimiyyah ce mara gaskiya ba Asad ba domin koma maye haka kawai bazai daketa batai masa komai ba tunda dai abun yazo da haka saimu jira ta farfad'o za kuwa taci ubanta daga lokacin dana gane cewa itace mai laifin zata yabawa aya za'kin da take dashi".

"Shikenan Allah ya rufa asiri tunda haka ta sakance zuwa dare idan su Ameer sun dawo duk abinda likita yace sai ayi idan kuma sun gagara nema sai mubi shawarar Ameer a fita da ita wajen".

"To yaya dama ni akwai inda zanje kafin yanzu gashi lokaci yana neman fita min nima sai daren zan dawo".

Kai mai martaba Alhassan ya d'aga yana cewa "ok ba matsala ka kula" yana mi'kewa Sultana Shafi'ah ma mi'kewar tai suna fita tare yayin da Sultana Hadizah ta tashi cikin kishi ganin sun fita buguzun buguzun tana hararar Mami tabi bayansu sai tsinewa Asad take a ranta d'an tsaki Mami tai itafa dama harga Allah Sultana Hadizan nan tun ba yanzu ba ta fahimci inda ta dosa sosai bata son laifin 'ya'yanta sannan ta maida d'an wani banza nata kuma dukiya hummm kullum tayi sallah tana ro'kon Allah yasa Khimiyyah ta farfad'o kodan Sultana Hadizah taji kunya ta gane 'yarta ce mara gaskiyar da bataso a fad'a..............................

"Hauwa'u kinyi magana da Asad ne"? Jin saukar muryar mai martaba yasa ta dawo daga duniyar tunanin data fad'a tana maida hankalin ta kansa tace.

"Na'am Allah ya baka nasara me kace"?.

Da mamaki mai martaba ya sake kallon ta yana cewa "tunanin me kike yi haka har nai magana bakiji ba ko abun ya damaki ne"?.

Kai Mami ta girgiza tana murmushi tace "a'a mai nasara babu abinda dake damuna kawai dai banji me kace ba".

"Ok cewa nai kinyi waya da Asad ne jiya ko yau"?.

"Eh munyi magana dashi jiya munkai kusan karfe sha biyu na dare a online yana fad'a min cewa sun ma fita operation ne cikin wani daji zasuyi kusan wata guda kafin su fito yanzu baida lokaci sosai kuma ba damar kiransa ta shiga saita chat dole wajen babu network".

Da murmushi a fuskar mai martaba yace "Tofa Asad d'ina yana can a daji gurin ma'kiya tab umh Allah ya fito dasu lafiya shiyasa Ajeeb yace bazai soja ba akwai wahala ya za'bi doctor👩‍🔬 Annur ya za'bi banker👩‍🏫 Ameer yace lawyer👩‍🎓 amma Asad ya d'age sai soja👮yafi son a ri'ka marmarinsa daga nesa balle abina yana da kwarjini ko bai soja ba da gani ba raini".

Dariya Sultana Fatima tai tana cewa "ra'ayi kenan cin d'an wake da diga kowa aikin daya kama zaiyi mana amfani Annur ba ruwan mu da wani harkar zuwa banki ciro ko sa kud'i Ajeeb yana duba lafiyar mu babu ruwan da hospital ga Ameer lawyer kaga shima zaiyi mana amfani ko".

"Humm zaiyi kam tunda ga Sultana Hadizah tana zancen zuwa kotu saboda rashin tunani" mai martaba na rufe baki Mami tace.

"Oh wai da gaske take sai takai 'karar da take magana"?.

"Lallai hauwa'u amma kin manta wace ita idan ana neman mace mara kirki da kara azo wurinta itace karshe".

'Dan ta'be baki Mami tai cikin rashin nuna damuwa tace "Allah ya kaimu lokacin fatana Khimiyyah ta tashi Allah yasa yarinyar nan karta mutu kawai ina so Sultana Hadizah ta fahimta ta gane abinda ya dace da wanda bai dace ba domin yawancin lokuta tana yin abu da ka kuma a gurin ta daidai ne".

"Humm bari kawai tabi a sannu duniya makaranta wanda bazai bama jiransa take balle wanda yake cikinta ya d'au rayuwa da fad'i" Mami ta karasa maganar tana jijjiga kai d'orawa Sultana Fatima tai da cewa.

"Ke kam kibar batun kawai kinsan tun farko Sultana Hadizah tana da jin kai🙄 idan kin lura"?.

"Eh ina kule da ita amma miye ruwana a ciki ta kiyayi duniya da zataji shawara da nace mata duk lokacin da taji girman kai yana shirin kamata tayi sauri ta kalli 'kasan 'kafarta maimakon haka sai take sake d'aga kansa sama tana shar'kar iska shiyasa akan ta samar da zaman lafiya sai take neman jefa fitana a cikin ahli" Mami tana rufe baki Sultana Fatima na shirin magana mai martaba ya katse ta.

"Wannan maganar ta isa haka ya kamata a sauya wani zancen ba wannan ba idan kasan halin mutum saika sha maganin zama dashi kun gane nasan kun fini sanin halayenta da d'abi'unta tunda kullum kuna tare nifa sai ranar da muka had'u nake jin irin wannan damuwar na dama min masarauta amma na kusa kawo 'karshen komai Allah ya baiwa Khimiyyan lafiya so nake sai sun had'u guri d'aya dukkan su hudun zanyi magana dasu naga babu wanda hankalin sa yake kan sarauta kowa harkar gabansa kawai yake ina so nasan waye zai gaje ni".

Baki Mami ta ri'ke "to babbar magana anya a cikin su akwai wanda yake sha'awar sarauta kuwa umh amma ban sani ba sai munji ta bakin nasu tunda kansu d'aya rana d'aya aka haife su babu babba ba yaro shiyasa suke ganin daman juna musamman Asad rigima ta masa yawa nasan baya ra'ayin sarauta dama babu shi a ciki ukun za'a tambaya Asad da sarautaa? wai da anga cakwakiya😂".

Murmushi mai martaba yai yana cewa "Hauwa kin raina min Asad d'in nan nawa komai sai kice shi gaskiya ban yarda ba karfa ya dawo yace zaiyi mulki ki bari zamu baki mamaki idan kika ganshi cikin kayan sarauta saikin rud'e kin kasa ganeshi kiyi tunanin ko daga Ethiopia yake tsabar kyau da d'aukar hankali".
Chapter 61 · 0% Book details